Page 1

1.1K 50 1
                                    

🌸🌸🌸🌸🌸🌸
*MAKAUNIYA CE*
🌸🌸🌸🌸🌸🌸

*Written by*
Jiddah S Mapi

*بسم الله الرحمن الرحيم*

*🌈🇰AINUWA 🇼RITER'S✍🏼*
*🇦SSOCIATION🤝🏻*

*Assalamu Alaikum wannan littafi nayishi ne akan yanda mutane suke nuna kyamarsu ga nakasassu, ayau abinda yazama ruwan dare a duniya shine nuna kyama da ake ga nakasassu, musani fa su wanda suke da nakasan bada son ransu bane ba! Allah ne yaɗaura musu, muma bamufi karfin Allah ya jarrabemu da nakasa ba,wasu idan kaji sanadin da suka samu nakasa saika yi kukan Tausayi, jama'a muji tsoron Allah mudaina nuna kyama ga nakasassu.*
*Ina fatan Allah yasa nagama wannan littafin lafiya*

*WATTPAD*
_Jiddah S Mapi_

*Page* 1

"Karamin gidane me ɗauke da ɗakuna biyu Ɗaki ɗaya babba ne sannan ɗan karami agefenshi,
Cikin gidan an zuba duwatsu kanana da Alama sabida yanayin da ake ciki na damuna akasa,
Katangar gidan tayi ɗan kasa kamar zata faɗo sabida yanda tagaji,
Langa langa ne kewaye da gidan wanda be gama rufe cikin gidan ba.
Mutumin dake waje ze iya hango mutanen gidan".

Da Alama wannan gidan na marasa karfi ne waɗanda suke neman ataimaka musu.

"wata matace nagani zaune abakin kofar babban ɗakin tana daka cikin turmi da Alama barkono take dakawa! Domin tana ta atishawa, matar bazata wuce shekaru 32 Zuwa 33 ba, daganin kayan jikinta zakasan tana cikin matsin rayuwa, riga ne dogo na Atamfa pink wanda tsabar koɗewa harya zama fari, farace sol kyakkyawa da ita duk da yanayin datake ciki hakan be hana kyaunta fitowa ba! gefenta kuma wata kyakkyawar yarinya ce me kama da ita saidai kawai yarinyan tafita haske, yarinyan bazata wuce shekara 15 ba, daganin fuskarta zakasan yarinya ce karama sai girman jiki da tsayi, ita yarinyan tana yanka albasa idon ta duk hawaye, Matarce tnaji tace "Minal meyasa bakya yin abu da karfinki ne iye tin ɗazu fa kike kan yanka Albasa Ama har yanzu ace baki gama ba so kike sai alalen tayi sanyi kafin kikai musu?"

"Yarinyan danaji ankira da Minal naga taɗago kanta tana goge idonta tace Umma wallahi albasar ce da zafi"
Umma tace ay Minal yakamata ayanzu ace kin saba da wahala, Umma ai ba'a sabo da wuya cewar Minal, hakane Amma ai akwai wahalan Daya zama dole Asaba dashi.. Bama wannan maganar ba meyasa kwana biyu naga kin daina karatu? Minal ce tace Agaskiya Umma nahakura da karatun, umma tace haba Minal meyasa zakice haka bayan kinsan mahaifinki tun kafin yarasu yaso kiyi karatu sosai meyasa zakiyi haka?
Minal tace Umma naga karatunnan cikin takura nakeyinta, kiduba mana kigani yanda muke shan wahala kafin musamu kuɗin time, aganina kuɗin da zamu kashe wajen karatu ba gara mukashe shi tahanyar cin abincinmu dakuma kayakin sawa tunda bamu dashi"

Umma ce tace "Minal bazan yadda karatunki yaɓaci ba insha Allah sai kinyi karatu, tinda Allah yasa kinada Ilimi,
Kici gaba dasayar da Alalenki tunda Allah yasa kina ɗan samu nikuma zanje na nemi aikin wanke wanke ko a inane"
Minal tace "to Umma"
Umma ce tace yanzu tashi kije kiyi wankanki kinji?
Minal tace to Umma.

"Wanka tayi tafito tashafa mai da turarenta na cikin kwalba wanda bazai wuce naira talatin ba, tashafa wani powder fari da aka kulla a leda taɗansa kwalli a idonta, tayi kyau sosai duk da bawani kwalliyan kirki tayi ba, wata koɗaɗɗiyar shadda taɗauko tasa wanda duk ta tsufa ta yayyage amma An ɗinka, tsugunawa nayi zata ɗauki Hijabi cikin riyon kayanta taji riganta ya yage tabayan, taɓawa tayi taga rigan ya yage har kusan cinyarta, tinawa tayi da zaren datake ɗinka kayanta dashi tabari agidansu Madina, kuka tafashe dashi na takaici, wannan wani irin rayuwa ne? ace mutum kullum yana cikin ɗinka kaya? Ya Allah kafitar damu daga cikin wannan talaucin"

Umma ce taji Minal shiru, taleka ɗakin tana tambaya wai ina kike ne Minal
Tin ɗazu kina kwalliya kamar wata Amarya?
Ganin Minal tayi tana kokarin goge hawayen fuskarta tace "Na'am Umma gani"
Umma ce ta tsaya shiru tana kallonta yanda take kokarin ɓoye damuwarta,
Tace "Minal meya faru kike kuka?"
Minal tajuya bayanta tana nunawa Umma inda rigan Ya yage tace "kigani Umma kullum ina kan ɗinka kayana da hannu?"
Umma tace "shine kika zauna kina kuka Minal? To indai wannan ne karki damu zan ɗinka miki akwai zare a ɗakina kinji ko 'yata?"
Minal tace nagode Umma na Allah yabarmu tare har karshen rayuwarmu,
Umma tace "Ameen"

MAKAUNIYA CE Where stories live. Discover now