14

216 17 23
                                    

RAYUWAR JIDDAH
Part 1/14
Mallakin DielaIbrahim

***********
"Jiddah ta soma karantawa"

*Hauwa'u* naso ki same ni but quite unfortunate for me before you arrived aka kirani for some important issues and i have to go,
you mean alot to me but, for now kimin uzuri please
Thanks much for coming, zuwanki ma kadai ya isa nayi farin ciki amma abinda zai kara sani murna shine ki samu ki karanta previous letter din dana baki kinji *Hauwa'u*
Thank you once again.""""

Ita kam ji tayi kaman yana kusa da ita,ji tayi kaman tana jin kamshin turaren shi, she never knew that she's gone too far, how did she even fall in love without her knowledge, ta cigaba da cewa to wannan ma shi bai fito yace yana sona ba , and here I am sai faman jin dadi nakeyi....Jiddah tai ta faman surutu ita kadai cen taji wani zugi akafarta sai alokacin ta kalli kafar, taga Ashe fa ciwo taji tsaki ta buga tana sake kallon hall din wanda har lokacin wakar ne ke faman tashi Kuma at the same time shaukin soyayyah na kamata, tace yanzunan this is all for me, saboda ni yayi decorations dinnan taji kuma ra'ayinta ya kuma canjawa taji aduniya kaman ta rufe ido ta bude taga Hafiz agabanta...in short ba ita tabar wajan ba sai misalin karfe 6:40pm an fara kiraye kirayen sallah, da kyar ta samu Napep ta hau har gida ya kaita saboda wani zazzafar ciwon kai daya kamata, daki kawai tawuce batareda ta duba Momma ba tana shiga bedroom dinta kuma taci karo da box dinta wanda tabari saman gado......tsayawa tayi tana tunanin ta bude ko karta bude and then she concluded by going straight to the box, ta fara ciro letters din da take saving, letter har hudu tace bari na bude naga miye aciki.
Dukdama batsan wanne ne first one ba rufe ido tayi ta kai hannu ta cinka sannan ta bude ta fara karantawa taga bazata gane ba sai ta fara daga na farko hakan yasa ta rinka dubawa daya bayan daya tana jerasu accordingly har takai na karshe sannan ta fara karantawa kamar haka.
The first letter (chapter 10)

Hauwa'u
Please be a fan of Hijab
because it suit you more than you think of, to tell you the truth ganinki da dan kwali kadai no veil yasa naji kishinki azuciyata kuma naji yakamata na baki advice,
am looking forward to see you in Hijab tommorow inshallah!!!

And the 2nd the second letter:

Hauwa'u
Today's outfit was so cute
Actually,I was very excited by seeing you in Hajib today
Nagode sosai
Bye!!!

3rd letter

Ki rage masifa Hauwa'u because it doesn't suit you!!!

4th letter

What you did today was so bad
Though I punished you because
baki tashi yimin magana ba sai da muka Isa gate But, am so sorry by dropping you at home nayi hakan ne don ki gane mistake dinki.
By the way,you look good today I like the outfit brown Hijab it's actually looks good on you
Hauwa'u!!!

