17

192 20 3
                                    

RAYUWAR JIDDAH
Part 1/17
Mallakin DielaIbrahim
Happy weekend fans

____________________________________
India-Mumbai
8pm

Bayan sun fito daga hospital din,suna tafiya ahankali Jiddah da Momma suna hira abinsu uwa da diyarta, Momma tana rike da hannun Jiddah tana mata jagora har suka iso wajan stair case. adai dai lokacin Hafiz ya shawo corner yana haurowa cikin sauri hannunsa dauke da phone yasanya a kunne alamar waya yakeyi, cikin ikon Allah sai aka samu cinkoso awajan, ta gefe yake tafiya but, suddenly wani Wanda ya fishi sauri ya ture shi ya wuce at that moment hannun Hafiz ya gogi hannun Jiddah na dama kasancewar Momma na rike da hannun hagu Kuma tana dayan side din.....Wani irin bugun zuciya taji mai karfi sakamakon shock din dataji ya shiga jikinta hade da wani iska wanda yake neman ya hure mata dan veil din data sanya cikin sauri ta fara waige waige gashi babu ido balle taga ko shine din da gaske,...haka zalika abinda ya faru da Hafiz kenan dasauri ya katse wayar da yakeyi ya dakata yana waigawa ko zai ganta don shi tabbas jikin shi ya bashi cewa Hauwa'u na kusa dashi moreover shock din dayaji, same shock ne babu abinda ya canja, Amma haka ya gama waige waige kasancewar duk fararan fata ne mata da maza keta faman safa da marwa, zan iya cewa ya hango wasu tsaye kaman hausawa amma baida tabbacin sune don haka ya karyata zucuyar shi yabar wajan dasauri don yasan Honey dinshi tana cen tana jiranshi.
"Jiddah ko bata so barin wajan ba Amma Momma tai ta faman mata fada akan ta kasa fitar da Wanda bai damu da ita ba acikin zuciya, ta kasa mantawa dashi, wannan wace iriyar soyayyah ce, haka tai ta faman mita, don dole suka bar asibitin tana bawa Momma hakuri don Allah yaji yagani Jiddah bata son mita, Amma fa idan itace zata iya yima kowa😜 suka iske Faisal da Muhammad a waje suka jera abinsu suna ta faman hira.
************
Aranar bayan sun koma gida Faisal da Muhammad na daki, Faisal yana kishingide a sofa ya kalli Muhammad yace my guy ka bani shawara mana kasancewar Muhammad age mate din Faisal ne Amma Faisal ya girme masa da wata biyu.
Muhammad yadan zare idanu yace bro tun da na ganka a hospital nayi observing kaman kana cikin damuwa meyake faruwa ne?
"Faisal ya dan gyara zaman sa yayi gyaran murya sannan ya shafa sajensa wanda yake kara masa kyau, yace Muhammad jiya kafin mu taho Abba da Ammi sun min wata maganar dayasa Jikina yayi sanyi sosai.!
Muhammad yace what, wace irin magana kenan Faisal?
Faisal yaja dogon numfashi sannan yace wato Muhammad hakika Ina son Jiddah tun tasowarta, ada banyadda da son ba, Amma ayanzu nagane Ina yimata so na hakika bana tunanin kowacce mace sai Jiddah, zuciyata ta kasa amincewa da wata in ba Jiddah ba, Amma daga baya na fara kokarin cusa mata soyayyah ta sai dai it turns out to be poor results saboda Jiddah kallon Dan uwa, Yaya kuma sometimes uba, take yimin, bata taba tunanin wata soyayyah a tsakaninmu ba, Muhammad yanzu haka maganar da nake maka ciwon idanun Jiddah saboda wani ta fada halin da take ciki!
Muhammad ya gyara zama hade da cewa what!
Yes" off course, Jiddah tana da wanda take mutuwar so don na karanaci Jiddah fiye da tunanin mai karatu, nasan in and out dinta, wanda kuma take so nasan shi but yanzu baya kaduna baya nigeria, nayi cigiyarsa saboda farin cikin Jiddah Amma har yanzu shuru....kwatsam saiga Ammi ta fito da wata magana, and due to that Jiddah loss her vision....I  thought after abinda ya faru baza akara yin maganar auran mu ba, Amma jiya kafin mu taho Ammi da Abba suka zaunar dani sukai min magana da ta kara wujijjiga ni, ta kuma kara dagula min lissafi yadan tsagaita yana kallon Muhammad.....
"Muhammad yace take heart bro, am listening'
Faisal yace Ammi tana nan akan bakanta aure na da Jiddah upon all what happened, Abba ya   tabbatar min da idan muka dawo za'a fara shirye shiryen auran mu.... Muhammad am speechless by hearing this from them, na shiga damuwa ne simply because of Jiddah, don Ina sonta kuma Ina fatan na aure ta amma that doesn't mean na kuntata ma rayuwarta, Muhammad ka bani shawara am in "dark reaction"(in muku na yan biochemist😎).
"Muhammad ya girgiza kai cikin nuna halin tausayawa yace idan na fahim ceka bro kana son Jiddah so na hakika amma akan abinda take so zaka iya sacrificing happiness dinka saboda ita"gaskiya kai din na daban ne Bro faisal, "yanzu shawaran dazan baka shine ka yawaita Addu'a ka dage sosai da sadaka, sannan bangaren Abba da Ammi kuwa ka barsu karka ce musu komai, likewise Jiddah ma kada ka fada mata komai,Muna komawa sai ka fada masu cewa kana da budurwa kuna daidaitawa ne!
Faisal ya zare ido yace Muhammad you most be crazy, Amma kasan ban taba yin girlfriend ba ko talkless of ma ace har maganar aure ya shigo a tsakanin mu, gaskiya acanja shawara I can't lie.....
"Muhammad yace to sai ka fada min inba karya kai musu ba wlhy bazasu barka ba sai sun tabbatar auran nan ya dauru, kuma ina daya daga cikin masu murna don farin cikin da zanyi ba kadan bane, Amma yanzu bana so nabi bayan su Ammi kaga kaman ban damu da kanwata ba, shiyasa na ke kokarin tsaya maka, ni nasan yadda zanyi dasu kaidai kawai ka amince da shawara na.
Faisal yace no wahala, na amince Allah yayi jagora"
Ameen" suka amsa sannan suka sauya hirar su.
*************
Hafiz Abubakar ya samu Honey dinsa a office din Dr.Rahul Jay. yana duba ta, after some minutes Dr. Rahul Jay ya cire glasses dinshi yace da Hafiz, eyes din granny dinka suna lafiya alamu sun nuna maganin da muke anfani dasu sun karbe ta, but yanzu tissue din idanun nata muke so mu gyara saboda kada watarana ya kawo mana matsala, ya cigaba da cewa" ku dawo ranar Thursday wannan week din sai muyi aikin Koh.
"Hafiz yace okay Dr. Thank you so much sai mun zo.
Sukayi masa sallama sannan suka bar hospital din.
Hafiz na zaune saman sallaya misalin 2pm na dare Yana mikawa Allah kukanshi akan Hauwa'u, shi jikinshi yana bashi cewa Hauwa'u Junaid tana kusa dashi amma dole sai da taimakon Allah zai samu ganinta,...bashi ya kwanta ba sai da yayi sallan asubahi 6:40 ya kwanta bayan ya tada granny shi kuma ya koma ya kwanta.

RAYUWAR JIDDAH ✔Where stories live. Discover now