24

162 18 6
                                    

RAYUWAR JIDDAH
Part 2/4
Mallakin DielaIbrahim

GORON SALLAH📚ALKALAMIN DIELAIBRAHIM ✍️

____________________________________
Asibitin Algarkawi
Kinkinau GRA
9am

"Morning"
***"Karfe tara da yan mintuna dukkansu suka iso hospital din, Ummi ce ta fara shiga dakin ta samu su Momma a ciki, suna cikin gaisawa ne idanuwanta suka sauka kan Hafiz wanda yake rike da hannun Jiddah, fuskarshi na kallon fuskar Jiddah, ji yake inama ta farka yanzu, yana son hada ido da ita, sannan yai mata alkawarin inshallah babu mai rabasu sai mutuwa""""
" Ummi taji bugun zuciya, dama bata taba ganin Hafiz ba sai yau, MashaAllah ta nunfasa, aranta tace ba shakka wannan shine jinin Abubakar, Hakika babu abinda Hafiz ya bari na daga wajan Daddy, sai dai ya dara Daddy haske"Ummi ta kalli Momma da idanu take tambayarta me yazo yi, Amma Momma bata iya amsa mata ba har sauran suka shigo, suma dai sunyi mamakin ganin Hafiz zaune adakin amma banda Faisal shi dama yasan dole Hafiz zaizo hospital din after all dama shi ya kirashi awaya.

"Bayan sun gama gaishe gaishe da sauransu Hafiz ma ya gaishe su cikin girmamawa harda Abba,  Yana gama gaishe su ya kawar da kai izuwa Hauwa'un shi ya cigaba da aikin kallonta"

"Momma ta kirawo Abba da Ummi waje tabar sauran, suna fita waje Abba ya kasa hakuri yace Momma banace kar na sake Jin and ambaci sunan yaran nan ba, ballantana kuma har yazo hospital dinnan!
"Momma tace, kayi hakuri ka saurare ni, Abba yarannan suna son junansu, soyayyar su tafi karfin adakatar da ita da karfi,, jiya bayan tafiyan ku yazo, kuma agaskiya bazan iya hanashi ganin Jiddah ba shiyasa na barshi ya shiga, But,to my own surprised sai na ga ya jima bai fito ba har wuraren sha biyu, kodana leka na iske har bacci ya dauke shi, babu yadda banyi dashi ba akan ya koma gida, Amma yaki, hakanan na hakura na barshi ya kwana anan,.....Abba kamar yadda soyayyah take wahalar da Jiddah haka shima soyayyar take cin jikin shi and kada ku manta bafah su kadai bane, ga Halima da Muhammad,...Don Allah na rokeka Abba kabari yaran nan su auri juna, kada ka haramta masu abinda Allah bai haramta musu ba,.....ka cire wani dalilinka na Ummi tasan Daddy" kawai ka mikawa Allah lamarinka Abba, shi zai samo mana solution,.....Kuma ni base on my opinion naga for how long kuke tare da Ummi, kuna rufawa juna asiri, kowa yasan cewa Ummi taka ce, to mezaisa ka tada hankalinka Abba saboda kawai yaran nan suna son juna,.....Momma ta tsagaita ta dubi Ummi sannan tace, Naji jiya kina cewa Daddy shi ya hada yaran saboda soyayyar ku" haba Halima don't be selfish mana, Baki zauna da Jiddah kin fahimci damuwarta da rayuwarta ba kamar yadda ni na zauna da ita, Halima nasan komai akan rayuwar Jiddah saboda komai zai faru da ita sai ta fito ta fada min,......wallahi Daddy baisan komai akan soyayyar yarannan ba harta shi Muhammad din da Leemarh, Allah ne ya hada su,(anan Momma ta basu labarin yadda Hafiz da Hauwa'u suka hadu)"
"Abba yadanyi gyaran murya yace yanzu kina nufin kice Engr.Abubakar Yusuf baisan komai akan wannan al'amarin ba"
"Momma tace kwarai kuwa, sannan zanso ka amince ku hada zuri'a badan Halima da Abubakar sunsan juna ba, sai dan kyauta tawa, ko ba komai zaka tai maki rayuwar yaran, zaka basu wani farin ciki da har abada bazasu taba mantawa ba duka biyun.......ta tsagaita tana kallon Abba da Ummi.
"Ummi ma ta koma kallon Abba don ita Bata da abin cewa musamman ma saboda tasan da tayi magana za'a iya cewa tana bayan Daddy, ita kuma bata son bacin ran mijinta saboda ya zame mata haske arayuwarta.....
"Abba"yace sai nayi tunani tukunna, ku kara bani lokaci" yana kaiwa nan yabar asibitin ma gaba daya, ya tafi wajan abokan kasuwancin shi.

"Momma da Ummi suka koma ciki suka samu sauran yaran, dama Ammi suna gida, hakanan Ummi taji Hafiz ya kwanta mata arai duba da yadda yake ta nan nan da Jiddah duk da bata farka ba Amma yana nan makale da ita, hakan kuma bai hanashi yin hira sama sama da sauran samarin ba,....Ummi ta dan share guntun hawayenta ta, suka cigaba da hira da Momma, Fatima ko tana gefen su tayi shuru abinta Momma tace Faisal kakai Fatima gida tayi wanka taci abinci sai ku dawo Koh"
"Faisal yace toh Momma"ya dubi Fatima yace sai ki tashi muje ko gimbiya"
" Fatima ta harareshi playfully tana sake duba su Momma fatanta daya Allah yasa basu dago inda zancen shi ya dosa ba"
"Hakanan ta bi bayanshi, ahanya kuwa babu wanda ya tanka ma wani, har suka isa Rahmat close, unguwan rimi, tace ka shigo ciki sannan ta fita.
"Ba musu yabi bayanta, Kai tsaye falo ta bude mishi ya shiga sannan ta kunna masa A.C ta kunna T.V , ta dauko mashi ruwa da chi-exotic along with cup and tray ta aje masa, sannan ta shiga ciki.

RAYUWAR JIDDAH ✔Where stories live. Discover now