AL'ADARMU

57 2 2
                                    

AL'ADARMU🏇
Page 02

Copyright©FADILA IBRAHIM

Al'ada ta kasance abu mafi banbantuwa a tsakanin yare daban daban da kabilu daban daban.

Zaria, Kaduna state
4:00pm

Tsugunne take gaban wutan murhu,an ɗaura tukunyar lamba goma sha biyar, sai dai wutan bata ci dalilin daya sa sai ta heta wutar da maficin kaba wanda aka kera shi da asalin kaba, tana yi tana hura wutan murhun da bakin ta....Da alama itacen ma ɗanyu ne don ko rabin kamawa ba suyi ba sai uban hayaki wanda tuni ya turnuke gidan ma gaba ɗaya.....cikin wannan yanayin ne wata macce wacce ta kai saba'in a duniya bakar fata ta fito sanye cikin shiga ta kamala shigar atampha....tayi matukar kama da matar bahaushe...irin wadan ɗa suka ci zamanin su tun kaka da kakanni.

"Haba Asma'u ki duba yadda ki ka turnuke mana gida da hayaki, ni wallahi bani son haka, ke kullu yaumin idan zakiyi girki bazaki nemo itace masu kyau ba sai ki nemo itacen da zaki ta cutan mu kina samu hawayen dole.....Tayi kwafa cen kuma ta cigaba da cewa,"Ni wallahi bani son irin wannan abu billahillazi haka kawai"

Ta karasa maganar tana neman waje saman tabarmarta wacce kullin take jikin bangon katangar gidan na su, tana mai tsirta yawu ɗabi'ar ta kenan.

Asma'u dattijuwar mace ce, tana ta damuwan ta har ta samu itacen suka kama da kyar ta taso ta nufi wajan randar ruwan su wan da yake manne cikin kasa ta ɗiba ta wanke fuskar ta sannan ta kwalkwali ruwan daga bisani ta koma gefen murhun ta zauna tana mai goge fuskar ta wacce tayi ja saboda hasken fatar da take dashi kaman na zabiya ida nuwan ta kuma sun sha hawaye har sun gode ma Allah...tana zaune saman kujera gefen murhun da take sanwa....sai a lokacin ta buɗe baki ta ce,"Inna kiyi hakuri yanayi ne na damuna yanzu itace ba a samun busassu"

Inna ta buga uban tsoki kafin ta cigaba da mulmula daddawar ta tana shanyasu saman buhu wanda ta shimfiɗe shi a inuwa jikin wata bishiya....tana cewa "Asma'u don rainin hankali irin naki na gama magana tun ɗazu sai yanzu kuke amsa min, ko dayake ba laifin ki bane...Allah sarki Yusuf, Ɗa na Yusuf ai wallahi da yana raye da ba zaki rinka min wannan iskan cin ba...sai kawai Inna ta fashe da kuka wai Asma'u ta mata rashin kunya....kuka wiwiwiwiiiiii tsofai tsofai da ita wai Asma'u take ma kuka.

Sanin halin Inna sarai kuma ba yau ta saba hakan ba, shiyasa ko gizau illah kawai ta waiga ta kalle ta, sannan ta bata hakuri ta ce,"

"Kiyi hakuri Inna wallahi ban yi hakan da nufin rashin kunya ba, kawai na kagu naga wutar ta kama ne.........

"Dallah rufe ma mutane baki, Farar mayya kawai, jiki duk haske sai kace zabiya"

Idan da sabo Asma'u ta saba da cin mutuncin da Inna take mata tun tsohon mijin ta na raye bata bar ta ba balle yanzu kuma da baya raye....wani abun ma sai taga kaman da gangan take yi, wani lokacin haka zasu zauna susha hira kamar ba Inna ba, wani lokacin kuma haka Innar zatayi ta mata masifa tana zazzaga mata buhun mita da masifa da komai ma, ko da kuwa babu abin da ra mata.....kwarai idan da sabo ta saba, don Inna ba ita kaɗai take ma haka ba, ko yau tayi bakuwa wallahi idan bakuwa bata mata ba a gaban bakuwar zata buɗe baki tace "kai nifa wagga bakuwa baki da kwarjini a waje na" ko kuma ta ce "Tir wagga bakuwa dai anyi asarar haihuwa ko farin jini baki da shi a wajan al'umma"

To tun tana yi tun ɗan ta na raye ko ace ma tun kuruciya, har ɗan ta ya kwanta dama tsahon shekara ashirin kenan da rasuwar sa, amma ba laifi Inna ta rike su amana ta zauna da su da daɗi ba daɗi tun suna tsohon gidan su har Innar da kanta tace su dawo kusa da ita su zauna tare......Ɗabi'ar INNA ce shiyasa nake muku Umma ta saba, kasancewar Inna ta san cewa Umma nada hakuri sosai shiyasa take zama da ita.

Karfe shidda dai dai ta kwashe tuwo suna nan a robobi ta ajiye a gaban murhun, yayin da sanwar miyar ta tana ta tafasa wanda gidan ya cika da kamshin daddawa da tafarnuwa....a daidai lokacin ya shigo gidan.

RAYUWAR JIDDAH ✔Where stories live. Discover now