Page 8

188 17 0
                                    

       Cikeda takaici yake kallonta a ciki-ciki yai sallama itama a hankali ta amsa ta matsa ya wuce.

     Shi ba abinda ya sake bashi haushi kamar yadda itama ta wani shareshi bako sannu da dawowa sema turo baki dayaga tanayi wanda besan dalili ba.

         Kayan jikinsa ya rage seda ya watsa ruwa tukun ya fito  da ba'kar T-shirt da blue jeans.Kitchen ya nufa ya zubo abincinsa da kansa, tana kallo ya shiga sitting room.

      Ta kula da yadda yake ta cin magani haka yasa ta shige d'aki abinta .

      "Kajimin mutum ya tashe ni a bacci da bugun 'kofa kuma yana cimin magani". Reyhana ta fad'a a  a hankali.

     Ita sam bata san ya dad'e yana bugu ba.

        Har ya gama cin abincin be nemi inda take ba illa shingid'a kan kujera da yayi.
   
      " Instead ta bani ha'kuri shine zata shige d'aki aiko naga meyiwa wani magana".Ya fad'a a ransa.

        A haka har akai maghrib ya tafi masallaci be dawo ba har seda yayi isha'i tukun ya komo gida dama ya fita da key d'insa.

       Sanda ya shiga cikin d'aki yaga bata ciki ,waje ya samu ya zauna.

      Reyhana lokacin tana sitting room cin abinci,taji shigowarsa sarai amma ta share dan haryanzu bata huce ba gashi dama ba wuyar yanzu tayi fushi abinka masu ciki.

      Around 9:30pm Reyhana ta fito daga sitting room, koda ta shiga d'akin.
      
        Yana kwance a kan gadon kuma bawai bacci yake ba.Ita kuwa toilet ta fad'a ta shiga ta watsa ruwa sannan ta zira sleeping dress nata ta hawo gadon.

      Duk abinda take yan kallonta,itama tana jin idonsa a kanta amma tayi burus kamar bata gani ba ,juya masa baya tayi tai kwanciyarta bayan tayi addu'ointa.

      Hakan ba 'karamin sake sashi tunzura yayi ba ,shima kwanciyar yayi ya juya baya.Kowa a cikin zuciyarsa da abinda yake tunani.

               ***
Washegari da asubah bayan tayi sallah yunwa ta hanata komawa ,seda ta zubawa cikinta tukun ta komo d'akin.

     "Ina kwana". Ta gaisheshi.

      " Lafiya".Ya amsa ciki-ciki.

       "Wai yaya laifi nayi koh meh?" Reyhana ta tambaya dan yadda ya amsa mata yasa taji hasushi tund ita ba haka ta gaidashi ba.

        "Bakisan mey kikai ba kenan?" Ahmad ya fad'a.

          "Kamarya ? Nifa kayiwa laifin ma,gafa yadda ka tasheni ina bacci jikina yana kyarma na bud'e amma kayi biris kamar bakasan ina gunba". Cewar Reyhana.

       " Lalle kuwa nida kika ajje a waje na shafe kusan rabin awa baki ko damu ba illa damuwa da bacci kawai".

       "Amma de ai kasani kullum da key naka kake fita, kuma ai da idona biyu bazan'ki bud'ewa ba". Reyhana ta fad'a.

     "Au haka ma zaki ce ?"
    
       "Toh Allah ya huci zuciyarka". Reyhana ta fad'a.

       Shi hakan ma sake 'kona masa rai yayi ,bece komai ba sakamakon kiransa da akai a waya.Koda yai picking yaji daga wurin aiki ne ogansu yana nemansa,dan haka ya mi'ke da sauri yayi wanka ya fito.

       Reyhana tana kallo ya sanya kayansa be ce mata ko 'kala ba.

      " Na tafi". Abinda yace mata kenan sanda ya zira takalmi.

      Shiru tayi har ya fice tabi bayansa da kallo.Ba abinda ta tsana irin taga ya fita beyi breakfast ba.

       Reyhana agogon d'akin ta kalla taga 7:17am ,mi'kewa tayi kan gadon ta koma baccinta.

ARZI'KI RABO(Completed)Where stories live. Discover now