26

213 19 5
                                    

RAYUWAR JIDDAH
Part 2/6

ALKALAMIN DIELAIBRAHIM ✍️

____________________________________
Hospital
10am

"The next day""
Misalin karfe goma kowa yazo hospital har da Leemarh Amma ta bar su Daddy agida...Hafiz kuwa yana nan babu inda yaje abinshi, a cewar shi Hauwa'u tana bukatar sa a kusa da ita don haka babu inda yaje sai dai da aka matsa masa da magana sai yayi wanka a bandakin dake cikin ward din, sannan Leemarh da zata zo sai ta  taho masa da kaya, hmm Oga kenan 😎 anan yasanya kayan sannan sukaci abincin da Ummi ta dafawa Jiddah, tare ma suka ci a plate daya ko kunyan mutanen wajan basayi."

Suna zazzaune abinsu suna hira aka kira wayar fatima, aka sanar  matà cewa first semester results dinsu ya fito, habawa tuni suka rude ita da Jiddah, da sauri Jiddah ta kunna data na wayar ta, whatsApp messages suka fara shigowa, ta shiga class group dinsu mai suna "BCH CLASS OF 15" Fatima tazo ta zuna suna dubawa tare har suka zo kan matric number dinsu, kasancewar accordingly ne Jiddah 1134, Fatima 1135, babu abinda suke fadi sai Alhamdulillah bakin su ya kasa rufuwa, suna ta fadin munyi passing" Faisal yace mugani, Jiddah ta mika masa wayar tana kallon Hafiz dayake murna shima yace "Congrats dear" tace thank you"
Ana ta taya su murna, suna farin ciki Fatima tace Jiddah sauran mu second semester and it's the final semester Allah ya bamu sa'a" Jiddah tace Amiin ya rabbi"

**************

Da misalin karfe goma sha biyu na rana 12pm dakin ya cika da mutane ana ta faman hira kuwa sai Muhammad yace Ammi abamu labarin please ana ta ja mana rai😣
Ammi tace wa badai ni ba, ta dubi Ummi tace gareki Ummi, 'ya'yan ki nason jin labarin ki"
"Ummi tai murmushi tace yaran kadai zan bamawa saboda haka manyan should excuse us, Momma tace dama ni kam gida nayi, Ammi tai saurin cewa jira ni mu tafi tare Momma, haka su ka fita harda Abba, Abba yace da Ummi zai fita wajan abokinsa, tace to Allah ya tsare"  Ummi ta lura kaman Abba ya sauko daga kan kujeran mulkin daya hau kwana biyunnan, ko dayake dama ba halinsa bane ara yayi ya yafa😂" Tana ta wannan tunanin, sai taji Saifullah na cewa Ummi we are all ready"
"Ya dawo ta ita daga cikin trance din data shiga, ta waiga sai taga daga ita sai yaran, Ummi ta tashi ta nufi gadon Jiddah, ta zauna very comfortable  sa'annan ta jingina da bango sannan ta kwantar da Jiddah a laps dinta tana shafa mata wuya" Ummi ta kalli Jiddah wacce hannayen ta na cikin hannun Hafiz ya rikesu dakyau kamar ance za'a kwaceta a gudu da ita" ahankali Ummi tai murmushi sannan ta soma.

******************************
TUNA BAYA

Shekaru Arba'in da suka wuce tunda ayanzu shekaran Hafiz 31 Jiddah kuma tana 21...............

"Sunana Halimatu wacce kuka fi sani da Ummi" tun Ina shekara goma Momma ta dauko ni daga katsina wajan Ammi, na dawo zama awajanta tun Uncle(Abban Faisal) baida kudi, har Allah ya bashi rufin asiri sosai, da farko dai unguwan dosa suka fara zama daga baya lokacin an haifi su Isma'il da Idris dasu Maimuna sai ya koma Unguwan rimi, ya gina gida na gani na fada, Uncle shike daukan duk wani responsibilities dina, ayayin daya hana Momma kashe ko sisin ta akaina, Lallai Uncle mutumin kirki, mutumin arziki har na gama secondary school bai dena dawainiya dani ba, sannan ya biya mana Hajji mukaje gaba dayanmu, dawowar mu kuwa bada jimawa ba (27th December,1980 na samu admission a Kaduna Polytechnic (Kadpoly) , dukda kuwa rayuwa bata tsada lokacin, shi kanshi jami'ar ma ba kowa ke zuwa ba saboda karancin wayewa, dukdama ilimi ya dade da shigowa amma neman ilimin baiyi yawa kaman zamanin yanzu ba, shiyasa muka kasance mu goma(10) a class dinmu, inda suka bani Business Administration.....Allah sarki Uncle, Allah ya jaddada rahama agaresa, shine yai tamin registration da komai ma, har na fara zuwa lectures,, kullin cikin maida hankali nakeyi a makaranta, Ina dawowa kuwa zan samu Uncle ya taya ni yin assignment sannan ya kara yimin  bayanin darasin da aka koya mana.
Ana haka muka fara test, Ranar da muka fara test itace ranar da har yau bazan taba mantawa da ita ba a rayuwata........Ummi ta dan tsagaita ta dubi yaran duka Wanda sukai shuru suna sauraranta tace lokacin sallah yayi, yakamata ku tafi masallaci" after zuhr prayer sai mu cigaba Koh!

RAYUWAR JIDDAH ✔Where stories live. Discover now