15

186 26 19
                                    

RAYUWAR JIDDAH
Part 1/15
Mallakin DielaIbrahim
Am so sorry for keeping you guys so long, bani da lafiya ne, but alhamdulillah sauki ya samu.
Thank you for waiting!!!!

__________________Barhim Estate
Katsina state
8:30am

Ammi,Mama,Abba,Ummi and Momma,Dukkansu zaune suke a katafaren falon Ammi,ayayinda Momma tace Ammi kin taramu anan, Allah yasa dai lafiya?
Ammi tayi gyaran murya kasancewar ta mace mai dan kasaita kadan, tace
Assalamualaikum
Suka amsa da Wa'alaikumus salam

Ammi tace na tara ku anan ne don muyi magana ta fahimta a tsakanin mu, ta dubi Mama kasancewar itace abokiyar shawarar ta, tace Mama wato observation dina da duk wani tunani na daya karkata akan Jiddah da Faisal, shakka babu na hango tsananin shakuwa da sukai da juna, sannan alokaci daya kuma naga tunda yan uwan juna ne mezai hana ahada su aure don anawa tunanin nasan baza su ki son junansu ba moreover auran zumunci na da dadi ko ba komai environment daya suka taso, ga kuma tsantsar kulawa da suke bama junansu,
Ko ya kikace Mama?
Mama da take sauraran Ammi tace Ammi kinsan one thing da auran zumunci shine idan yara basa son junansu to kada ayi forcing dinsu, kina da gaskiya da kikace a hadasu  aure Amma Ni abinda nake dubawa shine why not a tuntube su ko suna da ra'ayin juna aji ta bakinsu.

Ammi tace No bazamu sako yara a maganar mu ba,haba Mama, kina nufin mubi ra'ayin yara, kenan mu bamu isa mu ce masu ga abinda muke so ba, gaskiya wannan ba solution bane....adai canja wata.
ke Momma ke kike zaune dasu Kuma kinsan irin shakuwar dasukayi me zaki iya cewa akan hakan tunda wajan ki Jiddah take bazaiyu na fara da Ummi ba.
Momma tace wato Ammi maganar ki gaskiyace akwai tsananin shakuwa atareda da su, lallai shakuwar da Jiddah da Faisal sukayi ni kaina ina mamakinta.....kallo daya zakai masu kayi zaton soyayyah suke yi while deep inside it su ba ita bace sukeyi, kawai so ne na yan uwan taka, amma ni anawa view din Ammi,
Shakuwa daban haka zalika Soyayyah na aure daban....Ammi bana tunanin suna son junansu, kamar yadda Mama tace a tuntube su toh nima ina bayanta saboda kada ayi forcing dinsu.

Ammi tace auuuu kema hakan zakice....to ina daidai daku ta waiga wajan Abba tace Kai Kuma miye naka opinion din?
Abba yayi gyaran murya sannan ya dukar da kanshi saboda tsananin Jin kunyar Ammi da yakeyi,Yace Ammi duk yadda kuka yi ai daidai ne matukar yaran suna son junansu to ai babu wata matsala.
Ummi tace nikam dama na dade Ina yi ma Jiddah kamum Dana,na dade Ina mata sha'awar auran Faisal, jira nake kawai lokaci yayi, Ammi Ina bayan ki dari bisa dari, nikam ma ba sai an tsaya tuntubar ko suna son juna ba, ni agani na kawai asanya masu rana yau, ayi auran idan taje gidan mijinta ta karasa karatunta tunda shekara dayace ta rage.
(Niko DielaIbrahim gyan gyadi😴 nakeyi sanda Mama, Momma da Abba suke magana, Amma Ummi na fara magana na farka jin ta amshi maganar da hannu bibbiyu na gyara zaman alkalami na nace Yaaaayyyyy Ammi da Ummi kanku naja aradu nima Ina bayanku😉😜)

Ammi ta dade tana tunani, tsahon minti biyar sannan tace agaskiya bazan iya tuntubar Yara ko suna son juna ba, lokacin abu kawai ayi shi, saboda haka kawai nan da sati biyu zamu sa rana Abba take note of this a gidan ka za'ayi komai, ni na gama maganata sauran magana kwa samesu ku basu shawara inma basu fara son juna na aure ba toh su ci dammara su fara don kuwa aure babu fashi (ban dai rantse ba amma fah babu fashi )ta tashi tana tafiyar ta cikin kasaita don dama Ammi haka take, saboda ta hada jini da sarauta ta wajan mahaifiya dukdama ba daga uba bane amma abin yabi jinin jikinta, moreover magana daya takeyi kuma ya zauna ko Mama ta sani shiyasa take bin ka'idojin ta badan tana tsoronta ba sai don Mama tafi Ammi hakuri da juriya kuma tun fil azal zamansu yayi dadi basa fada ko kadan.
Ammi na tashi ta shige bedroom tabarsu zaune sunyi jugum.
Momma nata faman bankawa Ummi harara tace dama na gano ki so kike aiwa Jiddah aure,
Ummi tayi dariya playfully tace Ammi babu ruwana aciki yanzu dai kisamu diyarki ki Bata shawara gwanda dai ayi musha gagarumin biki.
Momma tadau throw pillow ta jefi Ummi tana cewa ai sai kuyi, Ni dauke diyata zanyi ma mubar garin tunda daga zuwanmu kun fara kawo mana kabli da ba'adi🤨
Mama ta amshe da cewa tohhh ya dai isa Ammi ta rigada ta gama maganarta yanzu kamata yayi ku fadi yadda za'a bullo wa al'amarin.
Abba yace mama abu me sauki, ashaida masu don susan halin da suke ciki kamar yadda Ammi ta fadi............
Momma ta katse su tace toh ni dai bari kuji koda kun fada masu ban goyi bayan aiwa diyata aure,bata gama makaranta ba, don haka dole ajira ta gama ehhheee ta tashi ta fice adakin,...Ummi na ce mata, Momma ahuce haka mana 😝 sai kace mu ne muka kawo shawarar, auren zumunci fah akwai dadi Momma......
Amma Ina momma ko waigowa batayi ba ta wuce dakin Jiddah.
Abba yace Ummi kije ki bawa Yar uwarki hakuri, ni yanzu wajan aiki zani anjima saif zaizo ya dauke ki, "Ummi tace toh Abba Allah ya tsare.
Ummi tace Mama bari na shiga ciki.
Mama tace Nima zan shiga na dan kwanta Ammi ta katse min baccin safe yau.
Ummi tace lallai kam yakamata arama baccin nan don itama yanzu haka baccin ta koma.
Mama tace kwarai kaman kinsani, bari na shiga ciki,"To Mama.

RAYUWAR JIDDAH ✔Where stories live. Discover now