20

211 21 14
                                    

RAYUWAR JIDDAH
Part 1/20
Mallakin DielaIbrahim

____________________________________
Rahmat close
Unguwan rimi

"Muhammad yace to mun iso guys sai mu fita Koh"
"Faisal da Saifullah suna Masa kallon mamaki, Faisal can't stand it yace Muhammad me zamuyi agidan su Fatima Kuma?
Muhammad yace kamanta kace min na karasa abin da nafara, I was the one that brought the first idea, and now this is the solution, Fatima is your best solution"
Sosai maganan ta taba zuciyarshi yama kasa magana, yace kana nufin nayi soyayyah da ita?
Yes har aure ma"
Faisal ya soma jijjiga kai yace nooooo it can't be possible Muhammad, ban taba son Fatima ba infact maybe tana da wanda take so, meyasa ni kuma zan mata katsalan dan a al'amuranta, please mu canja shawara.
So kana nufin kace batai maka ba kenan,
Noooo ba haka nake nufi ba, ni wannan bai dame ni ba, Amma abinda nake so ka gane shine what if tana da wanda take so?
"Saifullah yace mezai hana mu jaraba zuwa mugani inshallah babu ma"
Faisal yayi shuru ganin yan uwan nasa duk sun dage akan suje hakanan suka sauka a motar sukayi knocking gate din,Jim kadan sai aka bude, itace da kanta, sanye take da atampha dinkin straight skirt da riga tayi dauri mai kyau kaman wacce zata biki, kaman tasan da zuwansu, ta zare idanu tace lahhhh Yaya Faisal, Yaya Muhammad sannunku da zuwa ku shigo Mana,
Su ka shiga abinsu tai masu jagora har falo kasancewar daga ita sai Mama agidan su biyu basu da yara, gidan a gyare yake tsab sai kanshin turaren wuta yakeyi.
Fatima tace bari nayi wa Mama magana sukace toh"
Tana shiga kiran Mama sai ta dauko veil dinta ta yafa sannan ta nufi kitchen ta shirya musu snacks da zobo drinks da swan water, ta kai musu, ta koma gefen Mama ta zauna abinta, har suka gama gaisawa sannan mama ta basu wuri,"
Muhammad yayi gyaran murya yace kanwata nifa am salivating zobo drink dinnan ya tafi da kwadayina"
Fatima tace lahh Yaya Muhammad kasha mana, yace ai ko baki ce ba sha zanyi ya fada yana kokarin daukan glass cup yace wasu sai dai suyi ta kallo daga nesa bazasu iya sha ba"
Faisal yace kaji dashi dan iyayi kawai, Saifullah ya dau snacks (cake) ya soma ci abinshi sai da suka ci suka sha sannan, Muhammad yace Fatima mu zamu wuce mun gode ko, Allah ya biya ki, Allah ya kawo miji na gari"
Fatima tayi murmushi,tace nagide agaishe min da Jiddah, zata ji sosai ai batasan zamu zo ba da ta biyo mu.
Fatima tace lallai kam.
Ta raka su har bakin gate sannan suka tafi tana komawa taga sun bar black leather, tayi saurin dauka ta bisu Amma Ina tuni sunyi nisa.
************
Suna barin unguwan rimi suka dau hanyar gwamna road, Faisal yace Ina kuma zamu?
Saifullah yace ya wuce gidan su yarinyar nan da muka taba bigewa tun last year" ai har yanzu mutumin ka bai manta ta ba yana nan ya sanya ta arai.
"Faisal yace kut!all this while baka fada min ba"Muhammad yace na cire raine da ita bro Amma yau naji bazan iya hakura ba dole na koma gidan ko zata iya gane ni!
To Allah yasa ta gane ka.
Ameen
Suka tsaya akofar gidan knocking sukayi, malam dauda ya bude kofar yace sassanunku, wa kuke nema ne?
Faisal yace sannu malam don Allah muna neman wata yarinya ce yar fara haka anan gidan, bamu san sunan ta ba,
Malam dauda ya sake kallonsu yaga dai daga gidan mutunci suke saboda yanayin shigar su, sai yace Ko Halimatu kuke nufi?
Saifullah yace wlhy bamu san sunanta ba Amma confirm Nan ne gidansu fara ce dai haka
Malam dauda yace yarinyar gidanan guda Daya ce Kuma ayanzu haka sun dan fita ita da kakarta basanan......Yana cikin magana kuwa saiga motar su ta shawo kwana, su Faisal suka koma gefe suka basu waje......amma abinda ya basu mamaki shine sai sukaga Granny ta fito tana cewa Handsome da Faisal ya akai kuka gane gidan?
Faisal suka koma kallon kallo da Muhammad, daga bisani HAFIZ ma ya fito yana nuna murnar ganinsu, yace how comes kuka gane gidan muma fa yanzu haka daga gidanku muke munje gaishe da Jiddah, Faisal da Muhammad basu dena mamaki ba sai da Leemarh ta fito acikin mota, hamdala Faisal yayi ganin abin zaizo da sauki inshallah ga dukkan alamu Leemarh kanwar Hafiz ce, yayi murmushi yace wlhy kuwa mu nan ma wani damuwan mu ne ya kawo mu😂
Hafiz da granny sukace damuwa kuma, Muhammad yadan shafa keya yace granny sai mun zauna zakuji komai,
Hakanan granny tace toh ku shigo mana lema kaisu babban falo please.
