31

142 12 0
                                    

RAYUWAR JIDDAH
Part 2/11
MALLAKIN DIELAIBRAHIM ✍️

____________________________________

Yaya nah ne!
Yaya Hafiz ne!!
Da sauri na fito daga b'uyan danayi na nufi wajan cikin kid'ima da tashin hankali, zuciyata na bugawa, sand'a na rink'ayi bayan na samu wani katon dutsi har na isa wajan da Allah ya bani sa'a kuwa katon cikin su na buga mawa nan take kanshi ya fashe ya kwanta yana nishin azaba"
Sannan sauran sukayo kaina wai zasu kamani amma nai saurin daukar wani dutsin babba na nuna musu nace idan suka kuskura suka zo inda nake sai na buga musu" aikuwa suka rabu dani kasancewar ogansu yace su kyaleni" nikam cikin jin dadi na nufi inda Yaya Hafiz yake na rungume shi sannan nai mishi kiss a forehead dinsa Ina hawaye, na soma kunce shi, Ina cewa am here for you Yayanah, insha Allah babu abinda zai same ka" Ina gamawa na kama shi muka soma tafiya Ina yi Ina hararar su daya bayan daya har muka danyi nisa" abinda ban sani ba ashe trap suka hada mana, wanda kafin ma muyi nisa da wajan, muka ga wasu mutanen sun kuma zagaye mu da bindiga da wukake manya a hannunsu"

Awannan lokacin basirar tawa ta kare na rasa abinyi ga Yaya Hafiz a kafada na jikin nashi babu kwari ashe sun mishi allurar kashe karfin jiki"😢 dukkan abinda ke faruwa yana gani amma baya iya magana"  na Sanya hannaye na na rike nasa hannayen da karfi, kuka ne yaci karfi na alokacin tausayin halin da muka shiga nake, sai alokacin na tuna Yaya Faisal gashi babu wayar dazanyi kiransa,  na soma rokon su dasu barmu muje gida, nai ta magiya ina kara jaddada masu cewa yau aka daura mana aure kuma ana cen gida ana jiran mu" amma dayake mugaye ne sai suka sa dariya suna cewa
" Lahh ashe Ango da Amarya ne, Daya daga cikin su wanda ya fara magana, da alama shine boss "  yace na dade ina jiran wannan rana" na dade Ina burin daukar fansa akanka" yau gashi Allah ya cika min buri na" ya kalli Hafiz yace kai yanzu har ka isa ka auri wannan kyakkyawar yarinyar HAFIZ, kuma kace zaka zauna lafiya?  Hahhhhhh toh wlhy tunda ka sa aka kama mahaifina, kuma kasan shine farin cikin rayuwata" amma kasa aka kashe shi Ina ji Ina gani" toh bari kaji in fada maka yau zan rama abinda kamin"yau zan dauki fansa akan ka, abinda zan maka sai ka gwammaci mutuwar ka dashi wallahi"

Aikuwa na saki kuka mai karfi Ina Addu'o'i, sosai hankali na ya kara tashi na waiga ko zan hangi mutane kadan amma bana iya ganin komai" hade hannayena biyu nayi ina rokon su dasuyi hakuri don Allah amma mutanen nan suka karaso inda nake suka raba ni da Yayanah sannan suka kwantar dani awajan wai zasuyi min "fyade" kuka nafarayi Ina kiran sunan Yaya Hafiz"har sun fara rabani da kayan Jikina sai naji Hafiz dina yana magana ahankali kamar wanda yasha kayan maye" yana rokonsu akan suyi hakuri karsu min komai shi suyi masa duk abinda suke so Amma don Allah karsu keta min haddi"

Sai mutumin ya sake fashewa da wata muguwar dariya sannan yace zan kyaleta amma wannan bashi zaisa na ki yimata wani abu ba" yace da mutanen shi " Guys let go of her" ko dasuka sake ni dasauri na gudu wajan Yaya Hafiz  ya hada fuskokin mu, muna jin numfashin juna Yaya Hafiz yace *Hauwa'u* Da gaske an daura mana aure?
"Dukda acikin tashin hankali na ke amma bansan lokacin da wasu hawayen farin cikin suka fara zuba a idanuwana ba Yayanah yana share min yana cewa Uhmm Uhmm stop crying please answer me Hauwa'u!!!!

Gyada mashi kai na yi Ina cewa yes yes yes Yaya Hafiz an daura mana aure!! Ya sake ni sannan ya fuskanci alkibla yai wa Allah godiya sannan ya juyo gareni yai min rungumar da bai taba yimin ba😢"

*Jiddah ta tsagaita da labarin saboda kuka ne yaci karfinta, sai da na rarrashe ta da kyar na samu tayi shuru,sannan ta cigaba daga inda ta tsaya "

❤️❤️❤️❤️❤️❤️❤️❤️
Fans kar kuyi kuka fah, dukdama ni na dan taba nawa kukan😢 na matukar tausaya musu wollah😣

ALKALAMIN DIELAIBRAHIM ✍️
VOTE
COMMENT PLEASE

RAYUWAR JIDDAH ✔Where stories live. Discover now