07

241 27 13
                                    

RAYUWAR JIDDAH
part 1/07
Mallakin DielaIbrahim

*Momma taja dogon numfashi  sannan ta dubi fatima tace:
"Muna zaune gaba dayanmu a main palour tun dawowarsu,Faisal da Isma'il suka ce"Abba mu zamu tafi gidan  "Mama" kasan su Imran sunzo jiya kuma jibi zasu koma"(Imran daya daga cikin yaran kanwar Abba ne wacce take aure a Lagos, Mama kuma grandma din su Faisal ce)"Abba yace ina kwana zakuyi acen din?"
Isma'il "yace eh Abba gobe zamu dawo sai mu taho tare dasu, Momma tace tohm ku tafi da kannen ku mana!
"Isma'il ya ce noooooo Momma barsu kawai karma su fara Jin dadi, don takura ma Mama zasuyi musamman Jiddah
Momma ta tabe baki tace kasa ma Autanah ido Isma'il kamanta Jiddah mutuniyar Mamace! Jiddah tace eh mana ai harma nafika matsayi nida Yaya Faisal awajanta ma danma kasani.... takarashe maganar tana shan ice cream din data debo a spoon ko kallon inda suke ma batayi"Faisal yayi murmushi ya girgiza kai kafin ya kalli momma yace mukam zamu tafi sai da safe.
Momma tace toh ku gaida Mama da sauran yan gidan"toh suka amsa, Faisal ya dubi Jiddah ya langwabar dakai yace ahankali  my little girl babu rakiya ne?
Murmushi tayi tana lashe spoon tace Yaya Faisal dina kai kadai zanyi wa rakiya banda Yaya Isma'il kuma....Faisal yayi dariya kadan sannan yace tohm nagode koh, koma ki zauna na yafe miki rakiyan ma kinji"Jiddah tace toh sai da safe Yaya"
Momma tace Jiddah babu kyau haka, shima Yaya Isma'il kice mashi sai da safe kinji"Aa Momma bayace bazai je dani wajan Mama ba"..nikam danayi niyan zuwa ma sai dai kawai idan mun Isa yaganni na fito acikin mota abina".kaf palour din babu wanda baiyi dariya ba sanin halinta sosai zata iya aikata hakan"cikin kwanciyar hankali ta zumbure baki tace Yaya Isma'il sai da safe ta karashe maganar tana gyara kwanciyar datayi acinyar Momma hankalinta kwance...
"Hakannan kowa ya bita da kallo she is unbelievable, sannan su Faisal suka tafi.
"Hira muka cigaba dayi cikin wasa da dariya har lokaci ya ja sosai "Jiddah tana kan cinyata ita ta fara yin bacci ganin haka Abba yace toh Jiddah tayi bacci kowa yaje ya kwanta, su maimuna suka tashi zasu tafi daki sai Abba yace khadija zo ku dauke ta ahankali kar ta tashi.
"Sai asannan nace dasu maimuna  aa kunsan fah Jiddah a daki na take kwana yanzu idan ta farka tsakar dare ta fara kuka ya zakuyi?"khadija tace kuma fah hakane momma don rannan ma da tace zata kwana da rigima akabarta ta kwana amma sai gashi data tashi cikin dare taita faman yi mana kuka, haka mukayi kwanan zaune muna rarrashi wlhy,shiyasa washe gari idanun mu duk suka kumbura harda ita kanta Jiddarh. Maimuna ta capke da cewa toh baki ganin ba laifinta bane ta saba kwana tare da Momma ne kema ai haka kikayi da kina kamarta wani rigima ne bakiyi ba"
Khadija ta turo baki tana cewa nidai Momma kinsanme ta kwana dakinki kawai, don Ina so nayi bacci yau gobe monday kuma morning lectures mukeda ta karashe maganar tana hamma kafin tayi gaba tana cewa goodnight"
Maimuna ta girgiza kai tana cewa Momma kawota naje na kwantar da ita sai na wuce daki,
Maimuna ta dauke ta kasancewar bawani jiki gareta ba siririya ce batada nauyi hakan yasa bamajin wahalan daukarta, ta kaita dakina kafin ta wuce nasu dakin.