Bata kalle su ba ta zumbure baki tana kunkuni tace granny ni gaskiya bana son wannan sunan wollah it's Leemarh not Lema😂 Kuma batayi musu magana ba, sannan ta ganesu sarai kuma tasan saboda ita suka zo saboda tagane right from there reaction da suka ga granny da Hafiz....kai tsaye ta bude falon baki a gyare yake tace bisimillah ku zauna ta nufi fridge ta dauko masu ruwa da drinks ta kawo masu tana cewa kusha ruwa.
Faisal yace mun gode" bata tsaya amsa musu ba tai shige warta, abinta,sai ga Hafiz da granny sun shigo, Bayan sun gaisa ne Faisal yake shaida musu abinda ya kawo su, granny tace MashaAllah, Ashe Handsome ka dade da sanin matar da nayi maka, Amma fah akwai shagwaba don har sai ka gaji,Faisal yace barshi granny ai yasaba da shagwabar kanwarsa Kinga ko abin bazai zame mashi sabo ba.
Hafiz yayi murmushi yace MashaAllah gaskiya kam don Jiddah oga ce a rigima, don ko kafarta Leemarh bata kawo ba"
Faisal yayi murmushi yace kwarai kusa Jiddah ta wuce misali a rigima da shagwaba.
Haka dai suke ta hira har granny ta wuce ciki Mom tazo suka gaisa ta tamabaya yaya jikin Jiddah saboda tunda su granny suka dawo shekeran jiya take bata labarin Jiddah to which har taji Jiddah ta shiga ranta moreover Hafiz yanuna ita take so shiyasa tace su shirya yau suje su dubota, sannan ya fada mata itace ta taba diba mata blood sample a NAFHospital.
Su Muhammad suka ce jikinta lafiya lau, tace toh MashaAllah Allah ya kara mata lafiyar ido.
Ameen.
Tabar su suna ta hira abinsu har magrib yayi sukayi sallah sukace su zasu wuce amma Ina Hafiz ya hana su tafiya, yace dole sai sun tsaya sunci abinci.
Hakanan suka koma gidan, alokacin suka iske Leemarh na jera abinci a dinning, Hafiz yace suje su ci,
Leemarh ita tayi serving dinsu, Muhammad nata kallon ta,suna ci Saifullah na yaba girkin yana cewa Leemarh don Allah baki da kanwa nima adan kara ni, kingansunnan duk suna da budurwa ni kadai ne suka ware,
Leemarh tayi murmushi tace kada ka damu kaima zan samo maka wacce ma ta fi nasu so miliyan miliyan, Faisal yace Inaaaa ai banga wacce tafi Fatima ba, Hafiz yace nima dai banga wacce tafi Hauwa'u ba, Muhammad ya tura hulanshi gaba yace ita kanta wacce tayi maganar tasan babu wacce ta fita, ya juya wajan Saifullah yace malam kaidai kawai kace asamo maka yar dai dai misali😂
Suka kwashe da dariya, (Ni ko nace what a happy moments for the guys)
Karfe takwas suka bar gidan bayan Muhammad ya shawo kan Leemarh har da ansar contact, suka koma gida, Jiddah taita kumbure kumbure wai sun tafi yawo basu fada mata ba, haka sukaita lallashinta....Faisal ya bata labarin cewa ai Leemarh kanwar Hafiz ce, MashaAllah Yaya muhammad congrats Jiddah tace ai sunzo bayan tafiyan ku.
Saifullah yace gaskiya abu yayi kyau kowa yasamu angle dinshi, Jiddah tayi murmushi tace saura kai Yaya Saifullah, kada ki damu Ni tawa matar ba anan kasar take ba" Jiddah tace lallai kam na tuna yaya, ai kai matar kama duk tafi nasu matan😉
Dariya suka ringayi
tashi tayi ta nufi wajan su Momma da Ummi,
Ai kuwa ta same su zazzaune gaba dayansu suna hira, itama tayi joining dinsu.
************
The next day
Da yamma misalin 4pm Ammi ta kara tara kowa a falon Momma, na taraku ne saboda nayi wani magana mai muhimmanci, Muhammad,Faisal da Saifullah na baku nan da wata daya ku kawo matan da zaku aura, musamman kai Faisal da kace kun daidaita da ita toh Ina ganin naka bazai dau lokaci ba, Amma na barshi duka awata daya, bana son naji wata magana ta fito daga baya kunaji na.
Suka amsa da toh Ammi, Jiddah ta tashi zata fita saboda bata so ai mata maganar aure 😂, Ammi tayi saurin cewa koma ki zauna Ja'irah ai banzo kanki ba"
Momma ke kike goya mata baya duk abinda takeyi" Jiddah ta kalli Ummi da Momma tayi rau rau da idanu😖tace toh ni Ammi ni me nayi?
Ammi ta galla mata harara, sannan tace kada kiga Faisal yace yana da wacce zai aura ki dauka kaman na rabu da kene, toh kema kisani kina kan layi kuma kishirya ba ruwana da wai makaranta ko wani abu, kina jina lokacin abu in yazo kawai ayishi don haka Ina sauraron ki.
Jiddah ta gyada kai, tace toh Ammi"
Sannan Ammi ta sallami kowa ya tafi dakinsa.
********
Sati guda sukayi a kaduna, Abba,Ummi,Ammi da Mama suka koma katsina, mazan kuma sunce ba yanzu ba....sai faman chilling sukeyi barin ma Muhammad da suke ta soyewa abinsu, shi kuma Faisal ahankali yake nuna ma Fatima so wanda tun bata fahimta har ta soma ganewa, kuma Jiddah batasan komai akan soyayyar ba, ita Fatima atunaninta Jiddah ta sani shiyasa batai mata magana ba, kuma bawai sun saba da Faisal din bane all this while suna dai waya kuma Yana zuwa gidan su jefi jefi......nidai Ina musu fatan Alkhairi na tafi bangaren Hauwa'u & Hafiz😍

