Page 14

176 18 0
                                    

     Sis feezoh tnx for ur concern, Allah ya bar zumunci we are always together😘

  Mommy da ganin yanayin reaction na Abba yasa ta sake zage dantse.

      "Eh sakinta zeyi".Ta fad'a babu alamar damuwa tare da ita.
 
      " Kina da hankali kuwa Maryam? Ina tunaninki? Ina iliminkii ? Kina abu kamar wata 'karamar yarinya wannan ai shirmene!"Abba ya 'kare maganar  cikin d'aga murya dan ransa ya 'baci.

      "Ba zancen rashin hankali,nide da raina bazan bari 'yata tashiga wani hali na rayuwa ba,wannan yaran baze iya ciyar da Reyhana ba balle bata sittira kana gani wani nauyin ya sake hawa kansa".

       " Maryam arz'ikinnan kece mey bayarwa neh? Kada ki manta bada arzi'kina kika aureni ba".Abba ya fad'a.

      "Da daban yanzu daban,shikenan kafiso kadinga ciyar da ita tana gidan auren nata ? Haka ake rayuwa?"

       "Maryam bana son sakarci fah,ke yanzu  ba abun kunya bane a gareki ace d'iyarki daga zuwa wanka gida aure ya mutu yaran da koh shekara biyu da aure basi ba".Cewar Abba.

      " Du kai ka janyo mah yarinyarnan ta aureshi tun farko seda nace maka kada ayi ka'ki jina, yanzu kaga irin halin 'yarka data shiga kuma wai a haka kake so ta cigaba da rayuwa,kafiso sede kullum ka dinga yafita mata kud'i tana cida kanta da mijin koh? "

     "Maryam ke meyasa bakya jin magana neh a rayuwarki?" Abba y fad'a tare da mi'kewa tsaye.

    Itama Mommy tashi tayi daga zaunen."Kasan Allah bazan ziba ido Reyhana ta shiga cikin rayuwar 'kunci ba ,yarinyar da bata taso a wahala ba kawai rana d'aya ta shiga 'kuncin rayuwar da bata san ranar barinta ba".Mommy ta fad'a.

      "Baza a raba masu aure ba na fad'a maki ,wannan haukar baza ayi dani ba". Abba ya fad'a.

      " Shikenan idan kai bazaka d'au mataki ba ni zan d'auka".Mommy ta fad'a.

     Ba tare da ta jira Abba ya sake magana ba ta fita daga d'akin fuuuu.Yana kiranta amma tayi banza dashi ta koma d'akinta.

       Daga yara har Reyhana ba wanda yasan meyake faruwa sede sunji ba Mommy a parlor ba Abba dan ko alamar su babu ,dukansu kowa d'akinsa ya koma Reyhana itama haka.

     Tunanin komawarta gidanta ta shiga yi ,sede kuma abin da yake bata mamaki shine haryanzu Mommy bata yi mata maganar hakan ba.

    Tana cikin wannan batunne kiran Ahmad ya shigo.

     "Ummu Nasreen". Ya kira sunanta.

      Bayan sun gaisa yake tamabayarta ya batin dawowarsu.

       " Azizaty ana ta shiri?"Ya tamabaya.

       "Uhmm".Ta amsa.

       " Kin jiki ,gara ma ki bud'e baki ki magana kin shagwa'be da zaman gida koh toh aiko ki shirya ina nan ina jiranku".Ahmad ya fad'a.

       "Se mun 'kara sati biyu".Ta fad'a cikin zolaya.

       " No shekara".Yayi gatse.

      Haka suka sha hirarsu lokaci har yaja ta fara jin bacci dan haka sukai sallama ta kwanta.

             ***
     Washegari da safe koda Reyhana ta tashi taga Mommy bata ma shigo ba,Nasreen  ta lura taga itama ta tashi dan haka ta d'auketa.

       Tana bata mama sega Walida ta shigo d'akin dama  yau Saturday.

       "Mommyn Nasreen ina kwana". Walida ta gaisheta.

       " Au yau kuma sunan da aka samun kenan".Reyhana ta fad'a bayan ta amsa.

       "Mommy bata fito ba?" Reyhana ta tamabaya.

       "Eh nima ban ganta ba". Ta amsa tare da zama kusa da Reyhana tana shafa gashin Nasreen.