"Abba yace Momma yaufa dakina zaki kwana"na zare idanu Ina cewa lahhh Abban yara kamanta Jiddah na dakina kuma kasan zatayi kuka idan ta farka taga bana kusa, kanajin conversation dinmu da Khadija ae.....
Abba yayi gyaran murya sannan yace toh ki kwana daki na inyaso wuraren three 3 sai ki koma koh don karta farka.
Hakannan nabar Jiddah a dakina Wanda yake cen lungun wani corridor dazai sada ka da dakin su maimuna inba kasan kan gidan ba bazaka taba cewa akwai daki awajan ba.
Bayan kowa ya kwanta
"Misalin karfe biyu na dare na dan gyara kwanciyata, sai naji maganganu sama sama lokaci daya na razana Amma kafin nayi wani motsi naji an daura min gun a goshina......take zuciyata tayi wani mummnan bugawa na toshe bakina alokacin da aka kunna wutan dakin, mutane nagani cikin dakin zasu kai mutun bakwai sanye cikin bakaken kaya riga da wando na jeans black, hannayensu sanye cikin safar hannu kuma kowannensu dauke da guns, knifes dasauran su,haka fuskokinsu ma ke sanye da face mask, take jikina yadau rawa alokacin danaga Abban yara kwance gabansu, nima haka aka taso ni suka tashi Abba sannan suka tasa keyarmu zuwa main palour,wato wasu mutanen na kuma gani masu yawa, nidai akiyatsance zasu kai 20 koma fin haka,
hamdala nayi alokacin dana waiga ko ina babu ko daya daga cikin yara na, muna zaune a palour to which suka kwantar damu sai asannan shugaban su yace turo mu akayi kuma yanzu zamu aiwatar da aikinmu, mu bar nan cikin gaggawa, sannan bama bukatar kudin ku bama kuma bukatar komai,
Abba da kyar ya iya cewa, kuyi hakuri ku fadamin waya turo ku?Amma suka ki fadin wanda ya turo su......
Bansan lokacin dana fara magiya Ina rokon suba akan kada suji hudubar da shaitan yake masu, hakika su tuna ranan gobe kiyama za'a bima mutane hakkokinsu, su tuna cewa Allah kuma mai yafiya ne ga kowani bawa matukar kayi nadamar mummunan aikin daka aikata aduk lokacin dakayi niyan yin wani aiki mara kyau to idan ka fasa yin aikin,Allah zai yafe maka sannan azuba maka lada maimakon zunubin da zaka dauka,su tuna fah da akwai Allah suji tsoron Allah su kyale mu,kada su cutar damu"Amma tsawan da ogan ya dakamin shiyasa nai shuru Amma ko firgita banyi ba, ahankali na cigaba dacewa kada ka damu ayanzu bana jin tsoron abinda zakuyi mana nasan cewa duk abinda ya faru damu nasan rubutacciya ce awajan ubangiji,.sannan nayi shuru na tashi zaune Ina kare musu kallo, banyi aune ba sai jin karar bindiga nayi wanda bansan wa aka harba ba, sai dai ganin blood nayi yana fitowa daga kasan rigar Abba wanda yake kwance awajan, ban yadda da abinda idanuwa na suka gani ba hakan yasa na dauke kaina awajan na mayar hanyar corridor gudun kada ace yarana sunji karar bindiga Amma lokaci daya na sare ganin maimuna tana kusanto inda muke hankali tashe bayanta ma khadija ce...haka suka je wajan Abba suna jijjigashi suna kiran sunanshi......nidai Ina zaune Ina binsu da idanu to which kallon Abba nakeyi wanda ko motsi bayayi"sai ji nayi wani nacewa oga mun gama aikin mu, yakamata mubar nan fah"
Maimuna ta tashi tsaye rai bace ta nufi inda ogan yake tace ku wasu irin azzalumai ne, akan me zaku kashe rai, shin laifin me mukayi maku dazaku zo har gida ku kashe Abbanmu....wallahi sai na kai karar ku wajan hukuma tabi mana hakkin mu ta karashe maganar tana huci cike da kwarin gwiwa"
