Page 2

356 35 0
                                    

 Written by Dijensy💖

  Reyhana ba ita ta tashi ba se wajen 11:10am,wanka tayi tayi shirinta cikin material blue ya d'auketa sosai.Kitchen ta shiga ta d'ora tukunya tana canki-cankin me zatayi kuma tasan shi Ahmad ba ruwanshi ko ta kira ta tambayeshi ba za'ba zeba.Daga 'karshe de ta yanke shawarar yin tuwon semovita da miyan alayyahu.

     Around 12:00pm ta kirasa a waya,lokacin yana class ya fita tukun yayi picking.

     "Azizaty!" Ya kira sunanta.

    "My dear ya school d'in yau?"

    "Kinganni ina class ma na fito". Ahmad ya fad'a.

     " Ok, toh go back to your student seka dawo". Ta fad'a.

     "Toh my wifey sena dawo". Ya fad'a.

    Daga haka sukai sallama,komawa tayi kan girkinta dama miya ya rage ta gama.

               ***

   2:23pm Ahmad ya dawo gida,Reyhana kuwa tuni ta kammala komai ta sake dusting powder a fuskarta se lipgloss data 'kara a lips d'in.

       Tana jiyo knocking nasa tayi saurin fita,ba 'bata lokaci ta bud'e 'kofar.Bata ankara ba taga yayi hugging nata.

      " My dear mutanen waje zasu hangomu fa". Ta fad'a.
  
     "Ina mutanen suke azizaty banga kowa ba". Ya fad'a dan unguwar ba hayaniya sosai.

     'Kofar ya tura ya rufa tukun yayi breaking hug d'in." Kinyi missing d'ina ma kuwa azizaty? " Ya tambaya.

     "Meyasa kace haka?" Ta tambaya.

     "Ehmana naga kamar baki missing d'ina ba".

     " I do mana".Ta fad'a tana turo baki.

     "OK if you miss me then". Ya fad'a tare da nuni da kumatunsa alamar tayi masa peck.

       Murmushi tayi tukun tayi d'age nan tayi masa peck.

      " That's my Azizaty ". Ya fad'a tare da tallafota jikinsa.

       Kamar koyaushe ta kai masa ruwan wanka toilet,bayan ya shirya kuma ta kawo masa abinci.Yau tare suke cin abincin dan itama bata ciba,suna ci suna hira.

       " Yawwa my d yaushe zami je gaida Umma?" Reyhana ta tambaya.

      "Kede kawai kina so kiji yaushe zaki wajen mommy". Ya fad'a yana mata dariya.

      " Laaa! Ni ba haka nake nufi ba". Ta fad'a.

      "Zaki wayence ba". Cewar Ahmad.

      "Toh shikenan baka amsan tambayata ba". Ta fad'a.

      " Reyhana yau har kwanakin nawa a gidannan ma tukun?"

      "Kwana fa kace? Ana maganar wata fa kenan". Ta amsa da sauri.

      " A'a azizaty baki kaiba de".

      "Toh na lissafa ma?" Ta tambaya.

      "Eh lissafa". Ya amsa tare da tattaro attention d'insa kanta.

      Reyhana kuwa sosai ta fara lissafi tiryan-tiryan hadda yatsu a lissafin nata,yadda take lissafin ya bashi dariya sekace 'yar yarinya." Toh my azizaty na yarda". Ya fad'a.

      "Kaga harna 'kara kwana biyu akai ma". Ta fad'a.

      " Gaskiyarki uwargida". Ya fad'a cikeda zolaya.

ARZI'KI RABO(Completed)Donde viven las historias. Descúbrelo ahora