Page 10

236 17 0
                                    

       "Azizaty kin manta dani". Ahmad ya fad'a.

      " Ashe zan iya mantawa da kaina ,kana raina dear ".Reyhana ta fad'a cikin sanyayyar murya.

        " Toh ya kike ya babynmu?" Ahmad ya tambaya.

       "Lafiya but we miss you much".

      " Nima Azizaty tun d'azu ku nake tunani".Ahmad ya fad'a.

      "Kaci abinci?" Ta tambayeshi.

       "Na kasa ci Azizaty,ba dad'i".

       " Ayya! Ka daure kaci kaji".Reyhana ta fad'a.

        "Toh zanci amma ba yawa".

       " Yafi de ka'ki ci".

       Sun d'au tsawon lokaci suna waya kafin daga bisani suyi sallama sannan tayi kwanciyarta dama da wuri take baccinta.

        Washegari da asubah kiran Ahmad ne ya tasheta ,bayan sun gaisa ta tashi tayi sallah tayi azkar d'inta.

      Da safe kafin ya fita seda ya  sake kiranta a waya.

       Kamar koyaushe Reyhana ta shiga kitchen ta had'a tea tasha da cake dan yunwa take tashi da ita.

     Koda ta koma d'aki jin baccin ya'ki zuwa ta had'a ruwan wanka a kettle,'yan  minute kad'an ta shiga tayi wankanta ta zira doguwar riga dan kusan duka rigunanta basa shigarta sede tayi ta fama da dogayen rigunan.

      Jin zaman d'akin ya isheta ta fito parlour ta kunnaTV ta soma kallo.Se chan bayan wasu 'yan lokuta suka tashi Mommy ta sakko 'kasa inno kuma tana kitchen ta fara had'a musu abun breakfast.

       "Mommy ina kwana". Reyhana ta gaisheta.

      " Lafiya lao,ke kuma baki koma baccin bane ?" Mommy ta tambayeta.

      "Eh". Ta amsa.

      " Toh ki sha tea d'in?" Ta tamabaya.

      "Eh nasha". Ta amsa.

      " Yawwa ya jikin Walidan ? "Ta tambaya.

     " Walida taji sau'ki d'azu ta farka tasha tea sannan aka bata magani".Mommy ta amsa.

     "Bari na shiga kitchen na duba inno".Mommy ta fad'a.

     " Toh".Reyhana ta amsa ta cigaba da kallonta.

       Se around 9:30am suka hallara a dinning dukansu Ikram a haka ma bacci be isheta Reyhana ce ta tasota.

      "Yarinya kwanan zaki dena baccin safe". Reyhana ta fad'a dan nan bada dad'ewa ba zata fara zuwa university tunda ta samu admission.

     " Abinda nake fad'a mata kenan ai".Cewar Abba.

    "Gara ma yarinya ki soma 'koluwa kyaji yadda nake ji". Sageer ya fad'a.

     Dariya sukai ,ita kuwa harara ta watsa masa.

    " Toh kai ai dole kasha wuya tunda kake namiji ita ai mace koh".Mommy ta fad'a dan ta kare ta.

      "Atoh kuma dole a kaini school". Ikram ta fad'a tana masa gwalo.

     Shikuwa sageer baki ya ta'be ya cigaba da cin abinci,Walida kuwa ana d'aki ana bacci.

         ***

Da asr sega su Anty Asma'u da sauran sisters na Mommy ,Reyhana tana parlour tajiyo muryarsu kuma dama taji inno tana musu sannu da zuwa a waje.
 
     Da sauri Reyhana ta bar parlourn wai kunya take ji kar su ganta.

ARZI'KI RABO(Completed)Where stories live. Discover now