          Abba around 8:30am ya sakko 'kasa, Walida ya tarar da Ikram a 'kasa yake tambayarsu Mommy suka ce bata sakko ba.

       Abba kai kawai ya kad'a ya koma sama dan yasan dalilinta na 'kin fitowa.Koda yaje a bakin d'akinta ya tsaya yana knocking tare da kiran sunanta amma tayi burus.

        " Maryam ki fito na fad'a maki".

        "Na fito na muku mey?" Mommy ta fad'a.

          "A'a kamarya ? Da haka kike yi ga yara nan suna jiranki a 'kasa,ki fito kiyi breakfast".Abba ya fad'a cikin sanyin murya.

       Haka ya rabi da ita ya sakko daga shi se yaran sukai breakfast ,Reyhana ma se daga baya tayi nata breakfast d'in.

       Abin ya fara damun yaran dan Mommy bata saba haka ba.Suna cikin  wannan batun ta sakko.
   
      " Mommy ina kwana ".A tare suka gaidata.

      Sun lura mood d'in Mommy hakan yasa suka d'an yi shiru.

       " Lafiya".Ta amsa muryarta a ciki-ciki.

        Kitchen ta nufa ba tare da ta sake cewa komai ba.

       Abba kuwa yana d'akinsa,Reyhana tana d'aki itama basu jima da yin waya da Ahmad ba.

       Mommy a kitchen tayi breakfast d'inta ta shiga d'akin Reyhana.

        "Mommy ina kwana". Ta gaidata
    
        " Lafiya".Ta amsa.

        "Reyhana".Mommy ta kira sunanta cikin wata murya lokacinda ta zauna.

         "Na'am". Reyhana ta amsa gwiwarta ba 'kwari.

           "Kinsan ni mahaifiyarki ce kuma bazan yi wani abu dan cutar dake ba koh?" Mommy ta tambayeta.

         Kai kawai Reyhana ta kad'a alamar "eh" ba tare da tace komai ba.

          "A gaskiya ni ban amince da komawarki gidan Ahmad ba,bazan amince ki cigaba da zama a irin wannan rayuwar ba". Mommy ta fad'a.

          Wani irin fad'uwar gaba taji ,a take zuciyarta saurin bugunta ya 'karu.

        "Reyhana a kullum ina fad'a maki ke ba tsarar Ahmad ba ce,ki duba kiga aikin dayake baze iya ri'keku ba kuma yanzu nauyi ya 'karu idan yau Abbanki ya baki kud'i gobe wa ze baki idan matsala ta faru? Wannan abubuwan nake guje maki shiyasa tun farko na'ki amincewa da aurenki dashi,dan haka tun ba'ai nisa ba gara a yanke ala'kar aurenku ,gatanan dama Allah yayi itace rabon auren". Mommy ta fad'a tare da kallon Nasreen.

        Reyhana jinta take kamar wata kurma ,kwalla ta cika taf a idanuwanta a take ma'koshinta ya bushe.

            " Mommy? " Reyhana ta fad'a lokaci guda kuma hawaye ya gangaro a idanuwanta.

          "Reyhana nasan hakan baze zo maki da sau'ki ba amma ki sani dan farincikinki nake komeh da kika gani".

      Bata sake wata maganar ba Abba ya shigo d'akin dan already ya jiyo su da Mommy.

        Mommy tana ganin ya shigo ta tashi ta bar d'akin ,hakan yasa Reyhana ta gano sun sami sa'bani da Abba kuma tasan baze wuce akan maganar aurenta ba.

        " Ta fad'a maki koh?" Abba ya tambaya.

       Kuka Reyhana ta fashe dan bata da wani sauran dauriya a tare da ita.Bece sake cewa  komai ba yabi bayan Mommy.

        Ita kuwa Reyhana gefe guda ta ajje Nasreen ta shiga rera kuka,a lokacin kuma taji wayarta na ringing koda ta duba taga Dear❤

       Seda ta katse ya sake kira tukun ta iya  picking, d'an share hawayen tayi tare da sassaita muryarta tai magana.Duk da haka seda yaji yanayin muryar tata ya tamabayeta.

        "My Amarya meya faru?"

AR²💖

Please share..

Jasko💕

      
       
      

  
            
     

ARZI'KI RABO(Completed)Where stories live. Discover now