04

353 30 0
                                    

RAYUWAR JIDDAH
Part 1/04
Mallakin DielaIbrahim

*******

Jiddah tunda taji anbada umarni atafi da ita, kuma sannan ita bataji muryar mutumin daya bigesu ba tayi saurin dago fuskarta don ganin wanda yayi causing accident dinnan. So take tai mashi masifa kamar yadda zuciyarta take tursasata,so take ta nuna mashi taji zafin abinda ya sameta don ita gani take baima damu ba daga yanda taji escorts din na bada umarni.....ta runtse idanuwanta ayayinda take kara jin wani zafin ciwon na ratsa ko ina na jikinta....daurewa tayi ahankali take bude idanunta tafara kallonshi tundaga kasan takalminshi harzuwa saitin fuskarshi amma bata iya kallon fuskar ba tai saurin rufe idanuwanta tana tuno surar jikin nashi,
"Dogone sosai mai dan kumari,haka zalika farine tas wanda zaka iya kiran farin nashi da yellow saboda zabar turuwar hasken fatar tashi,kallo daya zakai masa ka kiyasta shekarunsa,"He is very young and handsome",ayayinda yake sanye da uniform na airforce sky blue din riga inda tasha ado da rank a shoulder,sai wasu igiya da aka sanya suka kara fito da kyan rigar sai trouser din dark blue sai wasu black cover shoe dasukai matukar yi ma kafar kyau, gaskiya tunda take a duniya bata taba ganin mutumin da kakin soja yai mashi kyau ba irin wannan sojan, lokaci daya taji tana son taga fuskar shi......Jiddah ta kuma runtse idanuwanta tana shirin budewa ne taji Fatima nace mata, Jiddah muje koh aduba maki hannun kowa ke yake jira.
Sai alokacin ta dawo cikin hayyacinta, sai asannan taji tana jin haushin kanta da batai mashi masifa ba, ta tsaya kallon abinda bazai anfane ta da komai ba....tsaki tayi wanda yasa hankalin kowa ya dawo kanta, pouting baki tayi tana galla ma mutanen harara kamar sune sukai mata laifi ayayinda ta hangi sojan yana gabanta Amma ya juya baya bata iya ganin fuskar nashi kuma yayi nesa da ita yanzu......wani irin karfin hali tayi at the same time ta nufi inda yake tasha gabanshi cikin sauri sannan ta daga kai ta kalle shi cike da masifa afuskarta...Daga hannu tayi zata fara magana amma mistakenly ta fama hannu mai ciwon, Auchhhh😣ta saki kara kadan sannan ta kuma kallon shi ta daure fuska ta sake pouting karamin bakinta dayan hannun ta daga ta nuna shi tace" who do you think you are? Kayi ma mutum laifi bazaka iya bada hakuri ba, ta galla masa harara sannan ta cigaba dacewa wallahi kaci sa'a hannu na yana min ciwo dasai na nuna maka ko wacece Jiddah Junaid.
Wani soja ne yayi saurin karasowa wajan Yana cewa ke bakida hankali ne shin kinsa ko waye tsaye agabanki kike yima magana haka babu respect aciki, are you out of your sense?
Kallon sojan tayi cike da masifa tace kaikuma waya tsomo bakinka aciki sai ka koma inda kake nikam banyi dakai ba, dana sama dakai nake ta karashe maganar tana nuna sojan da hannu.....
Rai bace escort din ya bude baki zaiyi magana Amma me.............
Sojan yayi saurin dakatar dashi da hannun, abaki kuma yace cikin tsawa M.malunfashi"keep quiet and go back to where you are please'
But, sir........ya kuma daga masa hannu wannan karan baice komai ba.....ya maida dubansa ga Jiddah, kallan cikin idanunta yayi,Amma Jin zuciyarshi ta wani irin bugawa mai karfi,wanda yasa kansa sarawa. Rasa abinda zai cemata yayi sai kawai yasaki murmushi lokaci guda fararan hakwaransa suka bayyana, to which kyawunshi suka kara fitowa, kafin yace " Sorry Ma'am" cikin sanyayyar muryar sa, yana kaiwa nan ya gota ta gefen ta ya wuce, sauran ma suka bi bayansu akabar Jiddah tsaye, Fatima ta dafa shouldern Jiddah tace zo muje rabudashi ko yaki ko yaso shine da laifi ae.
Jiddah tace teemah kina kallo ko hakuri bai bani ba, nikam babu inda zani ma.
Fatima ta zare idanu tace Jiddah kiyi hakuri don Allah mubisu a duba maki hannun ki, kin manta inda muke ne Jiddah, gidan sojoji fah muka kawo kanmu don haka dole muyi biyayyah, please rabudashi kinji kizo muje aduba hannun, Tsuke bakin ta kumayi kafin tayi gaba ko magana batai ma Fatima ba.
Fatima kam girgiza kai tayi aranta tana cewa Jiddah kenan kafin ranta ya bace ana jimawa, Amma idan rannata ya bace to komi taga daman yi, yi zatayi, ta girgiza kai sannan tabi kawar tata da gudu.

