page 33

391 21 1
                                    

*بسم الله الرحمن الرحيم*

🌸🌸🌸🌸🌸🌸
*MAKAUNIYA CE*
🌸🌸🌸🌸🌸🌸

By
Jiddah S Mapi

Page 33...

"Minal murmushi tayi Wanda ya bayyana dimple nata tace "nagode Hajiya Allah yabiyaki"
Matar tace "No kidaina godemin kuma banason ki kara cemin Hajiya, Ki kirani da Mommy, sabida inada yarinya wacce kuke yanayi da ita sosai, saidai ita tanada yawan surutu ba kamar keba shiru shiru".
Murmushi Minal tayi tace "to Mommy"
Matar ce ta kwantar da Minal a cinyarta tana shafa mata kanta a hankali har tayi bacci,
Lokaci d'aya taji Minal tashiga ranta sosai,
Suna Cikin haka saiga mutumin ya shigo, "ya jikin nata?"
Matar tace "da sauki Ammafa Alhaji ina ganin yarinyar nan tana Cikin matsala, a hankali ta fad'a mishi duk abinda Minal tafad'a mata, ta d'aura dacewa, Alhaji ya kamata mu taimakawa yarinyar sabida tana Neman taimako".

Alhaji ne yace "to ai Hajiya basai kin fad'amin ba, idan ka taimakawa mutum ai kanka kayiwa, Yanzu dai muyi Addu'an Allah yabata lafiya, Kinga idan tanada lafiya komai zaizo da sauki".
Da sauri matar tace " Ameen"

Bilal kwanciya yayi akan tyles zuciyarshi a cakud'e ji yake kamar ya tashi yayita ihu kozai samu saukin abinda yake damunshi,
Waya ya d'auko yakira 'yan sanda yabada cigiyarta agidan TV da gidan redio, acikin Daren ya tashi yayita Addu'a Allah ya bayyana mishi ita cikin gaggawa.

_washe gari_

Bilal ne yatashi da sassafe yatafi police station wata kila yasamu information akanta, yana zuwa akace babu wani labari, Idonshi ne ya cika da hawaye yarasa ina zaije ya ganta, zama yayi akan wani dutse dake cikin station d'in, yayi kusan Rabin Awa yana zaune baisan abunyi ba, yaga polisawa sun shigo da wasu samarai su Uku kallonsu kawai yakeyi, a hannun wani police ya hango wata jaka ta mata, idan ba gizo idonshi yake mishi ba, yana ganin kamar jakar Minal ce, da gudu ya nufi wajen 'yan sandan yace "yallab'ai waye me jakar nan?"
Police d'inne ya nuna samaran yace "wannan ne sukayi fashi, mun kamasu suna raba kud'in awani lungu na 'yan shaye shaye".

Da sauri Bilal yariko d'ayan yace " Dan Allah ina me jakar nan, wallahi idan kuka fad'amin zan Baku kud'in daya ninka wannan kuma baza'a kulleku ba".

'Dayanne yace "matar da muka karb'a a hannunta ta gudu kuma mota ya bugeta".
Kukan kura Bilal yayi ya shake wuyanshi yace "a ina?"
'Yan sandane suka fara kokarin kwace saurayin da idanunshi suka firfito tsabar Azaba.

Sauran da suka ga yanda d'an uwansu yasha matsa sai sukace zasu nuna inda suka ganta, motar 'yan sanda suka shiga dukansu harda Bilal dayake ta huci kamar zaki, daidai karkashin bishiyar da Minal ta kwanta suka nuna mishi, Bilal ne ya dirka akan motar yanufi wajen, saidai baiga kowaba, cikin sanyin jiki sukaje inda tayi accident d'in ma babu wata Alamarta, Zuwa wannan lokacin Bilal yakasa controlling na hawayenshi kuka yake kamar karamin yaro, daidai wajen da Minal ta fad'i ne yaga wata zube, d'agawa yayi yana kallo, yasan wannan tabbas zoben Minal ne, sa zuben yayi a hannunshi yana kuka.
Police ne suke bashi hakuri, har suka koma office, an kulle samaran shikuma Bilal sunyi mishi Alkawarin zasuci gaba da bincika mishi ita.
Da haka ya koma Hotel d'in cikin sanyin jiki.

Minal tad'an samu sauki sabida kulawar da matarnan da mijinta suke bata, kamar kullum yauma Minal ce ta kwantar da kanta a cinyar Mommy, cikin muryanta na shagwab'a tace "Mommy yaushe zamu tafi a Asibitin nan? Nifa nagaji dashan magani da karb'an Allura"
Dariya mommy tayi tace "haba mana sai kace keba jaruma ba, babyna fa bata tsoron Allura"
Minal ce tayi murmushi tace "Mommy inason inga babyn naki nima tashiga raina tin ban ganta ba"

Mijin matar ne yashigo d'akin yace "to Daughter ai gobema za'a sallamemu itama ta dameni tanason ganinki, nace mata saidai gobe, kinga sai jibi mu tattara mu koma kasarmu Nigeria ko?"
Cikin jin dad'i Minal tace "to Daddy".

Washe gari Doctor ya basu takaddan sallama, Minal sai murna take zataje taga Babyn Mommy, tariga kowa shiga motar cikin zumud'i tace " Daddy ayi sauri mana mutafi"
Daddy ne yayi dariya yace "to daughter"
A wani babban gida me kyau sukayi horn me gadi ya bud'e musu, Minal ce ta bud'e motar tafita, wata kyakkyawar yarinyace 'yar shekara 17 tazo da gudu ta rungume Minal, Minal tana ganinta tagane cewa itace Baby, cikin jin dad'i itama ta rungumeta,
Mommy ce tafito tana dariya tace "to baby saiki kaita d'akinki acan zaku zauna, yau dai gaki ga Minal"
Baby ce tayi dariya tace "wallahi kuma mom gata kyakkyawa, ai nasamu sister".
Hanun Minal tariko tace " sister muje kiga d'akinmu.

✔ote & comments

_Jiddah S Mapi_

MAKAUNIYA CE Where stories live. Discover now