Page 9

209 18 0
                                    

    Yau Reyhana tun 10:30am ta gama komai dan yau gida zata da wuri Ahmad dama yau alhamis  yana azimi shiyasa ko girkin rana batayi ba wajen 11:37am ta gama shiryawa.

      Sanda ta shiga gida Abba ze fita nan ya tsaya suka gaisa tukun ya fita.

       Tana shiga ciki inno ta gani tana goge-gige a parlour.
   
       "Ina kwana inno".Reyhana ta gaidata.

       " Reyhana kece a gidan? Lafiya lau ".Ta amsa.

        " Su Mommy suna d'aki ne?" Ta tambaya dan taga bakowa a parlourn.

        "Eh Walida ce bata da lafiya suna d'akinta dan basu jima da dawowa daga aibiti ba". Inno ta fad'a.

       " Tohh! Allah ya sawwa'ke bara na hau saman".Reyhana ta fad'a.

      A kwance ta isketa a gado se fad'a ake da ita wajen shan magani.

       Tana ganin Reyhana ta fara 'ko'karin tashi zaune.

      "Yi zamanki keda bakida lafiya". Reyhana ta fad'a.

         " Mommy ina kwana".Reyhana ta gaisheta bayan ta zauna a wata kujera dake d'akin.

        "Lafiya ". Mommy ta amsa.

         " Ya jikinnata ?"Reyhana ta tambaya.

        "Da sau'ki,tashi tayi da zazza'bi seda aka kaita asibiti". Cewar Mommy.

       Su Ikram da Sageer ma suka gaisa da ita.

  Bassam kuwa yana makaranta." Walida kisha magani kinji koh bakya so ki warke?" Reyhana ta fad'a.

     Kai ta girgiza alamar "A'a".

      " Toh maza tashi kisha".Ta fad'a.
 
      Da 'kyar aka samu tasha maganin sannan ta samu ta sake shan tea daga baya tayi bacci.Se lokacin ta barsu suka sarara dan Walida bade raki ba.

       Sageer ya wuce d'akinsa haka Ikram ma.Reyhana kuma d'akin Mommy.

       "Reyhana meyasa kike cutar rayuwarki?" Mommy ta fad'a .

        "Yanzu har takai ga kin fara sayar da abubuwanki ,wannan shine rayuwar da kika za'bawa kanki?" Cewar Mommy ranta a 'bace.

         "Mommy fa daman ta fara bani matsala wayar". Reyhana ta fad'a.

        " Bawani nan 'karya kike,nasan mijinki kika bawa kud'in".Mommy ta fad'a.

        Reyhana shiru tayi ta sunkuyar da kai dan ta rasa abin fad'a.

          "Ke bazaki ta'ba gane mey nake nufi ba ,ki duba kiga tun ba aje ko ina ba kun fara shiga cikin wannan halin ina ga kun fara yara,Ahmad sam ba tsaran aurenki bane baki dace dashi ba baze iya ciyar dake ba a haka kuma kike tunanin kuyi 'ya'ya dashi".

         Reyhana kwallar da take ma'kale take ta zubo kalaman Mommy suna tsorata ta.

      " Mommy umma ce fa bata da lafiya shine na siyar dan akaita asibiti".Reyhana ta fad'a murya na rawa.

        "Ummansa ce ba lafiya? Yanzu kinzamo kece mijin kenan". Cewar Mommy.

        " Reyhana ina tausaya maki amma ke gani kike kamar na matsawa rayuwarki ki".

       Sallamar Ikram ce tasa suka katse maganar da suke ,da sauri Reyhana ta goge hawayen idanuwanta.

        Mommy tashi tayi ta bassu suna ta hirarsu.Daga bisani suka shiga kitchen Ikram da Reyhana suka soya wainar flour dama gashi Walida tana so.

ARZI'KI RABO(Completed)Where stories live. Discover now