Accident and Emergency (A&E)
Suka Shiga sai da ta hada ido da sojan yana yiwa Dr. Bayani, ta gallah masa hararar da saida yasha jinin jikinsa, Kuma lokaci daya ya dauke kanshi daga kallonta.
aka bata gado sannan  aka fara duba hannu, babu abinda take fadi sai Inna lillahi wa'inna illaihir raji'un,tsabagen zafin da ciwon da hannun ke mata hakanan ta aje hannun gefe guda doctors biyu ne akanta suna duba hannun....tsabar zafi yasa hawaye ne kawai keta zuba a idanunta ayayinda ta lumshe idanun don hawayen ma ta gefen ido ya ke diga, basu bata lokaci ba akai mata allurar pain relief.
"Tun bayan da ya bada umarni aduba Jiddah, ya nemi waje ya zauna a kujerar dake wajan bench din doctors, sannan sojojin dake biye dashi su biyar, uku abakin kofa suka tsaya biyu kuma suna gefen sa, da alama escort dinsa ne, tunda ya zauna yake danne danne a iPad dinsa to which kana ganinsa zaka dauka bashida wata damuwa a tattare dashi Amma deep inside him yana mamakin yarinyar da karfin hali irin nata.
Hakanan ya damu da kukan da lady din takeyi kuma yana blaming kanshi, sannan time to time yakan kalla wajan da Jiddah take hakanan yana jin yadda zuciyarsa ke masa quna saboda ya tsani yaji kukan mace arayuwar sa, she yasa baya kula mata ko kadan"and yau sai gashi duk ignoring mata dayake tun tasowarshi yau shine accident ya hadashi da mace...... Although he's responsible for everything that happened and that's why his heart is completely shattered yanda yaga tana hawaye yasan definitely bakaramin zafi hannun ke mata ba......aranshi yace what kind of accident is this, how did it happened? Shi bai ma taba tunanin cewa abin yakai har haka ba to dole yace haka mana,...dafe forehead dinsa yayi yana tunanin abinda ya kawo shi hospital din, dukdama bai hadu da wanda yazo gani ba,and time nata tafiya ko fara processing project din daya zo yi base din baiyi ba.......maganar da ake mashi ne ta fitar dashi daga trance din daya shiga lokaci daya ya maida hankali ga wanda ke masa maganar.
Sir bamuje mu mungana dashi ba and time din Daya bamu is going,ko zamuje yanzu ne by then nasan sun gama dubata....Daga masa hannu yayi yai stopping dinshi,hade da girgiza masa kai yana kuma mashi nuni da hannu alamar ya tafi lokaci daya kuma yana cigaba da tapping IPad dinsa.Bashiri kuwa escort dinshi yabar wajan ganin yadda fuskar ogan nasu ya koma lokaci guda, baya ko smiling ganin hakan yasa ya koma bakin kofa kawai inda sauran colleague dinshi suke.Tsahon minti goma suka dauka suna taba hannun kafin suka koma bench dinsu suna tattaunawa.
Lokaci guda sukayi gyaran murya sannan suka nemi attention din mutumin hade da yima sojan bayani ta yadda zai fahimta ayayinda Fatima ke sauraron su...inda suke cewa suna tunanin gocewan kashi ne ba karaya ba, Amma yanzu za'ayi mata X-RAY don su tabbatar da matsalar da hannun ya samu.
Mutumin ya gyada masu kai kawai batareda yace komi ba kuma fuskar nan tashi tana nan yadda yake, babu ko fara'a.
"Fatima hankalinta duk atashe yake ta kalli sojan rai bace dukdama shi ba ita yake kallo ba, ji take kaman ta rufe shi da duka saboda ganin kaman girman kansa yayi yawa dukdama ga wani respect da taga ana bashi, don duk sojan dazai shigo wajan sai ya gaishe dashi cikin ladabi hakanan kuma he is not even saying a word sai dai ya daga masu hannu ta lura tunda abin ya faru ma bai ko furta koda kalma daya ba da hannu kawai ko da idanu yake magana, hakanan zuciyarta tabata kaman bai damu da abinda yasamu kawar tata ba ma,harara takai masa wanda ake cema harara aduhu, don kuwa shi baimasan tanayi ba, take kuma ta sake jin haushin shi aranta ....dauke kanta tayi daga kallon sa tayi saurin dena tunanin da takeyi ta share guntun hawayen ta daya zubo mata,ta dubi wasu likitocin dasuka zo tafiya da Jiddah wajan X-RAY din suna magana da doctors....dasauri ta nufi inda kawar tata take, da tayi shuru kaman mai bacci.
Ahankali tace JIDDAH!

RAYUWAR JIDDAH ✔Tempat cerita menjadi hidup. Temukan sekarang