05

316 20 0
                                    

RAYUWAR JIDDAH
part 1/05
Mallakin DielaIbrahim

*****************

..........Gwamna Road suka nufa tun bayan fitowar su daga NAFbase din suka hau kan titin express ayayinda basu tsaya ko ina ba sai bakin gate na wani katafaren gida, wanda yasha gyara, gate din gidan babba ne mai katuwar rumfa ciki da waje, inside the house kuma malam dauda gateman ne zaune kofar dakinshi kusa da gate,zaune yake saman wani dogon bench na  katako,Yana ta faman goga aswaki a bakin sa gefe daya na hannun daman sa kuma radio ce take ta faman surutu,Horn yaji bashiri ya tashi ya leka don yasan mai gidan dai duk yau bai fita ba in ba masallaci dayake zuwa ba, bude separate door din dake gefen gate din yayi hade da lekawa......take ya zare idanu hade dacewa ahhhhhh karamin mai gida MashaAllahu ya fada yana washe baki, Take ya rufe kofar sannan ya nufi gate yana turawa da sauri har karshe.
At that time motocin suka sako kai cikin harabar gidan sukayi parking awajan da aka ware domin aje motoci.
Bude murfin motar akayi tsahon dakika biyar kafin ya sako kafar sa daya waje ayayinda malam dauda gateman ya karaso yana kai gaisuwa cikin girmamawa....alokacin har ya fito yana kuma gyada ma malam dauda kai alamar yana amsa gaisuwar tashi sannan ya mika masa bandir din yan dari biyu sabbi dal, yana cewa malam dauda ayi hakuri da wannan banyi  maku tsaraba ba, malam dauda na murmushi yana cewa ahhh yallabai karamin mai gida wannan kyauta dayawa haka jiya an bamu yauma haka ai hakan ma mun gode sosai Allah ya saka da alkhairi. Shi dai bai tsaya sauraran malam daudan ba yayi wucewarsa ciki dasauri take kuma idanuwansa suka hango masa kanwar tasa tana nufo inda yake cikin sauri itama... hugging dinshi tayi tana cewa Yaya Hafiz welcome back.
Ya kama karan han cinta yaja ya matsa kadan yana cewa lil sis I missed you
"I missed you more Yaya"tayi saurin fada tana kwantawa ajikin shi lokaci daya kuma suna karasawa cikin main parlor dinsu....Mom ya fara hangowa tsaye a dinning tana jera warmers masu kyau na abinci akan dinning, bangaren parlor dinkuma Daddy ne zaune saman sofa daya daga cikin kujerun parlour masu design din Royal.Ayayinda Hannun Daddy ke dauke da newspaper.
Batareda sanin kowa ba ya daga murya yana cewa  Mom,Daddy am back, home sweet home ya fada with so much excitement a fuskarshi, yanayi yana daga hannayenshi sama kaman wani karamin yaro....Lokaci daya mom ta jiyo tana murmushi, haka zalika Daddy ma da murmushi yake kallon Dan nasu.
Leemarh tai masa kuri da idanuwanta tana dariya ta karasa palour wajan Daddy tana cewa su Yaya Hafiz anzo gida dole ka sake da kowa,yanzu kam da awaje ne dakayi kicin kicin da fuska, ka daure kaman baka taba dariya ba, shikam zuba mata idanu yayi yana hararar ta cikin wasa shima ..Cen kuma bayan ta tsagaita sai tace Nevertheless yaya ni nafi son haka saboda kada watacen ta janye min hankalin Yaya na, ta karashe maganar cike da shagwaba tana langwabar dakai ayayinda take kokarin zama gefen Daddy...Daddy da ya dago yana kallon son din nashi yana murmushi ya kalli Leemarh yace exactly kuma maganar ki gaskiya ce fah Auta, kinsan Officers dinnan akwai jiji da kai ya karasa yana shaking head dinsa....shiyasa up till now bai kawo matar aure ba, sosai leemarh take dariya harda rike ciki....tace oooooh yes Daddy ta kanne ido daya tana kallon yayan nata.
