36

170 14 4
                                    

RAYUWAR JIDDAH
Part 2/16
ALKALAMIN DIELAIBRAHIM ✍️

____________________________________

Ina tura handle din na tsaya Ina kallon gadon da aka kwantar dashi tun daga wajan naga yanda Yaya Hafiz ya tsura min kyawawan idanuwansa"kaman dai yadda na fita jiya na barshi" na karasa shiga dakin na jingina da bangon dakin acikin zuciya ta nace toh kenan Yayanah bai warke ba, shiyasa naga su Ammi suna magana kasa kasa" tunda gashi haryanzu idanu kawai yake bin kowa dashi , kasa karasawa nayi wajan na jingina da bango na rufe idanuwana at the same time kuma hawaye ke diga asaman kumatu na" Ina tambayar kaina yanzu yazanyi Yayanah yaki warkewa" banyi minti uku awajan ba naji ana share min hawaye na" da fari " I feel his sense of touch daga bisani na soma kokwanto acikin zuciya ta gashi Ina jin kamshin jikin shi akusa dani" amma na kasa bude idanu naga shin dagaske shi dinne" uhmmmm ban sake rud'ewa ba sai danaji muryar shi a kunne na yana cewa " Hauwa'u ba kiyi farin cikin gani na bane ?

Ya ilahi! ai bansan lokacin dana bude idanuwana ba da sauri na daura su a fuskar Yayanah" kuka, farin ciki da jin dadi sune suka ziyarce ni awannan lokaci kada kuso kuga yanda na rungume shi Ina hawaye da kyar na iya furta kalma uku nace "
"Sannu Yaya Hafiz"

Murmushi yayi shima ya rungumo ni sosai sannan yace Hauwa'u Allah ya amshi Addu'ar ki, kinga na samu lafiya, hakika nayi dacen samun mace kamarki Hauwa'u zo muje mu zauna muyi hiran yaushe gamo" ya kama hannuna da niyar mu koma kan gado" kawai sai yaga na fadi saboda ban rike stick dina ba na jinginar dashi a bangon dakin kasancewar doguwar riga na sanya kuma ba lallai bane ka gane bani da kafa daya"

Bayan na fad'i ne yace ohh shit am so sorry Hauwa'u nah ya daga ni na tashi sai yaga na janyo stick dina Ina dogarawa nayi tafiya har nakai wajan gadon na hau na zauna" da mamaki ya biyo ni, maimakon ya zauna noooo sai ya duka kasa ya soma daga min kasan doguwar riga yana son yaga abinda ya samu kafata" Hafiz was very shocked ganin an yanke min kafa daya, ya kalle ni da sauri yace Hauwa'u don't tell me that is because of what happened that day?
Ahankali na daga masa kai ina kallon shi naga hawaye na zuba a idanuwansa, adai dai lokacin su granny suka shigo dukkansu" Hafiz ya tashi da sauri ya tari Daddy yace Daddy am responsible for everything that happened to us on that very day" gashi har Hauwa'u ta rasa kafarta daya just because of me" Dadday me yasa baku sa an kama wa' inda sukaiwa Hauwa'u wannan abun ba, and Daddy kawai sai aka yanke mata kafa maimakon a gyara mata" a rud'e yake maganganun nan"

Daddy yace calm down my son" anan ya bashi labarin duk yadda abin ya kasance" Hafiz ya bata shuru yana kallo na yace Hauwa'u you get injured all because of me" komai zai same ki ta dalilina yake samunki, I blame my self Hauwa'u seriously am not good for you "Jiddah"

Nayi saurin kallon shi da idanuwana da sukai jazir jin ya kira sunan da baitaba kira ba wai Jiddah" na tashi da kyar na karasa inda yake nace Yaya nah baka taba kiran "Jiddah" ba sai yau" Yayanah I will never blame you for such a thing" I value your life more than mine Yaya Hafiz"""" Yayanah we are meant to be together, we are meant for each other" idan babu daya, daya bazai iya rayuwa ba" Yayanah komai dayake faruwa dani daga Allah ne amma kuma dama duk abinda zai faru da bawa toh akwai sanadi, Yaya Hafiz ban taba jin na tsane ka saboda abinda ya faru dani ba, asalima ni awajena wannan abin farin ciki ne agare ni saboda naje taimakon masoyi nah, Mijinah kuma Yayanah" hakan ya faru dani, da na barka kai kadai fah, da yanzu bansan iya abinda zasuyi maka ba, Yaya Hafiz I repeat you are my life" aduk lokacin dana kalle ka na kuma tuna farkon haduwar mu, Ina jin wani sanyi araina Yaya nah" you are like an angel to me, you are a blessing given to me from Allah" Yaya Hafiz" I can't afford to see you in pain, and I can't afford to see someone blaming you for this, So" da ba kai ka fadi wannan maganar ba da yanzu kaga yadda zanyi da wanda ya fade ta" amma saboda matsayin dakake dashi a zuciyata shiyasa zan hakura, amma please kar ka sake fadin irin wannan maganar Yayanah" Rashin kafata daya dama Allah ya kaddara haka zai faru dani, komai mukaddari ne kaji Yaya nah" Hmmm Hafiz can't stand it ya rungume ni yana hawaye hade da min kiss a forehead dina sannan yace Daddy za'ai wa Hauwa'u aikin kafa, dole za'a sanya mata kafar robar"
" Granny tace MashaAllah ta kalli Daddy tace Abubakar me na fada maka, ai dama na fada muku tun watannin baya nace idan Hafiz ya warke to sai yasan yadda yayi ya gyara kafar takwara" Ammi tace koni rai na ya bani hakan zai faru wallahi gaskiya yaran nan soyayyar ku ta gaskiya ce Allah dai ya barku tare amma kunsha wahala sosai, Allah yasa karshen wahalar taku kenan"

RAYUWAR JIDDAH ✔Where stories live. Discover now