Ogan ranshi ya rigada ya baci kallon wani yayi agefenshi yace "asakar mata kaifi daya"
Batareda da bata lokaci ba suka harbi maimunatu, alokacin idanuna suka hango Jiddah wacce take tsaye bakin corridor tana shirin karasowa inda muke but, karar bindigar dataji ne yasa ta fadi a bayan kujera alamar suma tayi kuma babu wanda ya lura da ita, atake Khadija ta nufi wajan maimuna  ta rikota suka fadi tare "inaji ina kallo maimuna tana ta shure shuren mutuwa sai alokacin nasamu na karasa inda take da rarrafe Ina kallon cikin kwayar idanunta itama kuma kallo na takeyi hawaye nake sonyi amma ya kasa zuba ko kadan, Khadija cikin bacin rai ta fara zaginsu tana tsine masu tana kuka tana fadin Allah saiya saka mana mugaye yan iska, kunzo gidan mutane kuna ta faman kashe su, sai kace rai ahannunku yake, wallahi sai an mana hisabi atsakanin mu...... bata karasa ba na rufe mata baki Ina girgiza kai Ina nufin tayi shuru but, sai naji wani yana cewa oga abarni na koya ma yarinyar nan hankali don Allah,
"Ogan yayi gyaran murya sannan yace munzo nan da niyan kashe mutum daya ne Amma sai aka samu akasin haka to which ba haka naso ba,jibril yaran nan sun batamin rai Amma ta biyun tafi batamin rai ko ta manta mu suwa ne take irin wannan zagin in our presence please make sure you torture her very well yadda ko gobe taga wani bazata kara zagin sa ba the way she just did now.
Momma ta tsagaita ta kuma share kwallan dayake zuba a idanuwanta"ta dubi fatima da itama awannan lokacin kuka takeyi sosai lallai labarin ya tabata, hakika datasan haka labarin yake da bata nemi sanin wani abu daga cikin "RAYUWAR JIDDAH ba"
Sa'annan Momma tace Fatima hakika naga tashin hankali awannan lokacin Ina ji Ina kallo aka tafi da ita daki damasu raping khadija wanda kusan maza biyar suka illata rayuwarta suka barta kwance wanda ko numfashi ma batayi sannan suka bar gidan cikin gaggawa........
Hakanan sukabarni nikadai da raina zaune waje guda ko mostin kirki banayi sai faman kallon Abbansu da maimuna nakeyi hana rantsuwa dai da kyar naja jiki na nufi dakin da Khadija take,kallo daya nai mata naji zuciyata ta buga sai alokacin naji zubowan hawaye masu zafi afuskata sai alokacin kuka yazo min wanda inayi ina gyara mata jikinta har nafara jin kiran sallan asubahi mai wankin mu wanda basuyi masa komai ba shi yazo ya taimaka min yana ta kiran Yan uwa yana sanar dasu, kafin bayan sallan asubahi su Faisal suka karaso gidan harda Mama dasauran yan'uwan Abba "sai alokacin numfashin khadija nah ya dawo wanda takeyinshi sama sama, na riketa Ina kuka Ina kokarin kiran family doctor a phone dina Amma kafin ya karaso Khadija tai wani numfashi mai karfi, jikinta ya saki gaba daya, Inna lillahi wa'inna illaihir raji'un abinda ya fito abakina kenan, Faisal dama Yana gefena sai ji nayi yace Momma Khadija fah bata motsi, kar fah ace itama ta mutu?shuru nai masa kawai saboda nasan lallai Khadija ta koma ga mahaliccinmu".tundaga lokacin ban sake sanin inda kaina yake ba har tsahon kwanaki uku, 3days Ina kwance sai dai family Dr.yazo ya dubani wanda kodana farka Jiddah na farayin tozali da ita daganin abubuwan dasuka faru suka dawo min cikin brain dina..... Yarana su sukaita bani hakuri har akayi bakwai,Hakika naga kokarin Jiddah saboda batacin abinci