16

191 23 12
                                    

RAYUWAR JIDDAH
Part 1/16
Mallakin DielaIbrahim
Jumma't Mufeedah 🕌

Katsina state
K/dara specialist hospital
____________________________________

Duk sunyi jugum suna sauraron Dr.majdeed, suna fargaban Jin abinda zai fito daga bakinshi, amma kuma dukda fargaban suna bukatar sanin halin da Jiddah take ciki.
Dr.majeed ya jinjina kai yace kuyi hakuri Hauwa'u Junaid loss her vision due to hypertension, analysis din danayi na gano Jiddah tana da damuwa azuciyarta,wanda ake kira High Blood Pressure, and shi high blood pressure idan yayi yawa sometimes yana damaging tiny delicate blood vessels Wanda yake supplying blood izuwa idanun mutum,muna kiran hakan da Retina,which can lead to bleeding in the eye, daganan sai kafara gani dishi dishi(blurred vision) Kuma daganan sai ka makance(loss of vision). just like yadda yadda faru da JIDDAH, so yanzu yanda za'ayi curing ciwon nata shine main point dinmu, akwai wasu drugs dazan daurata akai na hypertension sai mun fara controlling and lowering din high blood pressure dinta kuma inshallah vision din zai dawo, inshaAllah za'a dace....Dr. yadan tsagaita ganin dukkansu sunyi fuskar tausayi, sosai yakejin tausayin JIDDAH aranshi shima.

Hawayen da momma ke boyewa ne suka soma saukowa, Ummi kuma ta girgiza sosai to which sai da Abba ya rike ta,babu wanda baya hawaye acikinsu illah Abba, faisal,Muhammad and Saif da sukayi ta maza Faisal ya kama Momma da kyar ta iya takawa suka bar office din sai daya zaunar da ita shima ya zauna sannan Ammi suka biyo bayansu dasu Abba, Ummi ta kalli Momma sai taji tausayin Momma ya kamata, Ammi koh bata da bakin magana ta samu waje daga gefe ta zauna cikin ranta kuwa tana danasanin abinda ta aikata, dukda arashin sani tayi komai ita burinta kawai ahada auran zumunci duk bata duba abinda zaije ya dawo ba, yanzu ga abinda ta jawo.....tana cikin tunanin ne taji Ummi na cewa Momma ki yafe mana don Allah, da bamu fara kawo maganar auran nan ba da hakan bazai faru ba.....
Momma tace shihhhiiiiiii 🤫 ba laifin ku bane Ummi kada kuyi blaming kanku, komai daga Allah ne, yanzu Kam ya rigada ya faru sai dai muyi fatan Allah ubangiji ya bata lafiya.
Daga nan sukayi shuru babu mai cewa komai kuma basu tafi gida ba anan sukayi kwanan zaune har asubahi tayi Abba,Faisal, Muhammad da Saif suka tafi masallaci, sukuma matan anan sukayi sallah.
Ammi ta kara bawa Momma hakuri akan abinda ya faru amma still momma na fahimtar dasu cewa daga Allah ne, kuma shiyasan dalilin faruwar hakan,sannan kaddarar Jiddah rubutacciya ce ko basuyi maganan aure ba idan Allah yayi zata makance dole sanadi ya faru,dama komai akwai sanadi don haka su kwantar da hankalinsu su rinka mata addu'a kawai.
Da safe suka koma wajan Dr.majdeed don Jin sauran bayanai akan ciwon idanun nata.
sunyi sa'a he is less busy hakan yasa suka shiga gaba dayansu.
"Momma tace likita kamar yadda ka fada jiya yanzu muna so a fara mata treatment cikin gaggawa"
Dr.majdeed yace Hajiya za'a iya farawa amma karkice cikin gaggawa, kudai kuyi fatan Allah yasa ta samu lafiya.
Dukkansu suka amsa da ameen sannan suka koma dakin da Jiddah take, tana kwance idanuwanta a lumshe kaman mai bacci, ko data ji shigowan su tayi saurin bude idun tana juyowa ta setin inda take jin hayaniyar su tace "Momma"
Tsaye suke suna kallonta cikin fuskar tausayi, kowa da abinda yake sakawa acikin ranshi.(wai yau Jiddah ce ta makance)
"Momma ta nufi wajan da gudu cikin muryar ta mai rawa tana kuka tana cewa Jiddah na, Autana ya idan ya dena miki ciwo?
"Jiddah ta kankame Momma tace cikin muryar kuka da tausayawa " Momma bazan kara gani ba ko,bazan kara ganin kuba da yaya faisal da Ummi, wayyoooo Momma na shiga ukk...........
Momma ta toshe mata baki tana cewa kul! kar na kuma jin kin fadi haka waya  fada maki bazaki kara gani ba" Inshallah zaki samu lafiyar ido bi'iznillah.
Sauran suka amsa da Ameen" "Jiddah tace Momma Ina Ummi da Abba?
Momma tace gasunan, ta fada tana waigawa wajan su tana cewa ku matso kusa mana....sai alokacin hawayen da Ummi ke boyewa ya soma zuba, ta nufi inda diyar tata take ta zauna kusa da ita ta kira sunanta ahankali; "JIDDAH"
Jiddah tunda taji muryar Ummi tagane kuka takeyi tayi saurin Kai hannu ta lalubo fuskarta har takai hannunta saman idanun Ummi ahankali ta soma wiping mata tears din tana cewa Ummi nah dena kuka haka Allah ya kaddara min,Ummi kimin addu'a  kinji sai kuma kuka ya so ya kwace mata tayi shuru for a seconds tana kwance jikin Ummi, Ummi na bubbuga mata baya ahaka bacci ya dauki Jiddah Ummi ta gyara mata kwanciyar.
Sai suka fita gaba dayansu suka koma reception anan ne suka soma tattaunawa akan maganar.
"Abba yace naso dafari akaita India Amma tunda Dr.majdeed zai yi iyakan kokarin shi akai, so in my opinion mu jira mugani
Ammi tace"eh hakan ma yayi Allah yasa mu dace."Ameen su ka amsa.

RAYUWAR JIDDAH ✔Where stories live. Discover now