Hafiz daya zuba masu ido kaman wani maraya,hakanan fuskar nan ta koma kaman bai taba dariya ba yace haba Daddy, da tsokana za'a tarbe ni yau Koh?,......Nan take Daddy yace Leemarh look at his face......take suka kuma kwashewa dawani dariyan......cikin wasa.
Mom tsaye a dinning tana kallon su cikin sha'awa wanda tun fara conversation dinsu take murmushi itama tana kallon Dan nata yadda yakoma kaman wani maraya,tsabar tsokanan shi da sukeyi, Sai alokacin ta sauka zuwa palour din tana cewa Wallahi ku kyale min Babana hakanan, haba mutum ma ya dade baya gida,and ya dawo yanzu maimakon kuyi masa tarba mai kyau Amma kun zauna kuna tsokananshi, tohhh nagane nufin ku so kuke kucemishi kuna bukatar In-law tohm baza akawo in-law dinba takarasa alokacin data Isa inda Hafiz ke tsaye ta rike mashi hannu hade damashi murmushi tace rabudasu Babana.... Hafiz ya kalli Mom ya tura baki kaman karamin boy yace mom dama nasan ke kadai kikayi missing dina ya karashe yana rungumeta sannan yace kuma ma ke kadai zan kawo ma in-law sukam bazan kawo musu ba.....ae baima karasa ba Leemarh ta ruga da gudu wajan sa tana cewa Allah Yaya munyi missing dinka koh Daddy ta karashe maganar tana kallon Daddy...Ba Hafiz ba har Mom sai da suka dara saboda yanda leemarh tayi reacting,murmushi Daddy yayi yace ae duk yaron daya dade baya gida toh idan ya dawo dole ayi missing dinsa terribly, muma munyi Missing dinka kuma dai gaskiyar Mom ne, muna so ka kawo mana In-law dinmu ya karashe maganar fuska adaure Kuma yana kallon jaridar hannunsa Kaman bashi yayi maganar ba.
Hafiz yayi long breath kafin ya karasa wajan Daddy ya zauna ya rungumeshi ta baya cike da qauna da kewan juna Daddy yace welcome back son,ya aiki
Hafiz yace aiki Alhamdulillah Daddy, jiya nazo amma ban jima a gidan ba natafi saboda wani important meeting danayi attending a Abuja....Daddy yace  Mom dinku ta fadi min so I wanted to call you and she said you are in your way, dukdama baki suka hada da leemarh wai don ka dawo yanzu,....Hafiz yayi murmushi yana kallon Mom da take kokarin zama kusa dashi tace Amma bana fushi da Babana , Leemarh kuma tace and it's was my plan because we really missed you terribly, wannan karan Hafiz can't stop him self from blushing, take ya kuma jin son family dinshi na kara shiga cikin zuciyarshi, suna ta wasa da dariya Hafiz yace Mom where's my Honey?tunda na shigo gidannan banganta ba, ko batasan dawowana bane, let me go and see my honey" I missed her wollah ya karashe maganar yana kokarin tashi daga saman kujera, Daddy yace dashi batanan fah son.
Hafiz ya dubi Daddy cike da tambaya a fuskar shi yace ina take Daddy?
Mom tace "Babana sun tafi India da Baba Yusuf za'a duba mata idanunta, Hafiz ya dafe kai Lord! sannan yace Daddy har yanzu ciwon idanun na damunta ne?
Daddy ya gyada kai, sannan yace Idanun na damunta sosai shine nace Yusuf yatafi da ita aduba idon sannan abata magani, yanzu dai satin su biyu da tafiya amma sun kusa dawowa.
Hafiz ya gyada kai toh Allah yasa adace.
Ameen suna zaune suna ta hira aka fara kiraye kirayen sallah Daddy da Hafiz suka tafi masallaci, Mom da Leemarh kuma sukayi sallan su agida...sai bayan sallan isha'i Daddy suka dawo, sannan suka nufi dinning zasuyi dinner anan suka tarar da Mom suna jiran dawowansu.
