33

141 13 15
                                    

RAYUWAR JIDDAH
Part 2/13
ALKALAMIN DIELAIBRAHIM ✍️

____________________________________
💔💔💔💔💔💔💔💔💔💔💔💔
HAUWA & HAFIZ "HAUFIZ"😁
💔💔💔💔💔💔💔💔💔💔💔💔

*******
Muna ta tafiya ta cikin asibitin, kasancewar NAFHospital ne wanda yake da bangare daban daban ga girma ba laifi" na kosa naga mun fita waje, duk a tunani na a gida zamu naga Yayanah, kuma Mijinah" hakan yasa naita yin sauri, har Momma nacewa haba Jiddah easy easy don't injured your self" da fara'a a fuska ta nace Momma" na kosa na ga Yayanah ne pha kuma naga ke ba kya sauri ne🙃

Momma ta kama baki tana cewa lahhhhhh kuji mun yarinya pha baki da lafiya ana lallaba ki amma ke bai dame ki ba, burin ki kawai ke Jiddah kiga Yaya Hafiz" toh ki kwantar da hankalinki indai yaya hafiz ne kin kusan ganinsa, amma abinda nake so dake duk abinda zaki gani toh kada ki razana kada kuma ki dagawa kanki hankali kinga kema ba lafiyar gareki ba"

Na tsuke fuska nace ahhhh momma Ina ce shi Yaya Hafiz lafiyan shi kalau? Kafin ta amsa min,na kuma cewa Ina ce shi Yaya Hafiz din yana gida ba". Momma tai murmushin da yafi kuka ciwo tace Jiddah kiyi shuru don Allah" hakan yasa na maida kallo na ga hanya ganin babu wanda ma yake kallo na acikin su, cikin zuciya ta nace Uhmm ai nagane baku so naga Yaya nah ne 🙃 kuma InshaAllah sai na ganshi yau dinnan" maimakon muyi parking lodge sai naga mun bi wani hanya muna zuwa kofar da zamu shiga ward din"
Ina ta mamakin me zai kawo mu wannan ward din, muda zamu gida Kuma, na tura baki Ina cewa may be sako su Ammi zasu amsa ko zasu bayar" na gyara rukon danaiwa stick dina dukdama ban damu na tambayi kowa akan hakan ba, muka cigaba da tafiya har sai da muka iso male ward da alama mutun daya ne aciki" sai naja na tsaya Ina son naga me za'ayi awannan ward din, to tell you something I have a feeling that Hafiz yana kusa dani awannan lokacin" na ji kamshin turarenshi amma na kasa gane ta Ina kamshin nasa yake zuwa" Ina wannan tunanin kuwa naga kowa ya tsaya hade da juyowa suna kallo na" zare manyan idanuwana nayi nima Ina kallon su one after the other Ina mamakin irin kallon da suke jifa na dashi wanda yake daidai da kallon tuhuma ko wani abu daban" nikam na kasa gane nufin su" da kyar na bude baki nace Ammi, Abba, Ummi and the rest why this look all if the sudden?

Ammi tace Jiddah Ina kince kina son ganin mijinki Hafiz?
Da sauri na gyada mata kai, Ina cewa eh eh eh!!!! Eh Ammi Ina yake?
Ammi ta girgiza kai fuskar ta yana nuna alamar tausayawa sannan ta nuna min kofar dakin da muka tsaya, tace ki shiga yana ciki" Wallahi bansan lokacin da murmushi ya subuce min ba nama manta da cewa kafa daya gare ni wanda garin sauri in shiga ward din na turgud'e kafar na fadi"
Yaya Faisal ne yayi saurin taimaka min na tashi, yana cewa haba Jiddah kibi a hankali mana" ni kam ko a Jikina na amshi stick din na nufi kofar Ina murmushi Ina cewa toh big bros" "babu wanda ya kulani acikin su saboda dukkansu na lura duk basa dariya tun bayan fitowar mu daga ward din danake" na tura baki gaba acikin raina Ina cewa ku kuka jiyo, nikam nayi wajan masiyina, mijinah"(
Jiddah ce fah har yanzu dai halin yana nan, dukda cewa ta canja a fuska da jiki amma halin yana nan😅) ahankali na murd'a handle din kofar ta bude sannan na shiga na kuma maida kofar na rufe Ina kallon dakin" babu komai a dakin sai fridge, da gadon marasa lafiya guda daya, wanda naga mutum kwance saman gadon an dadd'aure kanshi da bandage" sai alokacin naji ashe mutumin ne yasanya turaren Yayanah", naja da baya Ina cewa ehhhhh toh ni kam Yaya Hafiz nake son gani, kuma babu kowa a dakin sai wannan marar lafiyar uhmm bari dai na koma na kara tuna musu nifah Yaya Hafiz nace, na fada ina kokarin fita daga cikin dakin" sai gefen ido na ya hango min dogon hancin Yaya Hafiz, komawa nayi da baya Ina sake kallon fuskar da kyau Ina cewa kai wannan ya kaman Yayanah ne" na sake dukawa da kyau Ina kallon kyakkyawar fuskar sai naji wani bugun zuciya mai karfi bansan lokacin dana kusan fad'iwa awajan ba, da taimakon karfen gadon na tsaya Ina maida numfashi Ina mai sake kallon Yayanah!!!! Kwantawa nayi a jikin shi Ina jijjiga shi nace Yaya Hafiz me ya same ka, ka tashi Yayanah Hauwa'un kace"

💔💔💔💔💔💔💔💔💔💔💔💔
Allah sarki Hauwa'unHafiz (HAUFIZ)

To me kuma ya samu Hafiz din ohhooooooo🤔

Taku DIELAIBRAHIM ✍️
VOTE
COMMENT PLEASE

RAYUWAR JIDDAH ✔Where stories live. Discover now