Page 15

191 16 0
                                    

       "Yaya ba komai ,kawai de kaina ke ciwo". Tayi 'karya.

       " Toh! Allah ya sawwa'ke kin sha paracetamol? " Ya tamabaya.

       "A'a amma zansha". Ta fad'a.

       " Toh ki samu ki sha,ya Nasreen?"

        "Tayi bacci". Ta amsa.

         " Toh ki shafan min kanta".Ahmad ya fad'a.

          "Kema ki samu ki baccin  kan ze dena,nima yanzu zan fita".

            "Ok,toh seka dawo". Ta fad'a.

        Daga haka sukai sallama ta ajje wayar wani sabon hawaye ya sake gangarowa a fuskarta.

       Mommy kuwa kafin Abba ya 'karasa d'akinta ta rufo 'kofarta,tana ji yana kiran sunanta amma tayi burus.

     Ba 'karamin 'baci ransa yayi ba haka ya koma wajen Reyhana ya tarar da ita tana kuka mey cin rai,rarrahinta yayi yana bata ha'kuri.

              ***

     Sageer ya lura da irin change da aka samu kwana biyu a gidan ,Mommy,Abba,Reyhana ba kamar yadda ya saba ganinsu ba ,kawai de be tanbayi Reyhana bane,abinci ma Mommy ta dena ci tare dasu  dinning haka Reyhana ma ko da daddare idan ya dawo d'akinsa yake shigewa dan yason ko meze ce wa Mommy ba sauraransa zatai ba.  
      
     Reyhana sun cikake 40 harda kwana biyu akai ,Ahmad har ya soma gajiya dan haka yau yazo gidansu Reyhana.

       Sanda ya shiga ya tarar da Sageer dake parlour nan suka gaisa ya hau sama yake fad'a ma Reyhana.
     
         Jiki a sanyaye ta tashi ko Nasreen bata d'auka ba dan bacci take.

         Reyhana tana taka step dan ta sau'ka bata 'karasa zuwa parlour ba ta hangi Mommy a palourn.

     Ba shiri ta tsaya cak,da alama Mommy bata dad'e da zuwa parlourn ba,lokaci guda bugun zuciyarta ya 'karu.

      "Shikenan Mommy zata fad'a masa komai". Ta fad'a a ranta tana ja da baya,da sauri ta koma d'aki ta fad'a gado ta shiga aikin kuka.

       A parlour kuwa Mommy bayan sun gama gaisawa da Ahmad ta soma gyaran murya.

       " Uh..Ahmad nasan dole wannan maganar da zan fad'a maka zaka ji nauyinta,amma banyi haka dan na ba'kanta muku ba nayi haka ne dan nema muku sau'kin rayuwa".Mommy ta d'iga aya amma bawai ta gama ba.

      Jin irin kalaman Mommy yasa Ahmad ya tsinci kansa a irin wani yanayi na daban.

      "Ri'kon mace ba abune mey sau'ki ba,kuma musamman ga Reyhana da bata saba da rayuwa irin ta gidanka ba,yanzu kuma idan ka duba zaka ga nauyi ya sake 'karuwa fiye da da wanda ba abune mey sau'ki gareka ba,sana'arka ba mey 'karfi bace da zaka iya ri'ke su dan haka ina neman alafarma daka sawwa'ke wa 'yata Reyhana".

       Ahmad maganar Mommy yadda ta doki kunnensa ze iya cewa be ta'ba shiga tashin hankali kamar na ranar ba,dan jiyake kamar mafarki.Reyhana matar tasa?Ummu Nasreen Azizatynsa?Tir'kashi!

      " Mommy dan girman Allah ki taimaka mini ki dena fad'ar wannan maganar ".Ahmad ya fad'a kamar mey shirin yin kuka.

       " Gaskiya ce dole na fad'a Ahmad,kuma babu uwa da zata so 'yarta ta shiga cikin wani yanayin wahala,inde har soyayyar da kake mata ta gaskiya ce toh baza ka bari ta sha wahala a rayuwarta ba".Mommy ta fad'a.

       "Mommy kiyi ha'kuri amma rabuwa de Reyhana ba abu ne mey sau'ki ba". Ya fad'a already 'kwalla ta cika idanuwansa.

       " Ai nasan da hakan shiyasa nace maka alfarma,kuma nima ba abune mey sau'ki ba na bari 'yata ta shiga wahala".Mommy ta fad'a a lokacin ta fara 'kosawa.
  
      "Mommy ki duba ki tausaya wa rayuwata da halin da zamu shiga nida Reyhana na sani itama bazata so hakan ba". Ya fad'a muryarsa na rawa.

ARZI'KI RABO(Completed)Donde viven las historias. Descúbrelo ahora