03

422 36 2
                                    

RAYUWAR JIDDAH
Part 1/03
Mallakin DielaIbrahim
____________________________________
Time pass
March,2018

Sitting room ne mai dauke da L shape din kujeru ash color da throw pillows black, sai center carpet da cottons masu kyau kallo daya zakawa palor din ka tabbatar da kyan da yayi ga tsabta komai yana ajiye a inda ya dace, sai kamshin turaren wuta dayake ta faman tashi.
Gefe daya ta bayan kujerun corridor ne da alamu shine zai kaika dakunan dake cikin palor din sai dinning area dayake kallon kofar fita wanda tundaga sitting room din zaka hango haduwan wajan saboda irin kayan adon dayasha.
Idan muka dawo bangaren sitting room wata yarinya ke kwance rufda ciki tana ta faman latsa wayar Android kirar Tecno....Sosai hankalinta ya zurfafa cikin dannan wayar tata lokaci daya kuma wayar ta soma ringing.....da sauri ta daga wayar tana kokarin kwantar da kanta akan pillow hade da bude baki donyin magana amma sai aka riga tacikin wayar ana cewa......

Jiddah meyasamu wayar ki ne bata shiga tun dazu? Budurwar da aka kira da Jiddah ta kyafta idanunta alamar mamaki sannan tace What! Wayata tana kunne fah tun jiya Fatima I guess matsalar network ne
Uhmmm Jiddah tun jiya around 11pm nake faman dialing contact dinki amma baya shiga and na miki text a What'sApp but no reply dukdama banga kin hau din ba kodayake nasan kinsa ta a flight mood as usual....ta tsagaigata tana jiran amsar Jiddah

Am so sorry Fatima it's might be a network problem saboda ko jiya da night sai danayi answering calls, Amma me ya faru ne?akwai matsala ne?
Yes,ta bata answer
Menene Fatima? Jiddah ta tambaya......Jiddah tun jiya SIWES CO-ORDINATOR dinmu ya sanar da class rep yana son ganin all 300level student, and the worst part of it shine yana so muyi submitting Acceptance letter ayau yau dinnan.

What! Cewar jiddah alokaci daya tana kokarin tashi daga rufda cikin datayi cike da tashin hankali, tace Fatima are you serious about this?

Daga dayen bangaren Fatima tace haba Jiddah do you think zan kiraki na tsorata ki akan abu irin wannan ne, and to cut the story short yanzu haka  muna department tsaye outside his office muna jiran isowarshi,so kishirya kema kizo class rep zai mashi magana yadan kara bamu time  saboda yawanci duk bamu anso acceptance letter dinba, and mu kinsan ma namu daban ne tunda ko SIWES LETTER din bamu samu inda aka amsa ba Koh, so  please don't be late.
Doguwar ajiyar zuciya ta sauke daganan zaune kafin ta gyada kai kamar tana kusa da kawar tata sannan tasamu damar furta okay  ciki ciki wanda zaka dauka muryar ta shakewa tayi....sannan ta kashe wayar ta tsura ma wayar idanu don ita tama rasa abinyi yanzu,
Tana nan zaune taji an dafa ta.
Firgigit tayi hade da kyafta idanu zara zaran eye lashes dinta masu yi kaman sun jike da hawaye....suka kuma fitowa ta zare idanu tana kallon mai dafa ta, lokaci daya kuma ta saki murmushin da baikai cikin zuciyarta ba hade da cewa Momma!

Meke damunki ne Jiddah? Naga kina cikin damuwa  after all yanzu fa na barki kwance anan muna wasa da dariya..... what's wrong with you? Jiddah ta kalli Momma...ko giyar wake tasha ayanzu dai bata isa ta fadawa momma halin da take ciki ba...don tasan fada zatai mata kuma ita aduniya idan akwai abinda yake bata mata rai easly to shine fada, kuma ayanzu dai tasan itace bata kyauta ba tunda SIWES LETTER dinnan tun January aka basu, Amma basu tashi kaiwa ba saida lokaci ya kure masu..........ji tayi ana jijjigata again Momma nacewa  
Jiddah wai lafiya bazakiyimin magana bane?
Dabara ta fado mata lokaci guda kuma ta sakarwa Momma da murmushi wanda itadai ta yishine amma bai kai har zuciyarta ba, tana shirin bude baki tayi magana ne, wayar tata ta soma ringing kallon screen din wayar tayi taga Fatima ce....tashi tayi, tayi hanyar bedroom dinta dasauri tana cewa momma ana neman mu a school bari naje na dawo zan fada maki.

Tashige daki tabar Momma zaune da baki bude tana mamakin yanda Jiddah take reacting....why is she behaving this way? Tabe baki tayi tana cewa idan kin dawo naji koma miye ne....ta dauki remote tana canja channel din arewa24 izuwa Bollywood.

RAYUWAR JIDDAH ✔Where stories live. Discover now