27

168 25 3
                                    

RAYUWAR JIDDAH
Part 2/27
ALKALAMIN DIELAIBRAHIM ✍️

____________________________________

"Uhmmmmm"
"Cikin dabara da wayo yasamu mai gadin gidan ya tambaye sa, wai me nake zuwa yi agidan"
" Shi kuma mai gadi ya kama zuba ya bada labari dukdama shi awajan shi yana alfahari da abinda nakeyi ne"  😂 harda cewa ai yarinyar nan yar Aljannah ce har wanki da guga take masa wallahi, Kai aradun Allah ka samu mata kaman wannan to kakanka ta yanke saka, Allah Ina gayamaka... Shikuwa yayi godiya yace toh Allah yasa mu dace, yai masa sallama kuwa yabar unguwan.

" Nidai ranar na koma gida naga su Momma basu kulani ba, nayi tadin har na gaji" sai da Uncle ya dawo ya aiko kirana, alokacin ya tambaye ni " waye Abubakar?
Me yake kaiki gidansu? naji tambaya daga sama da mamaki nake kallon ko wannensu, amma kasancewar bana masu karya, hakan yasa na zayyana masu komai tun farkon haduwar mu"dukda Ina ta sakawa araina cewa ai bazasu raba mu ba, beside ni Autan Ammi waya isa ya rabani da Abubakar"" na kuma shaida musu shi nake so na aura"
"Momma tace  aikin me yakeyi?
"Nace koyarwa yakeyi a wata private school" tace toh Allah ya tabbatar da abinda yafi alkahiri Amma kada ki sake zuwa gidan saboda budurwa bata zuwa gidan saurayi kina jina ko" na gyada kai nace mata eh naji" tundaga ranar kuwa ban sake zuwa ba sai ma shi daya samu sauki shi yake zuwa, Uncle ya karbe sa hannu biyu sannan suka bamu damar shimfida soyayyar mu hankali kwance" har tsahon shekara uku nagama Kadpoly" Ammi tace tunda na gama karatun nazo hutu katsina" nida Abubakar muka tafi yaga gidanmu na katsina sannan ya juyo batareda sanin Ammi ba" not knowing that am making things to be worst again,  one week later Abubakar yazo" muka sha soyayyar mu agidan su sa'adarh without Ammi's knowledge har ya tafi", Wata ranar sunday akai wa Ammi rasuwa childhood friend dinta ne ta rasu sunanta HAUWA KULU anfi kiranta da KULU, tare suka taso tun suna yara, ita sai tayi aure a Nijar, Ammi tace na shirya muje Nijar, nako shirya tsab, muka kama hanya har *NIJAR REPUBLIC(Maradi)*
Muna zuwa mu kayi gaisuwa kasancewar Ammi tasan yan uwanta haka tazake wajan yin hidiman rasuwa, Ni kuma ganin kar nazame mata liability  sai na fita waje na zauna akofar gida Ina ta kalle kallen mutane, because that was my first time being there * Maradi * Garin ba laifi akwai kyan gani kuma dai gadaishi kaman a Nigeria muke Amma al'adu da abincin su da yanayin rayuwar su, da yanda suke shiga duk sune suka banbanta  da namu"
Sa'annan su yan Nijar daka gansu zaka gane su kamar yadda muma idan kazo Nigeria zaka ga duk kalar mu daya"
" Ranar na hadu da "JUNAID MUHAMMAD"(Abba) ganinsa danayi bawai na masa kallon aure ko wani tarayyah atsakaninmu ba, nadai kalle shi yana kokarin shiga gida.....naji yara yara da suke zazzaune kofar gida suna fadin ga Dan kulu, ga Dan Kulu kasancewar shi Da daya tilo awajan *KULU*  mai rasuwa kuma dalilin wannan ihun nasu ya samo asali ne da duk sanda zai dawo sai yayiwa yan unguwa tsaraba haka zai tara su yaita raba masu* Biscuits* *Chewing gum* *Alawa* dadai sauransu* saboda ba a maradi yake karatu ba, kunsan su yara babu ruwansu, dukda rasuwa akaimasa amma ba wannan suke dubawa ba, sukam dan alawar dayake rabawa ita suke mawa.... asalima ranar ya dawo daga * Yamen* Jin rasuwar mahaifiyar tashi" Ni ko na dan waiga don na ga dan kulun da ake fada, kallo daya nai masa na juya Ina tausayinshi araina nace Allah sarki Mamanshi ce ta rasu, amma su kam yanzu sai faman ihu suke wa mutane, shima hala yana Jin yadda naji lokacin da Abbana ya rasu....na cigaba da kalle kallen mutane har yamma tayi Ammi ta fito muka koma gida, bayan mun koma gida da sati daya sai mukayi bako, Ina kwance a daki sai Ammi ta shigo tace Halima taho ku gaisa da yayanki"