sai na ci bata matsawa daga inda nake, tana nan makale dani, har akayi Arba'in alokacin na fara sabawa da rubutacciyar kaddarar mu wanda yake hade da RAYUWAR JIDDAH.......Kuma alokacin hutun Jiddah ya kare hankalina ya tashi matuka saboda zata koma, kuma awannan lokacin aka kama wanda ya turo barayin suka kashe Abba da yarana,Amininsa ne wanda suke aiki tare saboda hassadar karin girman da akaiwa Abba shikuma bai kawo rabin matakin Abba ba.....uhmm duniya kenan."ban sa ma iyayenta baki ba haka nabarsu suka tafi da Jiddah, saidai itama da kuka aka rabamu dan sai da suka tabbatar tayi bacci misalin karfe hudu na yamma kafin suka kama hanyar katsina state"Amma me zai faru ko da suka isa cen dinma rigimar ta cigaba dayi ita ala dole sai an maidota wajena, Abbanta baibi nata ba ya fara mata processing makarantar kwana, a Bakori
Ko da ta fara zuwa school din kwata kwata term daya tayi to which aka fara kawo kararta bata karatu, Jiddah datake zuwa na daya a school Amma itace takoma cin na karshe, gashi inta kafe akan abu to saita samu hankalinta zai kwanta, bata kuma cin abinci, don ramar da tayi kadai ya isa ka gane hakan basai anfada maka ba, bugu da kari kuma rashin lafiya ta kwanta ciwo yafi a kirga....ga masifa teacher na class haka zata bude kofa ta fita babu excuse, ga rashin kunya kullin sai sun jibgeta har seniors dinsu Amma shi kanshi principal din yakasa gane inda ta dosa don akullin sai ankawo mashi kararta akalla sau ashirin, ya daketa ya gaji hakan bashi zaisa gobe ta kuma aikata wani laifin ba.......daga karshe dai
Bayan anyi hutu ne principal yaba ma iyayenta shawara akan wata kila akwai abinda take sone bata samu ba, shiyasa take misbehaving.....su zaunar da ita su tambayeta damuwarta donshi ko dariya bai taba ganin tayi ba.
Abba yace dashi toh zaiyi bincike akanta.
Awannan lokacinne Ummi ta zauna da 'yarta ta fahimceta sosai at the end kuma ta yanke shawarar bani ita ganin abinda Jiddah take so kenan......dukdama itama Ummie ta zauna awajena kafin tayi aure....a kaduna tayi karatu (Kadpoly)
To wannan shine silan dawowar Jiddah waje na, hakanan tafara debe min kewar yara na dana rasa, kumà hakanan na daura mata son duniya wanda ji nakeyi kaman daga cikin Jikina ta fito,Hakika shakuwar mu da Jiddah daban ne wanda ko Ummi bata Isa ta Shiga tsakaninmu ba, Haka Abbanta yanaji yana kallo tilon yarsa mace daya wanda itace sanyin idaniyarsa kuma daga kanta har yanzu Ummi Bata sake haihuwa ba but, tadaiyi miscarriage so biyu, shiyasa  Abba yake tsananin son Jiddah amma haka ya hakura yabar min ita,but, har yau ya hana ni biya mata school fees wai bazai daura min nauyin hakan ba, sannan data gama secondary school ne ya bude mata account yana tura mata kudi akai kai, naso na hana shi Amma sainaga 'yarsa ce' tunda yayi hakuri ya bani ita to danme zan hanashi yi mata dawainiya amma fah hakan bai hanani yi ma Jiddah hidima ba dukdama na hanata anfani da kudin da Abban ke tura mata, saboda komai take bukata Ina yimata shi Jiddah itace farin cikina Fatima,.........
"Ko dana daukota kuwa muka dawo kaduna, daganan Faisal yai mata registration kasancewar lokacin muna Unguwan rimi kafin mu dawo Kinkinau,shiyasa ya nema mata school mafi kusa da inda muke J.S.S 1 aka sanya ta"shi kuma ya tafi Police Academy wudil.