Jiddah tasake karanta letters din akaro na hudu gaba daya maimaitawa takeyi uncountable har bacci ya dauketa tana tunanin Hafiz ta kosa jibi yayi ta samu ta ganshi a hospital.
******Monday*****
Jiddah na isa hospital ta wuce Lab direct Allah ya taimake ta ma week din zasu gama so babu wani work din da sukeyi.
Ta samu Fatima ta bata labarin abinda ya faru, Fatima ce tai ta faman rakata suna duba Com.Hafiz Abubakar amma har closing time yayi bai iso hospital ba.....Haka Jiddah ta jera sati tana jiran ganinsa amma shuru baya zuwa ranar da zasu kare SIWES sukayi hotuna da colleagues dinsu da staffs din Lab da oga c.o da sauran kawayan dasuka hadu dasu awajan.
Jiddah duk abinda akeyi hankalinta baya wajan Fatima ce ke faman rike mata hannu tana janta ta koma kaman wata gunki hotunan ma babu ko dariya haka take dauka, Fatima tayi tayi akan Jiddah ta saki fuska amma ina, sanin halinta yasa ta rabu da ita and at the end ta koma lallashinta,suka ansa certificate dinsu ahanyarsu ta tafiya ne sukabi ta office din Hafiz sunyi sa'ar samun M.malunfashi a office din Jiddah ta sauke ajiyar zuciya hade da hamdala ta shiga office din tace
Ina yini!
Lafiya lau ya amsa mata cike da annuri a fuskar shi.
Sai kuma ta rasa me zatace Fatima ce tayi karfin halin cewa sir. muna neman commander ne?
M.malunfashi yace Commander bayanan,he's out of the country.
Jiddah tace yaushe zai dawo please
"Yace gaskiya dawowarshi ba yanzu ba sai dai ku dawo nan da sati biyu zuwa uku.
Haka Jiddah ta koma gida helplessly tun daga ranar annurin fuskarta ya dauke, Jiddah mai tsokana a gida ta koma Hi Hi, yanzu ta dawo very silent to which har fever ya fara kamata saboda yawan tunani kullin cikin ciwon kai saboda bata taba sanya abu arai irin wannan ba moreover bata iya sa abu arai ba, don ji takeyi kaman zata mutu in bata samu abinnan.
Shiyasa duk sati sai taje base ita da Fatima su duba ko ya dawo amma har yanzu ce mata ake bai dawo ba and M.malunfashi ya bata number din Hafiz amma kullin data kira akashe take jin line din daga baya ma ya dena existing ...har kusan 4weeks tana abu daya wata ranar Monday ta shirya ta nufi base sai ta iske an kawo sabon commander bata ma samu ganin M.malunfashi ba saboda ance mata shima yabar wajan ya koma abuja....ranar Jiddah tayi wani tunanin zuwa gidan su Hafiz tunda ya taba kaita kuma she was very sure gidansu ne don hàka kai tsaye ta sauka a line din tayi knocking kofar.
Tsahon minti goma 10min tana knocking shuru ba a bude ba, har tayi give up zata juya ta tafi sai taji magana daga cen ciki ana cewa "waye"
Da sauri Jiddah tace "Nice"
Ko daya bude gate man ne Mallam dauda "yace baiwar Allah wa kike nema ne?
"Jiddah tace Hafiz nake nema"
Sosai ya kalle ta da mamaki a fuskarshi yace karamin maigida kike nufi koh assha ai yau kimanin wata daya kenan kaf gidan basanan suna kasar waje"
Kut! Ai Jiddah ji tayi gaman an buga mata guduma a zuciya, cikin sanyayyar murya tace kuma ba yanzu zasu dawo ba.
"Malam dauda yace gaskiya bazan miki karya ba ina ganin sun koma cen da zama ne don ko ni ban da masaniya akan tafiyar tasu sai dai na wayi gari nagansu suna shiri kuma basu fada min komai ba illah amanar gidan su dasuka danka min da kuma kudi da suka bani.
Jiddah tayi fuskar tausayi kamar zatayi kuka tace toh shikenan nagode sai anjima, haka ta tafi gida ranar ne fever mai tsanani ya kamata,Hankalin Momma yai matukar tashi saboda Jiddah tana dadewa batayi ciwo ba,infact sai tayi shekara ma ko mura batayi,shiyasa Momma da Faisal duk suka tada hankulansu wanda har ciwon ma yayi tsanani to which har akayi admitting dinta a hospital "Jiddah tana kwance a kafar Momma kallo daya zakai mata ka hango ramar da tayi fuskar nan tayi alamun rashin lafiya sosai ga Faisal a gefenta rike da tea cup yana bata kadan kadan....dukdama ba sha takeyi ba saboda da tasha sai ta amayar dashi.
Momma duk basusan damuwan Hafiz bane ya sanya ta ahalin da take ciki sai da fatima ta samu Momma separately ta fadamata kadan daga ciki,Momma tayi matukar mamaki all this while bata fahimci ina Jiddanta ta dosa ba, take kuma tausayin Jiddan ya dira a zuciyarta hakan yasa tai ta lallaba ta har tasamu lafiya for almost 2weeks tana jinya sannan suka koma gida.
Ba laifi ta warware sosai tana wasu activity dinta na gida amma duk sanda ta tuna cewa letter ta karanta ya janyo mata wannan tashin hankalin sai taji ba dadi, moreover soyayyar Hafiz dayake ta cinta a cikin zuciyarta wanda ta kasa mantawa dashi ko na second daya, ganin haka yasa Momma harhada kaya suka tafi katsina Banda Faisal.
Ranar Asabar da daddare Momma na ta faman hada masu kaya Jiddah na kwance akan gadon Momma tace Momma inajin kamar karmu tafi, kaman zai dawo Jikina na bani kaman yana kusa dani,"Momma tace Jiddah na rabaki da imaginations dinnan Koh, ke da komai sai kinyi imagination kul kar na karajin maganar Hafiz abakinki, kina jina, Jiddah tai fuskar tausayi tace ya hakuri Momma bansan ranki zai bace ba...."Momma ta kalle ta sai taji tausayin ta ya kamata, tace bawai raina yabace saboda Hafiz bane saboda kene Jiddah bana son ganinki awani hali tobe sincere.....Jiddah tace na gane Momma,sannan ta kwanta a saman gadon dukdama tun da suka dawo daga hospital dama a dakin Momma take kwana, Momma tace muje cen idan kina ganin yan uwa zaki manta da komai Jiddah walhy hankalina tashi yake idan Ina ganin ki cikin wannan halin....Jiddah ko bata kula taba sai ma zura mata idanu da tayi.
Haka kuwa akayi ranar asabar suka dira a katsinawan dikko in maku kirarin "katsainawan dikko dakin kara"
Sukace "kunyace gare mu badai tsoro ba"
Barhim Estate suka nufa kasancewar Ammi da Mama suma a estate din suke tun asali babban gida ne Family house
mai dauke da bangarori daban daban part din Ammi daban haka part din Mama daban ga jikokin Mama dasuka cika gidan kasancewar yaranta mata suna da 'ya'ya dayawa.

RAYUWAR JIDDAH ✔Where stories live. Discover now