"koda suka gama cin abincin palour suka koma sun jima suna ta hira inda Hafiz ke basu labarin kasar dasukaje yin wani course sun sha wahala, sai gashi kuma suna gamawa aka turo shi Airforce Base kaduna."Daddy yace nayi matukar farin ciki da aka maidoka kasarshi koba komai kanatare da family dinka yanzu, Mom ma tace exactly kuma ka tabbatar ka samo mana In-law kafin a kara cilla ka wani gurin, Hafiz kama baki yayi yana mamakin Mom, Leemarh kam kwance take saman kafar Mom  kuma dariya takeyi abinta, Hafiz yace Mom ki kwantar da hankalinki kiyita min Addu'a Allah ya bani mace ta gari,Mom ta capke tana cewa inshallah Babana Ina yimaka kuma zan cigaba dayi.... Daddy kam gyaran murya yayi, sannan ya cigaba da karanta newspaper dinshi har karfe 10
Hafiz ya tashi yana yi masu Mom da Daddy sai da safe, ya kalli Leemarh da har yanzu tana jikin Mom yace Mom haryanzu baki yaye wannan Autan bane wai?
Ahhh toh kaima kafada ai Babana" gatanan kullun shagwaba sai faman nanike min take kaman wata kuliya(cat)
Leemarh ta dago kai tana tura baki tace to bani bace Auta cikin sigar shagwaba.
Yayi folding 2 hands dinshi sannan ya dubi Leemarh yace oooohhh as big as you are, karki manta kina da kanne fah ya fara counting da hannu Yana cewa, akwai su salim, twins,aisha, and maryam('ya'yan kanne Daddy ne),and the rest kice wani kece auta kina wani kwantawa ajikin Mom sai kin sa kafafunta suyi mata ciwo....Allah Mom ke kike kyaleta ma.
Leemarh ta tsuke fuska ta bubbuga kafa ita ala dole shagwaban ya motsa tace Daddyna kanajin Yaya koh?
Daddy yace ooo ooo nikam bazan shiga tsakaninku ba saboda yanzu zakuba mutum kunya.
Hafiz yayi wa Leemarh gwalo Yana cewa kima dena hawa don aure zan miki kwanan nan.......ae bai karasa fada ba ta tashi tana yima Mom korafi.
Mom tace lah lah lah karki biye mashi kinji Auta sai ya farayi kafin azo kanki tunda he is   older than you,Hafiz dayaji maganar Mom sai ya sanya hannunshi a keya yana sosa kai yanacewa"goodnight"."Leemarh tana dariya tace dawo nan mana ka cigaba da tsokana yaya, bai ko kulata ba yayi gaba abinshi tsabar baya son biye wa maganan Mom, shi ya rasa meyasa yanzu suke son takurashi da maganar aure.har yakai bedroom dinsa yana tunani acikinranshi.sannan kowa ya wuce makwancinsa.
Hafiz na shiga daki wanka ya farayi sannan ya canja kaya izuwa sleeping wears fararen riga da wando, harda socks fara abinshi tsabar sabawan dayayi tun suna school idan zasu kwanta bacci sai sun saka socks.. Idan ko baka sa ba, ranar ka shiga uku, don kuwa tun asubahi za'afara maka ihu ana dariya duk abinda kayi aranar sai ayi ta dariya, wannan dalilin yasa ko baka son saka socks dole ka nemo ka sanya don kwanciyar hankalinta...  Hafiz na daya daga cikin wanda suka fara kawo saran sanya su lokacin bacci daganan kuma yazama dole kowa ya sanya".   Ya kwanta yana facing ceiling maganganun Mom & Dad su suke ta faman yi masa yawo a kwakwalwar sa, shikam nawa yake daza'a farayi masa maganar aure, toh wai ma shi da bai taba ganin macen data burgesa arayuwarsa ba, beside shi mace ma bata gabanshi yanzu saboda bai taba sawa aranshi zaiyi tarayyah da mace ba,"Sai dayayi numfashi mai tsayi kafin ya rufe idanuwansa lokaci daya kuma pictures din yarinyar daya bige a hospital su suka fara tsere acikin idanuwansa, saurin budewa yayi yana fadin Hasbunallahu wani'imal wakil, Allah kaimin tsari da wannan yarinyar nikam nasan nine sanadin karayan ta Amma ko mayyace ae ta sarara min tunda nayi mata dukkan abinda yakamata nayi, ya cigaba dacewa Allah yasa ma taji sauki kafin gobe subar hospital din donni bana bukatar ma na sake ganinta, haka yaita faman masifa shikadai kuma acikin ranshi yana danasanin saka idanunshi afuskarta.....ya juya ya kwanta ahannunsa na dama yana addu'a Allah yasa karya kara ganinta a idonsa ahankali ya ringa rufe idanunshi har bacci ya daukeshi.
