25

174 24 6
                                    

RAYUWAR JIDDAH
Part 2/5
Mallakin DielaIbrahim

GORON SALLAH 📚 ALKALAMIN DIELAIBRAHIM ✍️

who's ready for our very own HAUWA'U JIDDAH JUNAID 😁
follow me and see for your self 😂😂😂

____________________________________
Asibitin Algarkawi
Kinkinau GRA
6:30pm

"Ammi tace, dafari ina so naja hankulan kowannenku, Shakka babu rayuwa ko ince duniya cike take da darasi da abin mamaki,"
" You met people in different places,shiyasa ake so mutum ya kyautata zamantakewar shi da mutane, saboda gudun bacin rana, irin ta yau" Lallai nayi nadamar maganganun dana fadawa Abubakar shekarun baya, ban taba tunanin abu makamancin haka zai faru da zuri'a ta ba, sai gashi yau abun ya dawo kaina, kan jikata wacce na fiso duk cikin jikokina, kuma sha lele a idanun kowa a family (Hauwa'u Jiddah) Ina masifar son Hauwa'u saboda sunan Aminiyata taci, wanda ni na zabi sunan kuma ya bita, dafari naki yadda Jiddah ta koma Kaduna, Amma dayake RAYUWAR JIDDAH acen yake so sai Allah ya sanyamin hakuri a zuciyata na kuma fadawa Ummi da su dauketa su kaita kaduna, inshallahu babu abinda zai faru sai Alkairi" Toh Alhamdulillah zamuce tunda bawai wani mummunan abu ya faru bane"....
"Ammi tayi shuru nadan lokaci kadan kafin ta cigaba da cewa,
Hakika yau naji dadin haduwan da akayi anan, dama ko su Abubakar basu zo ba, na yanke shawaran zamuje har gida mu sameshi, saboda agyara matsalan tun kafin abu yayi nisa, to which ina sa ran yazama silan hadin kanmu gaba daya....ta dan tsagaita sannan ta ci gaba, da cewa, Abubakar Ina mai baka hakurin abinda Abba yai maku, wanda ba da sanina ya aikata komai ba, shine uban Muhammad da Hauwa'u nasan yana da damar dakatar da auran nan, Amma dukda haka da ina wajan,taron bazai watse hakannan ba" Shiyasa kwana biyu nai shuru ban sanya baki acikin damuwar taku ba,har sai da na gama yanke shawarar daya kamata..Shakka babu shekarun baya nasan nice silan rabuwarku da Halima, shiyasa wannan karan danaga abin yazo haka, na zauna na yanke shawara wacce nake ganin itace hanya mafi sauki da zamu bi, asamu abinda ake so.
"Abba ya bude baki zaiyi magana tuni Ammi ta dakatar dashi da hannu"
"Baiso hakan ba Amma babu yadda zaiyi, dole yai shuru yasanya wa zuciyarshi salama."

"" Faisal ne ya dan katse Ammi da cewa, Matar don Allah kafin ki  yanke wani hukunci muna so muji labarin soyayyar "Ummi da Daddy"sai yaga kowa na kallonshi all eyes on him,barin ma Abba Wanda ya cika yayi fam,😂Faisal ya shafa sumar keyar shi ya juya ta dayan side din inda Abba baya ganinsa yace Uhmm calm down please, yace kuyi hakuri don Allah mu yara yara da bamu san komai ba bamusan abinda ya faru shekarun baya ba, shine muke son adan fada mana sai yayi shuru ya dan ja rigar Saifullah yana kanne masa ido daya, akan suyi supporting dinshi, aikuwa tuni Saif ya soma cewa eh mana ehmana, Don Allah Ummi abamu labari" yasanya hannunshi biyu alamar roko,...Momma dake kusa da Saifullah ta rankwashe shi a kai tana hararar shi, Granny kuma tana kusa da Faisal hakan yasa ta kama kunnen shi ta murda playfully tana cewa, wannan yaron baka da kunya wollah...Faisal yadan yi kara kadan yana cewa to granny wayyo Allah Momma kibaiwa granny hakuri please, zata cirewa Autanki kunne"
" Momma tace wa, ai ni Auta daya nake dashi, kuma Jiddah ce" sai dai ko idan ka kawo matar aure sai na dan saku a sahun Autancin"
"Faisal ya dan zare ido, yace Haba Momma, Haba Momma na"

