23

209 19 7
                                    

RAYUWAR JIDDAH
Part 2/3
Mallakin DielaIbrahim
Hello Fans Taqabballahu minna wa minkum salihul a'amaal
*May Allah SWT accept it from us as act of ibadah *

     And here is your😁😁😁😁😁
👇👇👇👇👇👇👇👇👇👇👇👇
GORON SALLAH 📚 ALKALAMIN DIELAIBRAHIM ✍️

__________________________________
Kinkinau GRA,kaduna state
4pm

"Gidan Momma"
Hakika gida ya cika da baki kasancewar al'adar katsinawa ce sukanyi taro idan za'a yi gaisuwa, sa rana, kawo lefe duk sai sunyi taro kamar biki, awannan lokacin Jiddah da Fatima suna kuryar daki, suna ta hira abinsu, haka zalika su Ummi na bangaren Momma suna ta faman harhada kayan daza'a baiwa baki amatsayin tukwici.....Ammi da Mama Kuma nata faman taya yan aiki suna harhada abin buda baki(kayan Iftar) da alama bakin anan zasu sha ruwa saboda kwarya kwaryar walimar da ake hadawa.

"Abba da abokanan shi suna sashin Yaya Faisal",
"Muhammad,Faisal, da Saifullah kuwa suna zazzaune a falon baki, da sauran bakin da sukayi 'yan uwan Abba da sauransu.

"Motoci hudu ne suka shigo harabar gidan suka nufi "parking lodge" yayinda suka soma fitowa daga cikin motar cikin shiga ta alfarma, kallo daya zakai masu ka hango tsantsar farin ciki da rufin asiri atare da family din, kowa ya fita amma banda Daddy yana zaune cikin motar ya dafe kanshi, Alh.Yusuf ya dafa shi yace Daddy lafiya me ya faru ne?
" Daddy yace Ya ilahi ! yana mai dafe forehead dinshi yace Yusuf kai na ne yake sara min lokaci daya"
"Alh.Yusuf yace Subhanallah ciwon kai farat daya, toh Allah ya kawo saukin ciwon kan" amma zaka iya shiga ciki kuwa?
"Bismillah Yusuf muje kawai inshallah zai yi sauki"
"Toh Daddy, ya dan tallafa masa ya fito sannan Saifullah yai masu jagora suka shiga katafaren falon Momma, falon da take saukar da baki maza, falon dai babba ne duba da yanayin zuri'ar su dukda ba wani yawa suke dashi ba, but, Ammi ta bata shawara da tayi falon baki mai girma sosai....kuma falon yana shimfide da center carpet, kujeru royal cream color, da kuma tum tum yadda kusan falon sarki to haka nata ya kasance sai kamshin turaren wuta ke tashi," kowa yasamu waje ya zauna cikin palour din wanda tuni falon ya cika fam da baki.
"Sai bayan sun zazzauna ne suka gaisa da kowa sannan sai alokacin Abba ya shigo palour din da sallama cikin fara'arsa ya nufi su Daddy yana mika masu hannu suna gaisawa, one after the other, har yazo kan Daddy,

"Hakika Abba bai kalli fuskar Daddy ba Amma ya gane  shine uban Hafiz kuma uban Halima saboda yanayin shigarshi ta fita daban dana kowa, "don haka ya mika masa hannu cikin girmamawa da karamci, amma me zai faru hada idon da sukayi ne yasa zuciyoyinsu bugawa lokaci daya, Abba yayi saurin sakin hannun Daddy nan da Nan annurin fuskarshi ta dauke ya ja da baya, samun waje yayi ya zauna yai shuru, har aka fara magana Abba baice komai ba,haka ma Daddy bai ce komai ba, har wasu daga cikin mutanen palour din suka fahimci alamar damuwa a fuskokin Abba da Daddy.

" Abokin Abba da Yaya Idris suke ta magana sai dai idan anzo wajan abinda yakamata atambayi Abba sai su juya su tambaye shi, kuma koda zai amsa masu bazai basu full attention ba, sun rasa gane dalilin Abba na canjawa all of the sudden, haka zalika abinda ke faruwa da Daddy kenan, har aka Sanya rana without their knowledge don su hankalinsu ma baya kansu, sai da aka zo wajan sadaki, sai Abba yace, ba zamu amshi sadaki ba, Infact auran ma na soke "no wedding, no union" yana kaiwa nan ya tashi yabar palour batareda ya saurari kowa ba.

Turkashi😯ko ya za'ayi yanzu🤔

*************

"Alh.Yusuf shi ya kama Daddy suka fita waje saboda hayaniya dayai yawa,taro ya hargitse, yayinda duk mutanen wajan basu san dalilin dayasa Abba zai canja magana ba, kuma wai an fasa aure, to me ke damun Abba, wannan tambayar itace su Faisal suke ta faman yi a zukatansu  dama Family din Daddy"

"Cikin gida kuwa labari har yaje wajan su Ammi, a razane Ummi ta tashi tace Faisal me kake fada, Abba ya soke aure, to meyasa, wani abune ya faru?

"Faisal ya zayyano mata yanda akayi" Lokaci daya Ummi taji there was something fishy,inba haka ba, me zai sa Abba ya yace an fasa aure, da sauri ta tashi  tace Faisal miye sunan mahaifin yaron?
"Faisal yace "Engr.Abubakar Yusuf"Sunan yaron Ha...............
"Ai bai karasa ba sai ganin Ummi sukayi ta fita waje da gudu"""

RAYUWAR JIDDAH ✔Where stories live. Discover now