Page 1

1.1K 48 1
                                    

Assalamu Alaikum ,we met again a wannan sabon littafin nawa mey suna ARZI'KI RABO Allah ubangiji yasa na kammala lafiya,ina wa masoyana fatan alkairi we are together always and forever💕


Note:fiction

Written by Dijensy

   Dedicated to our mothers

        
     *****
Kano 

Gidane madedeci d'aki biyu yake d'auke dashi tsakar gidan ma ba wani fad'i gareshi ba.Sede ba lefi gidan ya tsaru ga shafe da akai hakan ya nuna alamar ba a dad'e da tarewa ba.Cikin sitting room kuwa yanda aka ziba kujeru masu tsada ba za'ace a wannan gidan suke ba d'akin gado ma haka furnitures ne tsadaddu d'akin kansa da'kyar ya iya d'aukan gado ,wardrobe se a d'ayan d'akin aka sa.

      Wata mace na gani a d'akin wadda ke zaune kan kujerar mirror tana tsara d'auri ,mashaAllah kallo d'aya zakai ka gano kyau da take dashi ,fara ce amma ba irin tass d'innan ba gata da hanci dogo haka girarta ma sirira lips nata yasha maroon janbaki ga earings da necklace nata masu stones green,tana sanye da atamfa green me d'auke da ratsin orange da black .Kayan jikin nata sosai sun d'auketa chif a jikinta,koda ta mi'ke bayan ta kammala d'auri na lura da tsahonta medium ce domin baza a kirata gajeriya ba haka baza a kirata doguwa ba  gashi batada 'kiba .

     Wayarta ta d'akko dake kan gado ,call log naga ta shiga inda tayi dialing suna "My Dear".Ba jimawa akai answering ta d'ayan 'bangaren " My Azizaty" aka fad'a.

      "Dear naji shiru baka taho bane?" Ta tambaya murya 'kasa-'kasa.

      "Azizaty sorry! Umma ce ta tsayar dani kinga amma yanzunnan zaki ganni". Ya fad'a.

     " Toh shikenan kagaida min ita".Ta fad'a.

     "Yawwa my azizaty sena dawo".Ya fad'a.

     Bayan ta katse wayar ne tayi hanging tare da sakin murmushi ,fuskarta ta sake kalla jikin mirror d'in sannan ta fita daga d'akin.

     Bayan like 10minute tana zaune a sitting room ta jera tray da sauran jug da cup ga warmers a kai ,tana danne-danne a wayarta tajiyo knock. Ba 'bata lokaci ta tafi bud'e 'kofar ,koda ta isa soron ta jiyo muryarsa yana waya lalla'bawa tayi ta bud'e 'kofar da sauri ta la'be bayan 'kofar.

    Yana shigowa kafin yayi wani motsi yaji an rufe masa ido da tafin hannu ,jin 'kamshin turarenda ke sanyaya masa rai yasa yayi saurin sakin murmushi.

     " Azizaty! "Ya kira sunanta.

     " Na'am Dear sannu da dawowa".Ta fad'a bayan ta sauke hannunta.

        "Wow! Azizaty irin wannan kyan haka ai seki sa na kasa shiga ciki". Ya fad'a harda zaro ido.

      Wani murmushi ta saki wanda ya sake bayyana kyawunta." Toh ka taimaka mu shiga".Ta fad'a.

ARZI'KI RABO(Completed)Where stories live. Discover now