32

142 14 5
                                    

RAYUWAR JIDDAH
Part 2/12
ALKALAMIN DIELAIBRAHIM ✍️

____________________________________

**********
❤️❤️❤️❤️❤️

Bayan yayi sujudur shukur ya mike ya rungume ni tsam a faffadan kirjin shi wanda bai taba yunkurin yin hakan ba sai yau" yau dinma sai da ya tabbatar da cewa an d'aura mana aure sannan yai min"
Yaya Hafiz can't hold it yai min rungumar da har yanzu na kasa mantawa da ita "very emotional hug" sannan yace cikin sanyayyar muryarsa wacce ta ratsa ko ina na jikina"
*I love you with all my heart HAUWA'U you are my life* sai daya ja numfashi sannan ya kuma cewa kaman rad'a " Hauwa'u please do me a favor and go back home, bana son wani abu ya same ki, kinji Hauwa nah" go home please "
Na rungume shi tsam a jiki na, nace I love you too Yayanah" but Ina tare dakai Yaya Hafiz" kada fa ka manta am now your wife and you are my husband" you expecting me to go home and leave you all alone" Nooooo Yaya nah I can't leave you alone" tare zamu koma gida insha Allahu kaji"   muka hada kai muna ta kallon juna kawai mukaji karar bindiga da sauri muka juya, nan naga mutumin yana shirin yin wani harbin wanda wannan karan ya seta bindigar adaidai jikin Yaya nah,.  Naji yana cewa wato ku masoya ko, muna nan ku kuma kuna cen kuna soyewa, to yau zanga karshen lovayyan naku, sai inga abinda zakuyi  " zan bude baki na fara rokonshi kenan naji karar bindiga bansan lokacin dana ture Yaya Hafiz ba na tsaya awajan kaman almara naji shigan bullet a kafata na dama" 😣 adai dai lokacin dana duka Ina ihu Ina kiran sunan Allah dana yayanah, kuma adaidai lokacin Yaya Hafiz yayi ihu na karshe wanda yasa ya fada cikin halin da yake cikin yanzu"

*Nikam ban bari Jiddah ta karasa ba nace "meke damun sa kenan Jiddah"*

Jiddah tace Ina kaiki ne ai so be patience" da sannu zamuje wajan" Yaya Hafiz yayi ihu ya kira sunana, tun daga lokacin ya fadi awajan, ni kuma ganin halin daya shiga wanda ni banma damu da halin dana shiga ba, dukdama Ina jin zafi, ciwo, rad'ad'in da kafata take min ahankali nima nakwanta awajan hannaye na suna cikin na Yaya Hafiz Ina kallon fuskar shi" Ina Jin mutanen suna fad'in boss kanshi ya fashe sakamakon faduwar dayayi yanzun nan ya bige akan dutse" kaga mu namu yazo a sauki boss yakamata mubar wajan nan saboda da alama dukkansu suna cikin wani hali, kuma da kyar in zasuyi rai"
" Boss din yace alright let take our leave now, hurry up guys duk suka bi cikin daji Ina kallon su, anan suka barmu tun Ina sanin halin danake ciki har nima na suma awajan"

Uhmmmm Rayuwa kenan ban bude idanu ba sai agadon asibitin Air Force Base "NAFHospital, ko dana farka ihu na farayi abinda ya faru ya dawo min sabo, Ina ihu Ina kiran sunan Yaya Hafiz sannan Ina kokarin cire duk wata na'ura da aka sada ta da jikina nurses ne sukayi kokarin rike ni alokacin dakin danake daban ne allurar bacci sukai min haka na sake komawa bacci batareda sanin inda hankali na yake ba"
Sai after 24 hours na sake farkawa, wannan karon cikin natsuwa na farka sannan na daura idanuwana a fuskokin yan uwa na, babu wanda ban gani ba" nayi yunkurin tashi zaune Momma ita tazo da sauri ta daga ni ta zaunar dani* na kalle ta nace Momma Ina Yaya Hafiz ?
Tai min shuru babu answer"
Na sake tambayar Ummi Ina Yaya Hafiz?

