22

214 21 6
                                    

RAYUWAR JIDDAH
Part 2/2
Mallakin DielaIbrahim

__________________________________
__
"On that very sunday"
*Daddy da Hafiz sukayi joining Mom a parlor dasu granny, zama sukayi suna ta hira cikin wasa da dariya har granny ke sanar da Daddy wai tayima lema miji"Daddy yace ahahhh Masha Allah ashe autana ta kusa zama Amarya itama
Leemarh ko tayi saurin rufe fuskarta tana kara shigewa jikin Mom, Hafiz yace Daddy ai brother din inlaw dinka shine sirikin namu,
"Daddy bai dauko zancen dakyau ba yace Come again son"
"Hafiz yace matar da zan aura to yayanta shi ke son Leemarh, shima jira yake ta gama NYSC ya turo ayi maganar aure, granny ta kara da cewa kuma mutumin kirki kuwa, sai ma ka ganshi wlhy"
"Daddy Koh baki yaki rufuwa tsabar murna, Autanshi ta samu miji dukdama baiyi binciki ba, Amma dagajin yadda su hafiz suke magana yasan yaran yayi 💯"gyaran murya yayi yace auta wai haka, to gaskiya hadawa za'ayi dana Hafiz Koh"

"Leemarh ta rufe fuska ta tashi ta ruga daki tana abin autanci, Mom na dariya tana cewa mara kunya da atsakanin mu nee da yanzu kin ishe ni da labarin shi.....kowa dariya yake tayi sannan suka canja hira, suna haka ne wayar Hafiz yasoma ringing yana dubawa screen din wayar, bakowa bace illah Hauwa'u Jiddah Junaid" His Final Choice"
Murmushi yayi ya dau wayar ya tashi ya fita, Mom ce kadai ta lura da yanayin shi,ta dago mai Kiran nashi.

"Dakinshi ya tafi, ya kirata back,bugu daya ta dauka......ya bude baki kenan zaiyi magana sai yaji siririyar muryar ta mai ratsa jijiyoyin jikin shi😘 ""Yaya Hafiz kazo yanzu please"" sai kuma ta kashe wayar, da sauri yasake dialing contact dinta amma har yayi tsinke Bata daga ba, ya kira yakai so biyar no answer.
Hakan yasa ya tashi ya shirya, cikin wani suit material maroon da wando milk color yasanya wrists watch ya gyara suman kanshi sannan ya dau car keys da phone dinshi, da sauri ya Isa parking lodge ya nufi daya daga cikin motocin shi, nan da nan escort dinsa suka biyo shi suna shirin shiga motar gabanshi, saurin daga masu hannu yayi fuskar nan babu annuri ko kadan, yace no need ba nisa zanyi ba yanzu zan dawo, sanin halinshi baya son naçi sai kawai sukayi yanda yace.

"Minti 30 talatin yayi kafin ya isa gidan su Jiddah, yayi horn, gate man ya bude ya shiga, yayi parking sannan ya fita, bai tsaya kiran layinta ba, sai ya kira na Faisal bugu uku ya dauka hade dayin sallama cikin girmamawa yace sirikina"
"Hafiz ya shafa sumar kanshi kaman Faisal na gaban shi, yace Yayan mu an yini lafiya?
"Lafiya lau In-law yasu Mom da Leemarh?
"Alhamdulillah duk suna lafiya"
MashaAllah how may I help you In-law?
"Hafiz ya sake shafa sumar kanshi sannan yace dama nazo gida ne kuma na kira ta bata daga ba.....
Faisal yace batayi picking ba, toh ko bata kusa ne,
"Wlhy ban sani ba"
Alright"Bari na gwada kira ka dan kara jira Koh"
"Okay babu damuwa"

""Tun farkon shigowarshi harabar gidan take kallonshi kasancewar window dakinta yana facing compound din gidan gaba daya, amma ba lallai kagane akwai mutum tsaye a wajan ba, yau dinnan tsokana takeji kuma akan Hafiz take son saukewa hakan yasa ta samu paper full sheet ta zauna ta yaga kana na kana na, ta dauko fararan duwatsun data debo a garden dinsu ta rinka sanyawa a cikin paper tana dukunkulewa, har ta tara kusan guda ashirin sannan ta tattaro su ta dawo bakin window ta fara jefa masa tana yi tana boyewa jikin purple cotton din dake dakinta.

"Yana gama wayar ya koma ya tsaya jikin motar shi, yana dannan wayar sa, ji yayi an wurgo mishi paper an dukunkule ta da dutse,yayi saurin dagowa yana duba ta Ina aka wurgo masa, Amma baiga kowa ba, ya koma ya jingina ya cigaba da tapping phone dinshi, sai aka kara wurgo wata again, Nan ma ya sake dubawa Amma baiga kowa ba,ya koma ya jingina.
Haka aka ringa mishi har sau goma ana sha daya ne Faisal ya kirawo shi yace Guy na kirata fa bata daga ba, I think bata kusa da wayar ne"
Hafiz yace okay toh ba damuwa"
"Faisal yace Amma na Kira Momma gatanan zata dubata, ka kara jira."
"Toh yayanmu godiya nake*
"Bakomai"
Yana kashe wayar aka sake wurgo masa, wannan karan Hafiz ya kulu dukdama bai da tabbacin ko Hauwa'u ce, Amma ranshi na bashi she is the one"hakan yasa ya kashe wayar ya sanya ta a aljihu sannan yayi folding hannunshi ya daure fuska yana ta kalle kalle ko zai kama mutum, har ya tsura ma window din dayake suspecting daga nan ake wurgowa.

RAYUWAR JIDDAH ✔Where stories live. Discover now