Page 24

186 17 4
                                    

        Lokacin da ya dawo gida su Umma na falo yana jiyo su ita da Zainab,d'akinsa ya shiga ya zauna yana ta tunano Nasreen.

      Se yanzu ya sake gane rashin kyautawar da yayi na rashin bata kulawar da ta wajaba a kansa.

  °°°
Se wajen maghrib daya fito zeje masjid Zainab ta ganshi.

     "Laa dama ka dawo gida".

      " Eh ai ban jima da dawowar ba". Ya amsa.

      "Masallaci zaka?" Ta tambaya.

      "Uhm". Ya amsa.

      " Toh seka dawo". Ta fad'a.

          Zainab bayan fitarsa ta shiga kitchen had'a abincin dare.

                   ***
  Reyhana tana d'aki hankalinta ya d'aga Sameer yazo Nigeria d'azu ya kirata ya fad'a mata.Yanzu bata da 'karyar da zata fad'a masa,bama shi kad'ai ba har Abba.Nasreen tuni tayi bacci ita kad'ai se juyi take ta kasa bacci tunani ya isheta.

       Saudat ce abokiyar shawara yanzu kuma dare yayi sede gobe,abunda ya fad'o mata a rai kenan.Dakyar ta samu ta iya yin bacci.

                     ***
      Washegari da safe bayan ya gama shirinsa ya fito falo ,Zainab ya tarar tayi shirin school da alama ma shi take jira.Shi ya mance ma da kaita school se yanzu ya tina.

       "Ina kwana yaya". Ta gaisheshi.

        " Lafiya lau". Ya amsa.

     'Kokari yayi ya kauda idonsa daga kallonta dan kwalliyarta tana masa 'kwarjini,sosai tayi mugun kyau.Doguwar riga blue tasa se rolling datai golden d'in mayafi ta sa'kala jakarta golden fuskarta tasha kwalliya ga maroon lipstick daya haskata.

      "Ka shiryo kenan".Umma ta fad'a sanda ta shigo falon.

        " Eh d'azu na shigo mu gaisa kuma kin koma bacci,ina kwana". Ya gaisheta.

       "Lafiya lau,bazaka karya ba?" Ta tambaya.

        "Eh se anjima". Ya amsa.

         " Toh sekun dawo"Ta fad'a.

          Yana ficewa tabi bayansa,a cikin ranta tana jin dad'i musamman da taga sunyi ango shi yasa blue d'in shadda.

        Cikin 'kan'kanin lokaci ya kaita kafin ta fita daga motar ya 'kara mata kud'in makaranta dukda ana bata daga gidansu.

•••

Yauma daga aiki be koma gida ba seya je school d'insu Nasreen,4pm lokacin yana tsaya a gate d'in yana tunanin yadda ze ganta.

      Da'kyar mey gadi ya barshi ya shiga wani daga cikin malamanne ya kira Nasreen tazo.

      "Kinsan wannan?" Suka tambayeta.

      Seda ta tsaya na d'an lokaci tukun tace "Eh".

      Wata daga cikin malaman tace " Ai gashi ma kamar su d'aya".

     Dama sun fito sallah basu koma ba dan haka ya kamo hannunta suka zauna daga wani bench a compound d'in makarantar.Ita de Nasreen tana jin d'ar-d'ar musamman idan ta tuna abinda Ummienta tace.

        "Nide ummiena ta hanani kula mutanen waje".Ta fad'a.

        " Kinmanta ni Uncle ne? Na kawo maki wannan ".Ya ciro mata Twix guda biyu daga aljihunsa.

        Aiko da sauri ta mi'ka hannu ta kar'be" Amma karka fad'a wa Ummiena kaji".Ta fad'a harda zaro ido.

       "Toh". Ya amsa tare da kad'a kai.

ARZI'KI RABO(Completed)Where stories live. Discover now