Page 12

205 20 0
                                    

     Ahmad jin amsar ta yasa ya kasa sake cewa komai ,shiru dukansu sukai credit na tafiya.

       Mommy data ke tsaye a jikin 'kofar d'akin 'karasowa tayi kusa da Reyhanan.Wayar ta kar'ba daga hannun Reyhana ma'kale a kunnenta.

       "Ahmad yanzu abinda kayi ka kyauta kenan? Reyhana ta cancanci kayi mata haka?" Mommy ta fad'a.

       Ahmad jin muryar Mommy kamar daga sama yasa ya gyara tsaiwarsa da yana jingine a garu amma jin muryarta yasa ya mi'ke tsam.

       "Eyyi? Activities naka sunfi lafiyarta,ace tun shekaran jiya rabon da kayi waya da ita rashin damuwa da ita ne komey?" Mommy ta d'ora akai.
       
         "Mommy wlh wayata ce ta samu matsala se d'azu na kar'bo daga gyara jiya na kira a wayar umma bana samun ta". Ahmad ya fad'a.

      " Mommy dan Allah kiyi ha'kuri".Ahmad ya fad'a.
        
       "Kiyi ha'kuri". Ya sake bata ha'kuri.

      Mommy bata sake cewa komai ba wayar ta katse sakamakon credit daya 'kare.

      " Matalauci". Mommy ta fad'a.

         Reyhana taji abinda Mommy tace amma tayi kamar ba sauraro take ba.

     Ahmad kuwa ba tare da ya 'bata lokaci ba ya taho izuwa gidansu Reyhana.

     Seda yayi kusan 5min ya iya shiga gidan dan nauyin had'a ido da Mommy yaji balle Abba.

         Yana shiga tun a harabar gidan ya had'u da Sageer.Bayan sun gaisa ya 'karasa dashi ciki.

     A parlour suka tarar ba kowo dan haka Sageer ya hau sama ya sanarwa da Mommy.

        Babyn na hannu Mommy lokacin Sageer ya isketa.

      "Mommy gafa ya Ahmad yazo". Sageer ya fad'a.

      "Shine yazo?" Cewar Mommy.

      "Eh yana parlour". Ya amsa.

        " Toh ungo ta kai masa ". Mommy ta fad'a tare da mi'ka masa babyn.

         Hannu yasa ya amsa sannan ya fice.

          Itade Reyhana ko " a" batace ba kuma bata tashi ba .

       A parlour Ahmad yana tsammanin ganin Mommy amma yaga Sageer tafe da baby,bawai be damu da yaga babyn ba amma a yanzu Reyhanansa yake son gani.

      A sanyaye ya kar'beta daga hannun Sageer daya mi'ko masa.

       Yana mi'ka masa ya fita daga parlourn dan school ze koma, Ahmad daga shi se baby a hannunsa.Ji yake kamar ba 'yarsa ba saboda mamaki.Daya kalli fuskarta da idanuwanta suke a rufe a ziciyarsa yana me godewa Allah.

       Sunan da za'a saka wa babyn ne ya fad'o masa dan,tuna Reyhana data ce zata fad'a masa sunan da take so a saka wa babynsu ya shiga yi.

      A zuciyarsa kuwa yana fad'in ina ma yana nan ta haihu.

      Addu'oi yayi ma babyn ya 'kura mata ido yana sake ganin kammaninsa a fuskarta.

      Sakkowar Mommy ce tasa yayi saurin d'ago da kansa.So yake ya sakko 'kasa daga kan kujerar amma kuma ga baby a hannunsa,hakannan ya 'kwantar da ita a kan kujerar daga gefe ya sakko 'kasa.

      "Ina kwana ". Ya gaisheta.

      " Lafiya". Ta amsa.

       "Mun samu 'karuwa kuma ,Allah ya raya ". Mommy ta fad'a.

       " Ameen".Ya amsa a hankali.

       Yana so ya tamabayeta jikin Reyhana amma ya kasa, Mommy ta gano hakan kuma dama haka  take so shiyasa bata cewa Reyhana ta sakko ba.

ARZI'KI RABO(Completed)Where stories live. Discover now