****************
Ranar Saturday
ranar ana ta iska kaman za'ayi ruwan sama, kwana uku kenan ana zafi ana ta jiran saukar ruwa, Jiddah na kwance saman gadonta tana karanta karatun Alqur'anul kareem, gefen ta letters din Hafiz ne da take ta dubawa tun safe kafin ta fara karatu.
Hafiz ya kira Jiddah a phone yace tazo Gamji, yana son ganinta 4pm.
"Tace toh"
Aikuwa 4pm ta fita a gidan Napep ta dauka yakaita gamji direct, tana zuwa ta biya kudin shiga ta shiga tana dube duben inda zata hango shi,
Cen ta hango shi wajan bishiyar mangwaro ta wuraren ruwa zaune saman carpet, ta nufi wajan tai mashi sallama ya amsa ya tsura mata idanunsa masu kyau yana kallon kyan datayi.
Bayan ta zauna yace sannu Hauwa'u'
Tace yauwa Ina wuni"
Lafiya lau yasu Momma?
Suna lafiya'
MashaAllah....ya dan tsagaita sannan yace HAUWA'U kullun muna waya amma na kasa fahimtar inda kika dosa, am eager naji answer daga wajanki.
"Jiddah tayi shuru tana wasa da yatsun hannunta ahankali tace "Mi Alma" reaction dina towards you ya isa ka gane inda zuciyata dani kaina na dosa, I can't say it in words, Amma ka bini bashi zan fada maka watarana....sai kawai tayi shuru abinta.
Sosai statement dinta ya Shiga ranshi cen yace "Mi Alma"
What's that?
Jiddah ta kulle fuskarta da veil dinta tace most you know?
"Yes I want to know"
"Jiddah tace nooo not now, the journey is still far akwai sauran time, don't be faster than your shadow kaji"
Hafiz yayi kayataccen murmushi yace MashaAllah Allah ya kaimu lokacin"
Ameen, Hira suka cigaba dayi har ruwan sama ya sauko mai karfi da sauri suka tashi suka nufi inda motar shi take anan suka karasa hirar tashi, Hafiz yake cewa azumi fah ya kusa Kinga anfara ruwa Jiddah tace Alhamdulillah
Allahumma Sayyiban Nafi'an🌧️
Hafiz yace Ameen ya rabbal alamin, ya kalli Jiddah yace HAUWA'U danyi min masifar 😁 nan mana,
Jiddah ta zare idanun ta tace ai yanzu am not in the mood of that, kabari zan maka watarana.
Hafiz yayi dariya yace wato shi masifar ma sai ana cikin mood?
Jiddah ta gyada kai"
To Allah ya kawo sauki"cewar Hafiz ya waiga yana kallon yadda ake ta ruwan saman abin gwanin ban sha'awa.
misalin 5:30 sannan ruwan ya tsagaita suka bar park din, yayi dropping dinta a gida shi kuma ya wuce gida"
*****************
Katsina state

