35

147 13 7
                                    

RAYUWAR JIDDAH
Part 2/15
ALKALAMIN DIELAIBRAHIM ✍️

____________________________________
❤️❤️❤️❤️❤️❤️❤️❤️❤️❤️❤️❤️

Bayan sun isa kasar, suka tafi hotel din dasukayi booking tun kafin zuwan su" the next day suka tafi babban asibitin kasar"

Anan suka hadu da likitan dazai musu aikin wanda Daddy ya riga da ya tura masa komai ta email,
Likitan yace am so sorry sir amma aikin dazamuyi masa yana da matukar had'ari, zai iya samun lafiya, zai iya kuma asamu akasin haka" Daddy yace doctor explain more please I really don't get you" doctor ya cigaba da cewa sir wato yaron ka kace tunda yasamu wannan accident din bai farfad'o ba sai bayan wata goma koh?

Daddy yace yes yes doctor, akwai wani problem ne da wannan ?
Doctor yace No but problem din shine ya dade bai farka ba, sannan kuma daya farka har yau bai yi magana ba.
Daddy yace toh Doctor hakan matsala ne babba kenan? Doctor yace eh, da ace sanda ya farka yana magana toh da abin zaizo da sauki, kuma ayanzu bamu sani ba ko ya manta da komai na rayuwarsa ne, bamu sani ba ko kadan ya manta, Kuma bamu sani ba ko bai manta komai ba" amma nevertheless zamuyi bincike sosai for now" ku dai ku kasance cikin addu'a ako dayaushe inshaAllah zai warke"

Daddy yace toh Doctor mun gode sosai" doctor din yasa date na aikin, ya bada 2days" awannan lokacin Jiddah addu'a take yi babu kakkautawa kullin tana tare da mijinta kaman chewing gum ko kunyar Daddy da granny ma batayi abinta" wannan abin da takeyi shi ya kara sanya soyayyar ta acikin zuciyar Daddy da granny kuma suka amince lallai d'an su yayi sa'ar mata"

Bayan kwana biyu suka koma hospital din sannan doctor ya shirya dukkan abinda ake bukata, shi da colleagues dinsa su biyar suka shiga room din sai Hafiz a tsakiyarsu, Jiddah na cikin dakin doctor ya kalle ta yace Mrs. Please can you excuse us, yanzu zamu fara aikin"

Da kyar ta iya sakin hannun Yaya Hafiz ta fara tafiya ahankali tana waigowa tana kallon shi" shima kuma idanuwansa suna kanta amma baya cewa komai har ta fita bai daina kallon kofar ba"

After 2hours doctors din suka fito, suka sanar da Daddy cewa Nan da 24hours zai farka meaning sai gobe da yamma zai farka" su dai sunyi aiki kuma sun gama successfully sannan suna sa ran zai dawo da tunaninsa da komai nasa ma.

Jiddah ko suman tsaye tayi awajan ta kasa cewa komai ita kam dama zasu barta taje ta zauna dashi har sanda zai farka"
Ammi ce ta dawo da ita daga trance din data shiga tana cewa Jiddah muje gida ko tunda sai gobe zai farka"
" Wani irin kallo na bisu dashi, na dan ja da baya sannan nace Ammi gida kuma, shi Yaya wa zai zauna dashi toh ?

Granny tace doctor yace zamu iya zuwa gida sai mu dawo gobe" na girgiza kai nace a'a granny Ni zan tsaya ko da ban kwana dashi ba zan kwana a waje, Ammi bazan iya tafiya gida nabar Yayanah a hospital ba"

Har Ammi na shirin yimin tsawa Amma Daddy yace no Ammi rabu da ita kawai, beside ba laifi bane ai idan ta kwana" nayi murmushi hakanan suka tafi suka barni, na samu wani fancy chair na zauna Ni kadai ban jima ba na duba wrist watch dina naga karfe bakwai ta dan gota, tashi nayi nace na nemi ruwa nayi alwala na dawo wajan nayi sallah ban tashi daga wajan ba sai da aka kira isha'i na tashi nayi sannan na koma saman fancy chair na zauna Ina ta Addu'o'i araina sannan duk bayan minti goma sai na tashi na leka dakin sai naga yana nan kwance yanda aka barshi"
Ranar idona biyu babu bacci sai sallah danake tayi har asubahi tayi"

Washegari da safe su Daddy suka iso hospital sun taho min da abinci amma naki cin komai buri na bai wuce naga farkawar masoyi na ba" muka yini a asibiti babu mai cewa wani kala kasancewar duk hankalinmu atashe yake" karfe biyar da rabi nayi naji wani faduwar gaba mai karfi acikin zuciya ta" doctors da Daddy su suka shiga dakin wanda sunyi kusan awa ukku adakin suna yin wani experiment din" Ni dai aka barni da tagumi da faduwar gaba" muna zaune Daddy ya fito da sauran likitocin" fuskokinsu kawai na kalla na samu amsoshin tambayar danake son yi musu" babu fara'a babu walwala kenan Yayanah bai warke ba"
Ina cikin wannan tunanin doctor Daya ya dafa ni ya dawo dani daga trance din dana shiga yace Mrs. you can go in your husband wants to see you"

Wayyooo Allah na ai na rasa me zanyi alokacin, ban tsaya sauraron su ba na rike stick dina da kyau sannan na fara tafiya cikin sauri har na iso kofar dakin , ahankali nasa hannu na tura handle din kofar""""

❤️❤️❤️❤️❤️❤️❤️❤️❤️❤️❤️❤️
Too short kuyi hakuri dani🙏
Thank you for your support readers😘

Taku DIELAIBRAHIM ✍️ your comments really make me happy 😁 please don't forget to press the little star below.

Happy reading 🤗

RAYUWAR JIDDAH ✔Where stories live. Discover now