30

154 12 0
                                    

RAYUWAR JIDDAH
Part 2/10
ALKALAMIN DIELAIBRAHIM ✍️

__________________________________

Yaya faisal ya tsagaita sannan ya sanya hannayenshi ya share min  hawayen dake zuba a fuskata hade da girgiza kai ya na cewa a'a my little girl banda kuka addu'a zaki yi masa kinji " dukdama kirjinshi dukan uku uku yake saboda baisan wani hali zan shigaba"sai yaji ina fadin"
cikin zuciyata nace Alhamdulillah  ina godema Allah dayasa aka d'aura aurena da Yaya Hafiz dukda baya nan, Lallai yau ranar farin ciki ce agareni ba ranar bakin ciki ba"  afili kuma nace"
Inna lillahi wa'inna illaihir raji'un 😣 Ya Allah ka tsare min mijina aduk inda yake" Allah kasa ya dawo gida lafiya" wannan itace Addu'ar danaita maimaitawa alokacin, yayinda duk mutanen dake cikin falon sai da suka tausaya min ganin irin karfin halin shanye damuwata sannan na ce dasu Ummi da suje a cigaba da shagalin biki insha Allahu yayanah zai dawo gida lafiya na kuma nuna mata a fuska na cire damuwa" hakan yasa suka dan saki jikin su sannan suka fita suka barni ni kadai adakin, ga kuma makullin motar Yaya Faisal dayace na rike masa zaije cikin gida ya dauko iPad dinsa" na amsa nace masa toh"

Ina nan zaune naji text ya shigo wayata ban kai ga dubawa ba, call ya shigo Ina dubawa naga Hafiz ne, nayi saurin dagawa Ina cewa " Hello,Hello Yaya Hafiz Ina kake muna ta jiranka" mai makon naji muryarsa A'a sai naji wani murya daban yana cewa " Baiwar Allah ba shiba ne, idan ke yar uwar sace kitaimaka kizo mando hanyar airport kizo kiga halin da dan uwan ki yake ciki"

Hankali na tashe na kashe wayar ina maimaita sunan Yaya Hafiz abaki batareda da sanin inda hankali na yake ba na aje wayata nayi hanyar waje tunawa nayi car keys din Yaya Faisal na hannu na hakan yasa na nufi motar sa da gudu, ganin na dama na iya driving wanda Yaya Faisal ne ya koyamin mota amma baya barina Ina driving da kaina, hakan yasa na shiga na kunna motar , inajin wasu na min magana amma nakasa tsayawa na saurare su, da sauri nabar layin na nufi express inda naita faman gudu akan titi in banda Allah ya tsare ni alokacin da accident din dazanyi awajan ba karami bane" cikin ikon Allah kuwa Ina cikin tafiya na hango motar Yayanah mijina, nayi kokarin yin parking a gefen titi sannan na fito cikin sauri na karasa wajan motar na bude amma wayam babu kowa hakan yasa na sake kokarin crossing road din da nufin na dauki wayata na kirawo number Yaya Hafiz amma waya tace daukar ni inda kika ganni, sai alokacin na tuna na bar wayar a gida, na fara waige waige ko zanga alamar yayanah amma babu bana ganin kowa.

Ina tsaye a wajan tsahon minti talatin kafin na koma wajan motar Yaya Hafiz ina wani tunani, na kulle idanuwana sannan na natsu waje guda" alokacin naji Jikina yabani Yaya nah yana kusa dani" amma where can I find him? Na bud'e idanuwana ina kallon kasa, Allah mai iko na ga sawun takalma tawajan driver seat wanda aka taka da tab'o ya mike a cikin dajin dake gefen hanya, batareda wani tunani ba na fara bin sawun takalman dana gani dukdama bani da tabbacin ko sawun takalman sune, nidai na shiga cikin daji har na luluka cikin dajin batareda sanin me nakeyi ba"Hankali na bai dawo Jikina ba sai da naji karar bindiga, a tsorace na tsaya cak hade da dago kaina Ina kallon wajan, baki na na rufe Ina zare idanu Ina kuma mamakin yaushe na shigo wajan nan na waiga naga nayi nisa da titi sosai, ban kai ga komawa ba na sake jin karar bingiga, aikuwa na sake rudewa, na kama jikina waje daya Ina kyarma na tuno lokacin dana ji karar bindiga a gidan Momma  sanda aka kashe Abban Faisal, take wani tsoron ya ziyarci zuciyata lokaci daya Jikina ya dau rawa" Ina nan tsaye na soma jin hayaniya sama sama" zuciyata ta fara jana akan na leka cikin dajin naga meke faruwa" tun ina kwabar zuciyar tawa har bansan lokacin dana kutsa kai na bi inda najiyo hayaniya ba anan na hangi wasu mutane su shidda sanye da bakaken kaya sun rufe fuskokin su day mask baka iya ganin komai ajikin su" hannayensu kuma na dauke da guns and knifes sun zagaye wata bishiya wacce Ina iya hango shatin rigar mutumin da suka daure a jikin bishiyar" Ina nan tsaye Ina ta faman son naga mutumin da suke tsorata wa, da bindiga tunda da alama babu abinda sukai masa, gashidai mutumin sanye yake da farar shadda sabuwa dal kafafuwansa na sanye cikin bakin takalmi cover masu kyau hannunsa mai dauke da links masu tsada da wrists watch mai matukar tsada suna daure a bayan bishiyar sai dai bana iya ganin fuskarsa sakamakon wani katon cikin su daya rufe shi"

" Sai nayi sa'a kuwa katon mutumin ya matsa " Inna lillahi wa'inna illaihir raji'un " Ya ilahi shin kunsan me idanuwana suka gani ?

❤️❤️❤️❤️❤️❤️❤️❤️❤️❤️❤️❤️

ALKALAMIN DIELAIBRAHIM ✍️
VOTE
COMMENT PLEASE

RAYUWAR JIDDAH ✔Where stories live. Discover now