Page 11

191 22 0
                                    

       Dayawa suna cewa Ahmad abun yayi masa yawa. I want to remind you this is just the beginning,kude ku cigaba da gashi🔥

   Mommy da Abba a tare suka furta"Alhamdulillah".

       Bayan an gyaggyara maman baby da babyn kanta su Mommy suka shiga.Su kansu nurses admiring kyan babyn suke, Reyhana kuwa kallonsu kawai take a zuciyarta tana godewa Allah.

     "Mey aka samu?" Mommy ta tambaya.

     "An haifi mace". Suka amsata.

     " Toh mashaAllah ,Reyhana sannu ko".Abba ya fad'a yana kallonta.

     D'an wahalallan murmushi ta saki ta maida kallonta wajen babyn.

     "Sannu koh". Mommy ma ta fad'a".

      Babyn tana hannun Abba Mommy tana daga gefe itama hannunta nakan towel d'in da aka nad'e 'yar.

         " MashaAllah".Mommy ta fad'a.

        Mommy  wayarta ta d'auka ta kira su Ikram take fad'a musu,murna suka shiga yi.

       Bayan ta katse kiran ta kuma kiran Ahmad amma shiru kake ji.Mommy kuwa a ranta tace bazata sake kira ba.

      "Kin sake kiran Ahmad d'in ne?" Abba ya tambaya.

      Kai kawai Mommy ta kad'a fuskarta ta nuna alamar rashin jin dad'i.

      Reyhana tana kallonsu kanta kawai ta kawar ita kanta Ahmad ya bata haushi.

      "Taya za'ai ace ta haihu uban yarinyar ma baya gun? Kuma why not be nemesu ba tun jiya gashi har yanzu" Ta fad'a a ranta.

      Anty Asma'u ma an sanar mata da sauran sisters.

             ***

Shikuwa Ahmad koda gari ya waye da wuri ya shirya ya fita wajen aiki,sunyi da ogansa yau zasu je kasuwa dan haka suka tafi.Amma Reyhana tana ransa dan so yake idan sun dawo ya biya gidan Umma yai waya da ita kafin a gyara wayarsa.

       Wajen 11:00am aka sallamesu daga asibiti,kafin su koma gida dama inno ta d'orawa mey jego ruwa.

       Suna isa Walida ce the first d'in kallon baby har wani rawar jiki take a d'ora mata ita a cinya.

       "Walida baza ki iya ri'keta ba". Abba ya fad'a.

       " A'a zan iya ".

       D'an d'osana mata ita akai kafin Ikram da Sageer su kar'beta suma.

      " Wow! Mommy kalli hancinta da lips d'inta".Ikram ta fad'a.

       "Dani take kama". Cewar Bassam.

      Daga Mommy har Abba seda suka dara,banda Reyhana da tunaninta baya gun ,rashin zuwan Ahmad shi ya tsaya mata a rai.

      " Tabb! Ka cuceta amma ka kalli kanka  ka kalli yarinya  kace kuna kama hhh kade duba(😀 nima nace..).

      Haka suka cigaba da kalleta suna yaba kyanta da farinta (Nide dana kalleta naga copy d'in Ahmad😛).

        Gashinta ma irin nasa ne,kamanninsa sun fito a fuskarta sosai.

         Ruwan wanka Inno ta kai mata toilet,harda hawaye ita wai yayi zafi banda Mommy ta sata a gaba ba da seta surka.

          A cikin atamfofinta ta samu doguwar riga mara nauyi tasa,tea mey kauri Mommy ta had'a mata tasha,se farfesun kaza da inno ta dafo mata taci kad'an.

ARZI'KI RABO(Completed)Where stories live. Discover now