Nayi mika Ina cewa Ammi wani Yaya kuma?
Tace dan Aminiyata *KULU* mana." Sai alokacin kamanninsa suka soma dawomin nace to Ammi gani nan, na sanya Hijab daidai gwiwa na fita na sameshi a falo kuwa cikin Shiga ta Alfarma" na zauna asaman carpet na gaidashi cikin girmamawa"..na kara yi masa ta'aziyyah sannan daga bisani nayi shuru shima kuma yayi shuru" har ya gama zaman shi sannan yai wa Ammi sallama shi zai koma, Ammi tace Halimatu tashi ki rakashi wajan motan ko" ba musu na tashi na rakashi, sai yayi min kyautar kudi, kudin yan Nijar ni kuwa na ki karba, yayi juyin duniya akan na amsa Amma naki, hakannan ya hakura ya tafi, * kwana ki nata tafiya hutun zama waje daya ya ishe ni, hakan yasa na fadawa Ammi zan koma kaduna naga su uncle, tace min toh bakomai"  Ina nan dai Ina ta shirin komawa kaduna saboda Abubakar, sai na fara Jin maganganu from nowhere, da fari dai kudin gaisuwa aka kawo, daga bisani aka kawo kayan sa rana" duk ban dauka nau bane" na shashantar da maganar ban tambayi Ammi ba" Ana gobe zan koma ranar Abubakar yazo kuma ranar Ammi tasan da zaman sa saboda ya taho da iyayanshi da yan uwanshi dama Uncle akan anzo nema masa Aure na"
" Bakaramin farin ciki nayi ba dajin wannan maganar, ranar na fasa asusu na na kwashi rabin kudin na siyo Alawa nai ta aikin rabawa yara, har da almajirai harda wa inda basunan sai da nabi gida gida Ina bayarwa akan a ajiye masu, Ammi na kallo na bata ce min kala ba, sai bayan da zasu tafi * Ina waje nida Abubakar* suka kuma bakin suna cikin gida Ammi tace dasu suyi hakuri su tafi da kayansu ita ta rigada tamin miji, anan aka kwaso kayan sa rana duk suka gani kuma sukayi na'am, sukace to ai basusan an sanyamin rana ba da babu abinda zai kawo su"
Haka dai suka bada hakuri suka fara shirin komawa, muna waje nida Abubakar muka ga sun fito fuskokin su babu annuri" Uncle shi yayita basu hakuri Yana nuna musu cewa baisan komai ba, daya sani bazai basu kwarin gwiwar zuwa ba, suma suna kara jaddada masa akan kada ya damu sun fahimta ai" kuma ma ai ya musu karamci tunda ya amshe su hannu biyu, suma sunsan ba laifinsa bane, ni da Aubakar muna cikin duhu, sai faman kallonsu mukeyi mun kasa ce musu komai, sai daga baya Mahaifin Abubakar ya umarce shi daya shiga mota su tafi, dukda yana son ya tambaya Amma ba'a bashi damar tambaya ba" nai masa bye bye shima kuma yamun,muna ma juna murmushi" har saida na daina hangen motar tasu sannan na koma cikin gida" na zauna Ina bawa Ammi labarin soyayyar mu da Abubakar all my taught was Ammi ta amince dasu" tsawa ta daka min wanda ya firgita ni, saboda tunda nake Ammi bata taba yimin tsawa ba balle fada,....naji tsoro matuka hakan yasa na boye abayan Uncle da Mama, anan Ammi tace ba Abubakar zaki aura ba Junaid zaki aura" Alokacin na soma tunanin waye ma Junaid, and ina na sanshi da har Ammi zata ce shi zan aura, Noooo bazai yu ba, ABUBAKAR nake so kuma nasan