"Granny ta kwabe masa baki tace yimin  shuru, wannan labarin is story for another day" so ba yanzu ba kana jina" ta kara jan kunnen"
"Da sauri yayi kara yana neman hanyar guduwa"
"Dariya sukai tayi, daga karshe sukayi shuru suna jiran suji ta bakin Ammi(boss)😎.
Suna ahaka ne, Hafiz dayake rike da hannun Jiddah yaji tayi motsi, sai ya sake saurarawa yaji ko dagaske itace tayi motsi, lol😁.
"Aikuwa sai ya hango ta tana yamutsa fuska kaman wacce tasha magani mai daci daci, ai baisan lokacin daya furta Alhamdulillah with so much excitement on his face wanda yasa duk halittan dake dakin kallon Hafiz" to which shi kuma alokacin ya fara fadin "call the doctor please,hurry up she is awake"
"Haka kowa yazo ya zagaye gadon nata, dukkansu masoyanta ne,"Jiddah kam sai kallon su takeyi daya bayan daya, yadda kasan bata gane su ba,har ta sauke idanuwanta akan Hafiz Abubakar, wanda har lokacin hannunshi na rike da nata hannun"
"Sai ta saki murmushi wanda dimple dinta ne kawai ya nuna, ko hakwaranta basuyi showing ba, ta kai dubanta ga Momma da Ummi, ta sakar masu murmushi mai kayatarwa wanda yasoma basu mamaki, suna tunanin anya lafiya lau take" daga bisani ta sauke idanuwanta akan Abba wanda lokaci daya annurin fuskarta ya dauke, ta soma recalling dukkan abinda ya faru , sai kawai ta kauda kanta gefe wanda kana iya hango guntun hawayen dake sauka a kasan eyes dinta"
" Zuwa wannan lokacin sun fara tunanin ko wani abu ne ya samu Jiddah, saboda sunyi magana har sun gaji Amma shuru bata amsa suba, har sai da doctor ya shigo ward din, yace duk su fita zai dubata, da kyar aka banbare hannun ta cikin na Hafiz, ita ala dole bata so ya bar side dinta"
" Duk suna waje sunyi cirko cirko, suna jiran likita, aikuwa sai gashi ya fito,  sukai mashi cha,suna son jin feedback"
Doctor yace ku kwantar da hankalinku, Hauwa'u Junaid ta na lafiya, yace yayi gwaje gwajen shi ya gano komai nata yaga yana tafiya normal saidai heartbeat dinta ne yake beating fast ba yadda yadda kamata ba,  amma da zaran ya daura ta akan drugs, zata samu sauki da yardar Allah"

"Ummi ta sauke nannauyar ajiyar zuciya tace, Alhamdulillah toh yanzu zamu iya ganin ta?

"Yeah ku shiga amma, ba dukkan kuba saboda kada hayaniya yai mata yawa"suka amsa da toh"

"Momma ,Abba,Ummi and Ammi ne suka fara shiga ba laifi ta sake dasu amma ba kamar yadda ta saba yi da kowannensu ba, su kansu suna mamakin silence din Jiddah, haka suka gama zaman su suka fita sannan samarin suka shigo suma ba laifi tama fi answering dinsu akan su Momma, sukai ta faman tsokanarta kuwa sannan suka fita.
"sa'annan Fatima da Leemarh suka shigo, sannan sai Daddy, Mom da Hafiz wanda daga karshe aka bar Hafiz a dakin, Yana zaune saman kujerar da take manne da gadon yana kallon ta kaman me tsoron kada ya rasa Hauwa'u,
"Jiddah ta dauko wani pillow ta jefa masa, tana cewa "Yaya Hafiz for God sake kadawo normal person, look at me am alive fah, bawai na mutu bane🤨
"Hafiz ya Sanya hannunshi cikin suman kanshi ya yamutsa sannan ya rufe idanu ya sake budewa, sannan yace Alhamdulillah ashe dai ba mafarki nakeyi ba"But, it's your fault Jiddah kece kinkiyin magana tun dazu, kin sakewa dakowa"
"Jiddah ko ta kalle shi da mamaki , sai kuma suka fashe da dariya lokaci daya gwanin ban sha'awa"Hafiz ya kamo hannunta ya sanya cikin nashi" amma sai yaji Jiddah tace Aa Yaya Hafiz babu kyaufa rike hannun Non- Muharram"
"Hafiz yace yeah I know, but akwai abinda nake so nayi feeling ne, Yana fadan haka sai ya lumshe idanuwansa "
" Jiddah kamar me rada tace "wani feeling Mi Alma?"
"Batareda ya bude ido ba ya bata amsa yace"
"The Shock"
Jiddah ta zare ido 😲😲😲, tace kaima kana ji Mi Alma?

Da sauri ya bude ido, ya sauke su a fuskar Jiddah, ya dade yana kallonta, kafin yace: Kema kina jine?

"Jiddah ta gyada kai tana wasa da igiyar rigar ta"
"Hafiz can't control it sai da yayi kissing hannun Jiddah sannan ya sake hannun yadan ja kujerar baya kadan ya mike kafa, ya kishingida, sannan ya lumshe idanu kaman mai Jin bacci ahankali yace Hauwa'u and Hafiz are meant to be together forever"

"Itama kuma kallon shi takeyi, ta dan juya kwanciyar ta, hawaye ne suka dan diga a idanuwanta, tana tuna Momma ta fada mata Hafiz tunda yazo baije gida ba, baici abinci ba"

" Jiddah tace Yaya Hafiz Momma tace tunda kazo baka koma gida ba anan kake kwana, why not ka tafi yanzu kaje kayi bacci ka huta sannan ka dawo."
"Hafiz yayi murmushi still idanuwan sa na a rufe yace "lahh"sai naga kinji sauki kafin zan wuce, don't bother your self kinji" Yana kaiwa nan yayi shuru baccin da baiyi bane na kwana biyu shine ya dauke shi, itama Jiddah baccin tayi.

"Momma ta leko ta iske duk sunyi bacci abinsu, tayi murmushi tace ohhh yaran zamani, wai su nan soyayyar su suke aikatawa ko kunyar mutane basa ji....Allah dai ya bar ku tare "Hauwa'un Hafiz"
"Ummi wacce ke gefenta ta amsa da Allahumma Amiin"
Sukayi murmushi sannan suka bar dakin.

*****************
guys how far now please take this mike 🎤 oyaaahhhh  one ward for any character that you love in this story bikoooo ooooo😁

"Kuma dai"
Nikam har yanzu banga masoyan "Faisal da Fatima ba
Kuma wallahi amana fah bata ce haka ba😁shin ko su soyayyar tasu bata birge ku ne😂
You guys should please do say something koh one word ne ma Allah I will be happy 😘"

Happy reading

Vote
Comment
Please

RAYUWAR JIDDAH ✔Where stories live. Discover now