01

1.5K 52 7
                                    


Assalamualaikum
Dasunan Allah mai rahama mai jin kai

*****************

Assalamualaikum Fans
Na dawo muku da sabon labari to which I hope zai nishadan tar daku, fatana dai kukasance atare  dani in this long long journey, zanso ku biyoni don jin sabon labarin danake tafe dashi,mai suna Rayuwar Jiddah
***********
I DielaIbrahim assure you that,I'll never disappoint you with this story  inshallah but,In need of your support for sure🙏 just to encourage me.(please).

Rayuwar Jiddah
Part 1/01

____________________________________
Gwamna Road,Kaduna State
10 of August,1988

******
Sefa Specialist Hospital
5, College Road,Badiko Kaduna State.

Misalin karfe takwas 8pm wata karamar mota kirar Toyota ta kutso kai cikin harabar asibitin direct wajan parking ta nufa, cikin sauri kuma batareda bata lokaci ba wani kyakkawan mutum ya fito ya bude kofar baya, kafin ya fara kiciniyar fito da matar dake back seat, babu abinda yake fitowa daga bakinshi sai sannu,yayin da yake kara sauri yana fito da ita daga cikin motar, Bayan ya fito da ita ne ya kulle kofar, sannan ya kamata suka nufi hanyar cikin hospital.

Late pregnancy ne ajikin ta tana cikin third trimester kallo daya zakai mata kagane she is in second stage of labor  ita kadai tasan irin wahalan da take sha
Dukdama da alamar shan wahala da matar take ciki bai hana ta daure tana takawa ba har suka isa cikin hospital din.....Wasu Nurses guda biyu da fitowansu kenan zasuje wajan doctor suka hangosu ba shiri suka nufi inda suke sa'annan suka kama matar sukayi cikin labour room da ita
Sai da suka sanar da doctor, sannan suka dubata cikin ikon Allah Kuma suka ga tana mataki na takwas to which da alamar haihuwan akusa kusa take.

Barinta sukayi for an hour, dukdama suna jin ihun datake ta faman yi, hade da Addu'o'i sai dai fa ihun nata yafi yawa, ta Kira nurses da sunan mijin nata zai kai akalla so hamsin da wani abu Amma  Nurses din koh basu je sun dubata ba har saida sukaji shurun matar lokaci guda kuma sukaji kukan jariri sannan sukayi ciki da gudu.

Da mamakin su ko suka ga 'Da ya fado sai faman tsala ihu yakeyi, matar kuma idanun ta arufe kaman mai bacci tayi shuru, ba shiri suka soma aikinsu to which sai da suka dauki tsahon minti ashirin suna gyara matan da Kuma Dan data haifa.
Cike da murna suka mika ma mutumin daya kawo matar, suna mishi congratulations dayar ke cewa hope kaine baban baby?

Murmushi yayi yana gyada masu kai,bakinshi kuwa ya kasa rufuwa tsabar murna da farin ciki
Nurses din sukace it's a boy

Alhamdulillah ya furta baby boy
Allah na gode maka hade da
Kissing forehead din babyn, sannan yai mashi addu'a ya Kuma karagodewa Allah dayai mashi babban kyauta,..... Dago kai yayi dasauri Yana ce musu " can I see my wife please?"

Daya daga cikin nurses din tace
"Yes sure" but Bari muyi transferring dinta zuwa ward tukunna.

Gyada masu kai yayi hade da neman waje yazauna Yana kare wa kyakkawan jaririn kallo, fadi yake MashaAllah, a ranshi kuma Yana ta saka kamannin da sukeyi da jaririn, Dan kuwa kallo daya zakaiwa babyn kasan ya dauko kaman ubansa sak.....Yana nan zaune sai faman wasa yake da jariri yaji nurse na magana

Sir,Munyi transferring dinta, you can now see her"

Okay thank you" ya amsa cike da annuri a fuskanshi burinshi bai wuci yaga matar tashi ba ayanzu.
Da sauri ya nufi ward din wanda yake cen sama, Kai tsaye dakin ya nufa ya tura ahankali, gadaje shidda ne a ward din, ita tana cen kurya don haka Kai tsaye yayi wajanta yana murmushi......itama dai murmushin ta sakar mashi, sai dayayi kissing dinta a forehead kafin ya nuna mata baby, yana cewa

It's a boy, and you see he looks like me, ya kuma kissing forehead din babyn yana cewa my look alike you are highly welcome to the world.

Wani murmushin ta kumayi ta dubi Uban dan nata, wani irin kara sonshi takeyi...... cikin kula da nuna son ganin babyn playfully tace toh ni bazaka bani na dauke shi ba, ko addu'a nai mishi.

RAYUWAR JIDDAH ✔Where stories live. Discover now