Ammi na bazatai min Auran dole ba* na rarrafa na nufi wajan Ammi with my confidence, da wani irin courage don ina tunanin Ammi bazata taba so raina ya baci ba,saboda nasan irin son da take min" nace Ammi Abubakar nake so, ni bansan wani Junaid ba yaushe yaushe na ganshi Ammi, Ni wlhy bashi nake so ba" Ammi tace Junaid Dan kulu shine zaki ce baki sanshi ba Halima, to wlhy baki isa kisa nayi magana biyu ba" bana magana biyu sannan kisanya aranki cewa Junaid zaki aura, shine mijin ki" ta kara da cewa ko bakiga sun kawo kayan sa rana bane so kike yanzu na cemusu an fasa kisa naji kunya, to bazai yu ba kina jina, na gama maganata
ke bakisan yanzu lokaci kawai muke jira ba""" Inna lillahi wa'inna illaihir raji'un 😣 ai kukan ma ya kasa zuwa, sai wani irin trance dana shiga, na kasa motsi ko kadan, tun daga lokacin na dena walwala, babu irin magiyar da banyiwa Ammi ba amma tace ita sam JUNAID zan aura,"Watarana da tsakar rana na saci dari biyar a saman dressing mirrow dinta ko kaya ban hada ba, Hijab na sanya da silipas na nufi park, nako samu mota nace kaduna zani, nahau muka nufi hanyar kaduna wanda bamu muka Isa kaduna ba sai karfe bakwai na dare, kai tsaye gidan su Abubakar na nufa, mai gadi da kyar ya gane ni, duba da yanayin shigata ya  barni na shiga gidan, na samu mummy ( granny ) Ina kuka, tai ta lallashi na har Abubakar ya dawo, batareda tunani ba na rugume shi Ina kuka mai tsuma zuciya, ya kwantar dani akafadarshi yana comforting dina to which da kyar na samu natsuwa nayi shuru yajani zuwa inda Mummy take ya zaunar dani, sannan yace Ina jinki yimin bayani Halima"na bude baki da kyar na fada masu yanda akayi, Abubakar yace Nima haka Abbana ya fada min"
Da sauri na dago kai nace to yanzu ka yadda a raba mu kenan?
." Abubakar yace aa Halimatu, nayi attempting komawa katsina but, Mummy ta hana ni, ta nusar dani akan cewa lallai lallai na dauki dangana idan Allah yayi ke matata ce to babu makawa za'a daura auran mu"hausawa suna cewa matar mutum kabarin sa na zuba masa idanu, na kasa cewa komai, har ya tambaye ni daga Ina nake saboda ganin irin shigar danayi" Nace daga katsina nake kuma babu wanda yasan nazo"
"Sosai suke ta mamaki, na taho all the way from katsina, it's  5hours journey and the worst part of it shine babu wanda yasan na taho , Mummy tace maza Abubakar kaita gida kaji" Hakanan na tashi ya kaini gida, kamar daga sama su Momma suka ganni, Momma tace ke lafiya daga Ina kike" miya kawo ki kaduna cikin darennan?" Sai kawai na fashe da kuka, taita lallashi na, har bacci ya dauke ni, Ashe Ammi suna ta faman nema na, sanin babu inda zani sai *Kaduna* shiyasa itama washegari ta shirya ta taho kadunan.....Ina kwance kan cinyar Momma tana lallashi na kasancewar ta Yaya kuma uwa awajena" sai kawai muka ji muryar Ammi daga sama ko data shigo, duka ta fara kaimin da hannu ta ko ina, Momma na ta rike ta, har sai da Uncle yazo ya ceceni....hakika rànar naga ikon rabbi😂
" I never knew that haka Ammi take da zafi, I was irin like ni Auta ce tayaya za'aimin auren dole" not knowing that it's a bad taught for me hmmmm"Ina nan ina shan duka" kuma tana gama duka na ta kama hannu na wai aranar zamu koma katsina" naita magiya ina rokonta Amma ina, muna bakin kofa zamubar gidan sai ga Abubakar, Ranar itace ranar rabuwarmu ta karshe dashi."

RAYUWAR JIDDAH ✔Where stories live. Discover now