Engr.Abubakar Yusuf (Daddy)ne yake tafiya cikin mota hankali kwance ya dawo daga meeting da clients dinshi, Hotel din daya sauka nan ya nufa, Amma ganin wani supermarket sai ya tsaya ya siyawa Leemarh tsaraba don gobe zai wuce da sassafe kuma baya tuananin zasu bude da safe, yayi parking ya shiga ya zaba su chocolate saboda cimar ta ce sai ya daukawa Mom perfumes masu tsada, Hafiz ma perfumes aka daukar masa,yaje ya biya kudin ya fita yasa key zai bude motar shi kenan yaji ankira sunanshi da muryar da bazai taba mantawa ba dukda manyartar muryar Amma yasani ko da kuwa bai juya ba.
"Abubakar Yusuf"
Yana waigawa ya hangota tsaye tabbas itace, dama tana raye aduniyan nan, tuni idanuwansa suka kada suka canja launi ciwon dayake fama dashi tsahon shekara da shekaru sai yau ya sake dawo masa sabo"rasa abin cewa yayi kawai......
Ahankali ta taka zuwa inda yake tace Yusuf Abubakar"kai nake gani ko mafarki nakeyi.
Daddy cikin murya mai rauni yace Haliiiiimaaaaaaa!!!!!!!!!!!!!!!!

************
Alhamdulillah I've come to the end of Part 1/20
To be continued Inshallah
Please do vote and comment

RAYUWAR JIDDAH ✔Where stories live. Discover now