34

172 14 6
                                    

RAYUWAR JIDDAH
Part 2/14
ALKALAMIN DIELAIBRAHIM ✍️

____________________________________
❤️❤️❤️❤️❤️❤️❤️❤️❤️❤️❤️❤️

***********

Ranar da kyar aka iya fitar dani daga dakin" sai da nayi kwana biyu Ina kuka" babu yadda Ummi da Momma basuyi dani ba akan nayi shuru amma na kiyin shuru" shin da wanne zanji da rashin kafata guda ko kuma da rashin lafiyar mijinah"Wanda bakomai ke damunsa ba sai neuronal disorder, cuta ce wanda yake taba kwakwalwa sannan ya sanya kokwanto acikin brain din mutum, sai dai kuma shi Hafiz cutar ta kamashi da yawa wanda ko farfad'owa baiyi ba tun bayan da aka kawo shi asibitin ya farka so daya daga nan kuma ya sake komawa bacci wanda har yau bai tashi ba" kuma likitoci sun tabbatar da yana numfashi" am helpless and no one will understand how am feeling awannan lokacin aka soma shirye shiryen fitar da Yayanah waje domin ai masa aiki a brain dinshi ya dawo daidai kwatsam sai aka wayi gari da wata cuta wai ita Covid-19" aka sanya lock down mai tsanani sannan jiragen dake zuwa kasashe daban daban suma an hana su wannan aikin sakamakon kulle ko wacce kasa da akayi saboda wannan disease din"

Tunda naga haka nace da granny da Daddy da su barni naje asibiti na rinka kwana da Yayanah" Kuma suka amince" dukdama dokar da aka sanya a KADUNA STATE  yayi tsanani amma da taimakon Yaya Faisal da Abba na muka samu aka kaini hospital din " granny ta tafi gida don dama ita ke kwana dashi"

Sabuwar RAYUWA  na fara nida Yayanah wanda har lokacin bai farfad'o ba, kullin zan tashi tsakar dare nai ta sallar nafila Ina rokon Allah daya bashi lafiya, abinci ko wani abu ba damuwa bane saboda komai akwai a hospital din kitchen na kusa damu don haka time din abinci nayi zasu kawo min abinda na zaba, dukdama ba wani ci nakeyi sosai ba, ban kuma damu da rashin ganin family ba saboda nasan ansanya lockdown" akwana atashi yau har munyi wata d'ai d'ai d'ai har wata biyar a hospital" kullin bani da aiki sai dai na tsura masa idanu Ina imagining ranar da zai bude idanuwansa"

3rd September, 2020

Abbana ya tashi da wani ciwo wanda yake numfashi sama sama, Ina hospital aka kirani aka sanar dani sosai na tsorata naji Ina son ganin Abbana, NAFHospital aka kawo shi, likitoci suna ta faman gwaje gwaje atunaninsu corona ce amma da aka duba sai aka ga ba ita bace,  amma sun kasa gane takamai mai abinda ke damun Abbana ga numfashin sa yaki dawo wa daidai"
Kwanan biyu kacal a hospital akwana na uku ne Ina ward din mijina, Abbana yasa aka kira masa ni" naje na ganshi Ina kuka yana kuka Ina tayi masa addu'a" Abba yace Alhamdulillah Allah na gode maka dayasa na aurar da 'ya'ya na biyu da raina" ya dube ni ya rike hannayena da karfinsa yace Mamana ki kula da mijinki" kuma ki kula da Ummin ki" Ya kara cewa Mamana ki bautawa Allah mahallincinki kamar kina ganinsa kuma ki kiyaye fushin Ubangijin ki" kibi mijin ki sau da kafa" insha Allah zai samu lafiya kinji mamana"

Kuka ya kufce min nace Abba inshaAllah zan yi abinda kace Amma kaima zaka samu sauki da yardar Allah kaji Abba"
Abba cikin Jin ciwo ya girgiza kai ya kalli Ummi wacce take gefensa idanuwanta sunyi jazir yace a'a Ummi addu'a zakiyi min awannan lokacin ita nafi bukata akan komai" ya kara cewa Ummi ki kula da kanki kuma ki kula da amanar yaran mu" Ummi tace haba Abba kayi shuru mana kana ta wasu irin maganganu haka" kowa awajan ya tausaya wa halin da Abba yake ciki, lokaci  daya ya rame, yai fari" Saifullah shi yake tayi masa Addu'o'i a ruwa yana bashi yana sha" Muhammad kuma yana gefensa yana karanto masa Addu'o'i shi kuma Abba yana kamawa tsahon minti arba'in mukayi a haka mun kasa yin nisa dashi" gashi ciwon sai karuwa yakeyi nikam ma kuka kawai nake ta famanyi toh naga fah an sanya masa drip tun safe amma ruwan baya tafiya, baya shiga jikinshi ko kadan" ga jikin yayi sanyi kararau sai zufa daya keto masa a goshi" muna zazzaune misalin karfe hudu 4 Abba yace Ummi kiyimin alwala zanyi sallah"
Ummi tai masa alwala su Yaya muhammad suka fita don zuwa masallaci, ni da Momma muka fita muma waje zamuyi sallah bamu jima ba muka dawo dakin sai muka iske Ummi na kuka ta rirrike Abba wanda ya sassadare yana ta mimmikewa idanuwansa kuma suna kara kallon sama" Ummi nata yimasa kalmatusshahada shi kuma yana amsawa irin a zabure" Momma ce tai saurin rufe min idanu sannan muka juya muka bar dakin Ina cewa momma barni naje wajan Abba mana bakiga baya da lafiya ba, zan mishi addu'a ne" amma Momma tai kaman bata ji ni ba a waje muka zauna gashi kafa daya gareni dana shiga ciki da gudu"

RAYUWAR JIDDAH ✔Where stories live. Discover now