Fatima tayi smiling mai kayatarwa sannan tace exactly Momma wannan ranar itace rana ta farko dana fara haduwa da Jiddah Although bamuyi wani magana ba kasancewar nima ranar aka min registration...ana gamawa aka kaimu class dinmu duk sanye muke da kayan gida....Momma seat daya muka zauna da Jiddah, Amma bamuyi magana ba, the next day ma haka
In short sai da mukayi good 2weeks. Ranar Monday bazan manta ba masu proverbs sunacewa "Don't judge a book by its name"Toh nikam afarko na dauka Jiddah tana da girman Kai ne, Amma daga baya nagane wacece ita.... during  break time na fita cen backyard din school dinmu akwai flowers awajan kuma students ba sosai suke zuwa wajan ba" Ina zaune nikadai  tsahon minti biyar ina karanta wani old story book (King Lion) sai naji taku abayana, ban waiga ba na cigaba da karatu cen naga an zauna kusa dani ko dana waiga sai naga Jiddah ce dukda bansan sunanta ba.....ta zauna abinta hannunta rike da story book thesame as mine idanuwanta suna kan book din....ganin ba kallo na takeyi ba hakan yasa na maida kaina kan book dina, after 5min sai naga an fizge book din, ba kowa bace illah Jiddah na bita da kallon mamaki,....hararata takeyi tana kokarin rufe book din.....zare idanu nayi inacewa don't close it please, ban duba page din danake ba, sai tamin gwalo tana cewa sai na rufe, na tashi Ina binta tana gudu, muna ta dariya har saida muka gaji muka zauna, alokacin Jiddah ta mika min hannunta tace Assalamualaikum am" Hauwa'u Junaid by name and you can call me Jiddah"
Kallon mamaki nake mata nima na mika mata hannu Ina cewa"am Fatima Umar by name"nice to meet you, Jiddah tace "you are welcome"
Tohm tundaga lokacin muka zama aminan juna don dayawa classmates cewa sukeyi mu cousins ne wai saboda sunga rana daya aka kawo mu school, and sai muka barshi ahaka mu Yan uwa ne, shiyasa zumuncinmu yayi karfi.
Fatima tasaki doguwar ajiyar zuciya sannan tace Momma Allah yajikan su Abba da rahama, Allah ya gafarta masu
Ameen fatima it almost 6:30 bazaki tafi ba,ina ganin Jiddah bayanzu zata farka ba."
Eh momma bari kawai na tafi idan ta tashi sai ki fadi mata na wuce....
"Okay then ki gaishe min da Mama kinji
"Inshallah zata ji sai da safe"
"Okay ki kula da hanya fah kinji"
"Toh Momma".

***********
One week later

Ranar Monday itace ranar dazasu fara zuwa SIWES dinsu Jiddah ta samu sauki har anyi discharging dinta."tana cikin daki tana shiri abinta hankalinta kwance, tana gamawa tayi wa Momma bye bye sannan ta wuce,
45min tayi ta isa hospital din anan ta samu Fatima na jiran ta suka jera tare har Lab din inda suka Shiga common room suka shirya cikin Lab coat dinsu mai badge na KASU wanda yake dauke da sunayensu,da course dinsu Biochemistry department.
Kai tsaye reception suka shiga anan suka hadu da External supervisor shiya kaisu kowani bench yayi introducing dinsu, wato a Lab din suna da 6bench ma'ana Reception, Phlebotomy, Haematology, Chemistry, Serology,and Microbiology bench sannan kowani bench 1month zasuyi tunda 6month zasuyi SIWES din. sannan yakai kowannensu bench din dazasu fara,Fatima aka aje ta a reception wajan bada result, Jiddah Kuma Phlebotomy wajan ansan "blood sample".
Jiddah ta samu wasu course mate dinsu suna ta murna ashe basu kadai sukazo base ba.ranar tafara koyon yanda ake ansan blood sample a hannun Fatima, Fatima taji zafi sosai haka tace itama idan zata koya ahannun Jiddah zata koya...Jiddah na tayi mata dariya har suka rabu. Zuwa 1week Jiddah tasan komai na phlebotomy ta iya ansan sample tayi transporting dinsu inside the lab inda ake running test din.

