Page 32

201 24 0
                                    

    Yana 'karasawa wajensu ya mi'ka wa Sameer hannu su gaisa,beyi musu ba ya mi'ka masa shima.

       Sede kowa a zuciyarsa da abinda yake tunani.Ita de Reyhana ido ne nata.

         "Sannu koh". Ahmad ya fad'a yana kallon Reyhana
    
          " Yawwa".Ta fad'a ciki-ciki.

       Daga haka ya wuce ya shiga gidan,yana gaisawa da Mommy ya fito dede lokacin Reyhana tana shigowa.

       Kallo d'aya tayi masa ta d'auke idonta ta wuce ta barshi a tsaye ta shige,shima ba tare da yayi magana ba ya fita ,har ya koma gida be dena tunanin Sameer daya gani ba.

        Lokacin daya shiga parlor Umma bata nan se Zainab.

      "Sannu da dawowa ya Ahmad". Ta fad'a.

        " Yawwa".Ya amsa.

         Shiru ne ya ziyarci parlorn kafin daga bisani Zainab ta sake wata maganar.

        "Yaya naga sa'ko na gode". Ta fad'a.

       " Uhm?" Ya tamabaya cikeda neman 'karin bayani.

       "Na agogo da ka bada a bani". Ta fad'a.

        "Uh..ok". Cewar Ahmad yana tunane-tunane.

       " Sadiq?" Ya fad'a a ransa.

       "So ,shine ya bata agogo yace ni na bashi ya bata.." Ya fad'a a ransa.

       "Ka dawo kenan" Umma ta fad'a sanda ta shigo.

        "Eh na dawo". Ya amsa.

         Tashi yayi ya fita ya koma d'akinsa ya d'auki way a ya dannawa Sadiq kira.

       " Na zee".Sadiq ya fad'a yana dariya.

        "Sadiq zan maka wula'kanci". Ahmad ya fad'a.

        " Daga nayi maka abin arzi'ki,dan'kon soyayya na 'kara maku fah".

        "Bana son irin wannan ". Cewar Ahmad kamar yana ganinsa.

        " Kode kishi kake? Gaya mini in baka so nake mata magana sena dena".

        "Ni na saka ka saya mata agogo har kace nina ce ka bata?"

        "Beyi kyau bane agogon?" Sadiq ya tambaya cikeda rainin hankali.

     Ahmad dan tsabar takaici kashe kiran yayi ,ya ajje wayar gefe.Tunani Sameer da Reyhana ne ya sake dawo masa a take ya d'auki wayarsa ya kira ta.

     Seda ya kira sau uku tukun tayi picking.

    "Assalamu Alaykum". Tayi sallama.

     " Waalaikumussalam,nayi sa'a an d'aga min  kira". Ya fad'a bayan ya amsa.

      "Eh ai saboda ban gane number d'in ba shiyasa banyi picking da wuri ba". Ta fad'a.

     " Au dama har yanzu number ta bata chanchanta ayi saving ba?"

       "Eh". Ta amsa a ta'kaice.

         " Toh yanzu ina fatan kingane mey magana?" Ahmad ya tambaya.

           "Ina fatan bazaka sake yimin irin wannan tambayar ba?"

       "Ni na isa". Ahmad ya fad'a.

        "Reyhana wannan dana ganku tare waye?" Ahmad ya tambaya dan sam hankalinsa ya kasa kwanciya.

     "Ina ruwanka dashi?". Reyhana ta fad'a.

ARZI'KI RABO(Completed)Where stories live. Discover now