*********
Karfe Biyar na asubahi ya farka hade dayin salati yana kokarin tashi daga kan gadon, ya nufi toilet yayi alwala yazo ya sauya kaya izuwa ash color din jallabiya ya feshe jikinshi da Arabian perfume Mai kamshi, ya dauki sallayarsa ya fita ahanyar fita ya hadu da Daddy suka jera har masallaci.
Around 6:20 suka dawo gida don saida suka tsaya yin karatu, suna dawowa ya cire kaya ya nufi bathroom donyin wanka kodaya fito lokacin karfe 6:40 shiri yakamayi cikin uniform irin na jiya Amma bana jiyan ya maimaita ba kasancewar yana dasu kusan guda biyar duk kala Daya,Banda Kuma sauran kakin sojojin don kowani rana da irin uniform din dasuke sawa,
Karfe bakwai 7:00 ya fita zuwa dinning yana kokarin answer call  din M.Malunfashi yanacewa kun karaso ne, okay tohm gani nan fitowa, kai tsaye ya nufi dinning room din nan ya samu Mom tana shirya abincin, ya rungumeta Yana cewa good morning my beautiful Mom,
Murmushi Mom tayi sannan tace Morning Son how was your night?
Hafiz yace it was awesome Mom, me Kika dafa mana ne? Yakarasa Yana kokarin bude wani cooler....tace na hada maka komai a basket ka tafi dashi cuz naga kaman zakayi late....Amma ka tabbatar kaci kaji Babana. Murmushi yayi yace that's my Mom, Thank you so much you are the best mommy in whole world, I love you Mom 😘yai mata peg a kumatu sannan ya ansa basket din Yana cewa good bye mom.......Mom ta tsaya tana kallon shin adoringly tana Jin son Dan nata aranta sosai da sauri tace, Take good care of your self Sweetheart and make sure you eat your breakfast.
Okay Mom consider it done.
Bye tace tana daga mashi hannu.
Tana nan tsaye taji an rungumeta tabaya Leemarh ce, tace Mom na fara kishi fah, yau kin manta da Auta,kinma manta ki tashe ni da asubahi, and baki ko leko kin duba ni ba tun jiya, ta karshe maganar kamar me shirin yin kuka,
Mom ta kama hannunta tace Haba Autana kishi kikeyi da Yayannaki....ooo ooo bansan Auta da wannan halin ba.
Leemarh ta girgiza kai... Toh ae.....
Shihhhiiiiiii 🤫 mom ta katse ta tana cewa kul nasan bazaki school bane and shi kuma nasan zai fita da sassafe shiyasa na tashi na hada masa breakfast da wuri.
Leemarh tace Mom stop it please am just kidding nima tunda na kwanta tun jiya sai yanzu na tashi fah, Kawai I blame my self ne da ban tashi da wuri na tayaki aiki ba,......mom tayi murmushi tace don't worry Auta nasan baccin ne yai maki nauyi shiyasa ban tada ke ba., bari naje na duba Daddynku ko ya gama shiryawa, Please ki karasa fito da sauran warmers din dake kitchen kafin mu fito.
Okay Mom dina ta fada tana yima mom murmushi.

RAYUWAR JIDDAH ✔Where stories live. Discover now