Ayau sunyi 20days da fara SIWES dinsu, kuma tunda suka fara basa fita sai dai idan lokacin sallah yayi kuma suna yin sallah suke komawa ciki, ko abinci sai antashi suke zuwa su ci,yau kam Jiddah tun 10am ta fara jin yunwa tasamu Fatima a reception tace teemah "am hungry please escort me to restaurant"
Fatima tace "yunwa kuma Jiddah yau kuma!
"Nidai idan zaki rakani let's go please"
Fatima tace anhankali"Jiddah can't you see am the only one here and kinsan Oga Abdul da masifa yanzu idan akazo ansan results bana nan, wazai bayar?"
Jiddah ta tura baki tayi wucewarta"
Fatima tayi murmushi tana cewa oooo Jiddah rigima yanzu fushi zakiyi dan ban raka ki ba.
"Jiddah ta wuce ko kula ta batayi ba".
Kai tsaye restaurant ta wuce,samun empty table tayi ta zauna tana cewa ni banma san me xanci ba"bari dai na zauna tukun nayi tunanin har dai ta tashi taje ta zaba abinda zata ci,
20mins tayi a restaurant din kuma ba wani abin kirki taci ba Amma har taji she is okay, tana fita Lab din takoma ko wajan Fatima bataje ba.
Ko data isa phlebotomy din sai taga babu kowa ga kuma patients har uku, haka ta Sanya sabon hand gloves ta fara ansan sample tana cikin yi kuwa saiga wasu sun shigo sojoji ne bata ko daga kai ta kalle su ba ta cigaba da aikinta cen saiga  wata staff soja ce tana cema Jiddah kiyi sauri kigama, zan ansa sample din commander.
Gyada kai Jiddah tayi tana kokarin tashi don ta rigada ta gama diban masu, sai taji ana cewa "No allow her to take the sample" Commander din ya fada yana kokarin zama a kujera...sai alokacin Jiddah tasake kallon shi,azuciyan ta tace wannan sojan dan girman kai ashe dagaske shine commander uhm " tana nan tsaye tana tunani taji staff din na cewa no sir she is learning,let me just collect the samples.
Hafiz ya girgiza kai sannan yace "Nooo let her collect it, don't worry " haka staff din ta wuce ita awajan ta tana ganin bai kamata IT Student su diba ma commander blood sample ba, Amma tunda shi yayi insisting ba matsala ta kalli Jiddah tace please take his sample, make sure  you name it and take it to Haematology bench, tell them that he needs the result now"
Jiddah ta amsa ta okay ma!
kana ta koma ta zauna saman kujeran, ayayinda idanuwanta suka koma kallon kasa don batason ta hada ido dashi, tambayar kanta take Anya zata iya diba masa jinin kuwa,Taya ma zata fara rike masa hannu,sai wata zuciyar tace mata toh sauran mazan dasuke zuwa kike diba masu samples din fah.........tana cikin tunanin taji Fatima nace wa Jiddah collect the sample yana jira.
bashiri tafara kokarin daukar masa,cikin natsuwa ta rubuta suna a containers din sannan ta kama hannunsa batareda ta kalleshi ba,Lord! wani irin shock taji wanda yasa tasaki hannun dasauri lokaci daya ta kalli idanunsa.
Hafiz da tunda take kokarin daukar masa ya koma kallon gefe abinshi aranshi yana mamakin yau bai ga tana masifa ba....ji yayi kawai soft hannunta ya taba jikinshi ta kama masa hannu tana kokarin daura masa tourniquet Amma kuma bashiri ta saki hannun tana kallon idanunsa,shima kallonta yakeyi yana mamakin wani shock dayaji
Jiddah ta kawar dakanta tace "Fatima I cannot collect his sample,can you please call oga musa yana cikin Lab ta fada tana kokarin tashi daga wajan.
Hafiz ya bata rai lokaci daya ya canza fuska batareda kallon taba yace cikin tsawa"Don't you dare move from where you are".

*************************

Happy Reading
Don't forget to
VOTE & COMMENT
PLEASE.

RAYUWAR JIDDAH ✔Where stories live. Discover now