Page 18

191 18 4
                                    

        Thank you so much for your warm support Ummeeytr,sisi kema ban manta dake ba ina godiya ,masoyan littafinnan na whatapp godiya mara adadi Allah ya barmu tare 😘 Ameen.

         Umma da suka dawo tare da Sadiq jikinta a sanyaye ,tana tunanin yadda ze gudanar da rayuwarsa har tsahon lokacin da ze gama karatunsa,dan d'an nata be ta'ba yin nisa da ita ba kamar wannan karan.

       Around 8pm Umma taji ringing d'in wayarta ,koda ta duba international number ta gani,dama a cikin ranta tayi tunanin Ahmad d'inta neh.

         "Umma". Ya kira sunanta.

         " Ahmad kaine".Umma ta fad'a da saurinta.

         "Eh". Ya amsa.

          " Kun isa lafiya?" Ta tambaya.

          "Lafiya lau Umma". Ya asa.

           "Toh kuna makaranta ne ko kuwa?" Ta tambaya.

           "A'a mun samu Apartment ne tare da  wasu 'yan kano da muka tafi dasu". Ahmad ya fad'a.

          " Toh abinci fah ?" Ta tambayesa.

           "Zanci". Ya amsa.

            " Toh ka samu de kaci karka zauna da yunwa kaji".Cewar Umma cikeda damuwa.

        "Toh inshaAllahu". Ya fad'a.

         " Yawwa ka kula sosai".Ta fad'a.
     
         "InshaAllah". Ya amsa.

     Daga haka sukai sallama,bayan nan ya kira Sadiq ma ya sanar masa ya isa.

        Ahmad ya samu yaci abinci kad'an duk da kuwa yana jin yunwa ,kawai kewa ce da ba'kunta suka sa ya kasa ci dayawa.

       Sauran da suke apartment d'aya dashi suna falo su uku se surutu suke kamar ba wanda yau neh zuwansu na farko ba,Ahmad kuwa rufo 'kofar d'akin da yaye ya kwanta dukda ba shi kad'ai ne a d'akin ba.
 
        Da'kyar ya samu bacci ya kwashe shi dan daya rufe idanuwansa Reyhana yake gani.

Washegari,6:08am ya tashi,hayaniyarsu ce ta tashe shi.
    
         Da sauri ya mi'ke yayo alwala yayi sallah.D'ayan room mate nashi yaga ya baje se narkar bacci yake da alama beyi sallah bama.

      'Karasawa yayi gadon da yake ya tasheshi,daga nan ya komo ya zauna.

       Ba jimawa sauran guda biyun sukai knock a d'akin.

        " Shigo". Ahmad ya fad'a.

         "Assalamu Alaykum". Sukai sallama.

      Ahmad ya amsa musu ,'karasowa sukai  wajensa sukai handshake.

        Nan suka sake introducing kansu.Da Ibrahim da  Idris se room mate na Ahmad, Imran sunansa.

        Kusan shine  sa'an Ahmad sauran kuwa baza sufu 22 zuwa 23 ba.

        Tare dukansu suka fita cin abinci a restaurant bayan sun shirya.

        Shawara sukai a junansu suka siyi kayan abinci ,inyaso sa dinga girkinsu a gida.

ARZI'KI RABO(Completed)Waar verhalen tot leven komen. Ontdek het nu