Page 4

473 24 0
                                    

🌸🌸🌸🌸🌸🌸
*MAKAUNIYA CE*
🌸🌸🌸🌸🌸🌸

(An heart touching story)

*Written by*
Jiddah S Mapi

*بسم الله الرحمن الرحيم*

*🌈🇰AINUWA 🇼RITER'S✍🏼*
*🇦SSOCIATION🤝🏻*

_wannan littafin sadaukarwa ne ga yayata Maryam S Mapi_

  *WATTPAD*
_Jiddah S Mapi_

    *Page* 4

"Latif ne yafita dagudu kiran likita,
Atare suka shigo cikin ɗakin da Bilal yake kwance  babu alaman motsi atare dashi"

Kiran sauran Ma'aikatan sukayi,
Aka taru aka ɗauke Bilal awajen.

"Anje an birnesu Bilal be sake ganin fuskarsu ba,  yana kwance luff baya hayyacinshi"

"Tin daga wannan rana Bilal yadaina dariya,  yadaina kula mutane idan zaku shekara awaje tare bakayi mishi magana ba,  tofa shi ko kallo baka isheshi ba!

Jinya yake a asibitin bayason cin abinci ya rame yayi haske sosai,  idan anayi mishi magana sai Eh Aa yake iya faɗa.

Baban Latif da Latif ne suke jinyarshi,
Yau kwanansu Uku kenan a asibiti,  doctor ne yashigo yace musu ba wani matsala zasu iya tafiya,
Godiya Baban Latif yayi suka fara tattare kayansu,
Alhaji Umar ne da mamanshi Hajiya Salamatu suka shigo ɗakin,
Cewa sukayi saide Bilal yakoma gidan Alhaji Umar dazama,  da farko Bilyaki yadda saida Baban Latif yasa baki kafin ya yadda.

Bilal yakoma gidan Alhaji Umar dazama,
Amma yana cikin takura,  Afrah ta takurawa rayuwarshi,  gashi Alhaji Umar yanason sashi yin Auren Dole.

Hajiya Salamatu kuwa (mahaifiyar Alhaji Umar)   banda harara da tsaki ba abinda yake shiga tsakaninsu dashi.

"Alhaji Umar yanada yara Uku,  Hafiz, Sabir, sai Autarsu Afrah takwarar hajiya Salamatu,
Hafiz yatsani Bilal,  hasalima bayason ko ganin Bilal ne yayi, 
Tinda Bilal yagane haka saiya fita a harkarshi, 
Yaran haji Umar an sangartasu,  sam sam basusan darajar mutum ba!
Sabir ne kaɗai yafito me hankali,  shine wanda mamanshi tarasu Daddyn Bilal sukaje gaisheshi,
Bilal jiyaje azuciyarshi yayi Babban rashi,  tinda yarasa iyayenshi da kanwarshi"

_cigaban labari_

"Tissue yaciro a aljuhun rigarshi ya goge hawayenshi,
Jiyayi an dafa kafaɗarshi, be ɗago ba sabida yasan Daddyne ko Latif zasu iya zuwa inda yake kai tsaye"

Kayi hakuri Bilal nasan yanda kakejin zafi azuciyarka,  hakika rashin iyaye bakaramin rashi bane,   amma ahalin yanzu ba kuka yakamata kayi ba Addu'a yakamata kayi musu,  kaji?
Cewar Latif

Bilal ne yace "bazan iya ba, wallahi Latif bazan iya ba, iyayena suna matukar sona!  Ina dana sanin rashin binsu gidan rasuwannan danayi.  kuma wallahi ko mata sun kare aduniya bazan taɓa Auren Afrah ba,
Na rantse akan na Auri Afrah gara na nemi 'yar kauye wanda batasan komaiba in Aura,  yarinyan Da idanunta abuɗe yake,  tasan komai na jikin namiji,  bata tsoron jikin maza,  ace in Aureta Kai inaa"

Latif ne yafara lallaɓanshi harya samu Bilal yadaina surutun.
Yace "yanzu dai katashi kashirya akwai meeting dazamuyi yau ana jiranmu a office kuma idan anyi wannan zaman Zai taimaka mana wajen bunƙasa wannan Companyn"

Bilal ne yace "meyasa baka sanar dani dawuri ba?"

Nima bada wuri suka sanar dani ba,  cewar Latif.

Dasauri Bilal yatashi yashiga cikin gida domin shiryawa,
Toilet yanufa sabida yayi wanka.

_Minal_
Ita kuma yau ganin wani faɗa ta tsaya yi a anguwansu har tayi lattin siyan wake,
Sai bayan an gama faɗan kafin ta tafi gida,   sauri take taga ta iso gida.

MAKAUNIYA CE Where stories live. Discover now