Ita ma shuru taimin" uhmm haka na cigaba da tambayar su daya bayan daya" amma babu answer" Jin shurun nasu yayi yawa hakan yasa nayi yunkurin saukowa daga kan gadon danake amma to my own surprised" daya daga cikin kafafuna!
One of my legs😢😭 naji yana min ciwo da zafi sannan banji alamar kafa awajan ba! Ya salam iskan da akeyi ne ya shigo ta window to which ya yaye farin zanin gadon da aka lullube ni dashi" Lahaula wala kuwata illah billah" Daga Allah muke kuma garesa zamu koma"

Inna lillahi wa'inna illaihir raji'un"abinda baki na yake iya furtawa kenan, sakamakon abinda na gani" one of my legs was cut off wanda ciwon ma har ya soma warkewa amma ba'a cire bandage din ba" na zare idanuwa na Ina kallon duk wani mai rai acikin dakin da nake"

Wallahi kukan ma yaki zuwa,alokacin nashiga kid'ima da tashin hankali sosai, maganar ma taki zuwa idanu kawai nake bin kowa dashi" gashi dai an yanke kafa daya but I can't believe that wai yau ni Hauwa'u Jiddah na koma mai kafa daya"  masu karatu kuyi imagining kune kuna zaune da ko wanni part na jikin ku, and kawai Rana d'aya ka farka kaga an cire maka" ka rasa daya daga cikin part din jikin ka, Don Allah ya zakuji a zuciyan ku" toh ku kwatanta irin zafin da zakuji, Nima fah shi nake ji a wannan lokacin" Na sake kallon Momma nace" Momma please Ina Yaya nah yake ?
Where is Yaya Hafiz? You people should please say something"

Abba na shi yazo inda nake ya zauna ya rike hannayena biyu ya kalle ni, idanuwansa kaman mai shirin yin kuka" yace Mamana yayanki yana lafiya!

Nace toh Ina yake Abba, ba zai zo ya ganni ba Abba" Abba yace yazo ai kusan kullun sai yazo amma baki farka ba" Jiddah kinsan yau kwanan ki nawa a hospital ko numfashin kirki bakyayi" yau kwanan ki talatin da biyar Jiddah, da fari mun dauka bazakiyi rai ba" amma likita ya tabbatar mana da cewa kina numfashi amma ba yanda ya kamata ba" sai da akayi operating heart dinki sannan bugun zuciyar ki ya fara tafiya normal" anan mukai ta zaman jiran farfad'owan ki, kullin cikin hope muke amma shuru baki farka ba" sai jiya likita yake sanardamu kin farka"

Na runtse idanuwana sannan nace Abba haka Allah ya kaddara min a Rayuwata kenan" nayi folding hannaye na nace amma burina ayanzu bai wuce inga Yayanah ba" don Allah ku kirashi yazo"
Yaya faisal shi ya karaso inda nake yace Jiddah kwantar da hankalinki zaki ganshi insha Allah, yanzu likita yace kar kije ko ina, so shi zaizo ya gaida ke kinji"

Yaushe? na kara tambaya

Ya dafe forehead dinsa sannan yace gobe insha Allah"
Murmushi suka ga nayi sannan na jingina da pillow, to fah alokacin kome kace nayi zanyi saboda Ina farin ciki yayanah yana lafiya kuma gobe zan ganshi"

*************

Wasa wasa har na kara sati biyu Yaya Hafiz bai zoba, kullin sai suce min wai aiki ne yai mashi yawa sosai" haka nai ta kara hakuri har na kara wata biyu, alokacin na fara takawa da stick, Momma ce ke taimaka min har na saba" gashi kullin Ina ganin family na, hankali na yana dad'a kwanciya, saboda kowa soyake yaga ya faranta min"
Likita kuma ya tabbatar musu na samu lafiya sosai zuciya ta tana bugawa yanda yakamata har yai musu albishir ma ya kusan sallamata"
*****************
Kwanaki na ta tafiya, sai kaga anyi shekara ma Amma  kamar ba'ayi ba,....Allah cikin ikon sa doctor din dake dubani ya rubuta takaddar sallama, kuma aranar su Yaya Faisal sukai min albishirin cewa aranar zanga Yaya nah" farin cikin dana shiga ya wuce tunanin mai karatu"
* Tsabagen farin ciki kuwa ranar sabon kaya na sanya doguwar riga Abayah black" Momma ita taimaka min na rike stick dina Ina d'ingisawa, sai ya zama kaman dama na iya tafiyan saboda yadda na kware a rike stick din 😅lol.

❤️❤️❤️❤️❤️❤️❤️❤️❤️❤️❤️❤️
🤔 Let see what will happen in the next chapter" but for now your comment are highly welcome 😁

VOTE
COMMENT PLEASE

RAYUWAR JIDDAH ✔Where stories live. Discover now