page 13

377 23 1
                                    

🌸🌸🌸🌸🌸🌸
*MAKAUNIYA CE*
🌸🌸🌸🌸🌸🌸

   By
Jiddah S Mapi

Page 13...

"Tashi yayi yashiga toilet domin yayi wanka, saida yawanke cikin bathtub d'in sosai kafin ya iya wanka aciki, towel ya d'aura babba tareda sa karami akanshi yana gogewa,
fitowa yayi yaje gaban mirror yashafa manshi me kamshi tareda taje gashin kanshi Wanda yake bak'i wuluk, agogonshi yad'auka yasa a hannunshi na dama,  kafin yajuya zuwa wajen wardrobe, wani dark blue na polo yad'auko da farin wando dogo, jikin aljihun wandon dark blue ne, sawa yayi a hankali, nan asalin kyaunshi na cikakken Fulani ya bayyana,
jikin rigan an rubuta Mad Over You da manyan harufa.

zuwa wajen mirror yayi yana kallon kanshi a madubi, a zuciyanshi yace " Alhamdulillah ko ba'a fad'amin ba nasan inada kyau, to meyasa zan cuci kaina in Auri Makauniya?
Dolene in nemo wacce takeda lafiyan idanu, wacce zataga cikin k'wayan idanuna tafurtamin kalaman soyayya, wacce zansan tana cikin farin ciki ko bak'in ciki, Amma wannan Makauniyar ai bazata iya wad'annan abun ba, Anyway zansan abunyi" yana fad'in haka yad'auko eye glass nashi bak'i babba yamak'a afuskarshi, sandarshi yad'auko tareda Fita a d'akin"

Har ya iso bakin kofa yatuna cewa yafad'awa Minal shiba makaho bane "to idan tafad'awa Daddy fa? Kai anya banyi kuskure ba? Wannan yarinyan da karamin bakintan nasan magana baya mata wuya, kai dolene naja mata kunne yafad'a tareda komawa cikin d'akin"
Minal kuma bacci yayi mata dad'i cikin baccin take mafarkin an kaita India an gyara mata idonta yayi sauk'i, murmushi tafara najin dad'i.
"Wato ta kwanta akan gadona tana bacci harda murmushi ko? Zakici Ubanki yarinya, sandar hannunshi yad'auko yakwala mata a bayanta, afirgice Minal tafarka tana salati, ke? Harkin samu damar yin murmushi akan gadona? Wato baccin dad'i yake miki ko? To bari kiji daga yau idan kika kara kwanciya akan gadona saina kwakule idonki d'aya"
Da sauri Minal ta dirko akan gadon, Ash tafad'a cikin Azaba Dan ta bugu da jikin gadon ba wasa.
"Kad'an kika gani, nan gaba wuta zan aje akasa kifad'o akai mayya, kuma idan kika sake Daddy yasan cewa niba makaho bane saina kwakule idonki da daddare kina jina?"
Cikin rawan jiki Minal tace "eh"

"Kitashi ki gyara d'akinnan sannan kicanja bedsheet d'in akwai wani a cikin wardrobe ki shinfid'a,
Minal tace "to"
Saura nadawo bakiyi ba saikin gane kuranki Miskiniya kawai.

"Yana fita Minal takwanta akasa tana kuka, nashiga Uku ni Minal wannan wani irin bak'ar kaddara ne? Dana sani baya maganin komai, ya Ubangiji ina rokanka daka fitar dani a wannan rayuwar, ya Allah ka d'auki raina, awannan lokacin..kukane yakubce mata tasa hannunta ta toshe bakinta dashi, hawayene yakebin hannunta har zuwa wuyanta. kitashi kiyi aikin daya saki Minal karki jawa kanki matsifa cikin zuciyarta take magana, tashi tayi tafara laluben gadon, cikin ikon Allah tasamu tacire bedsheet d'in, d'aukan bedsheet tayi tafara share cikin d'akin dashi, dakyar tagama sharan, tafara Neman inda wardrobe yake, ahankali takeyin komai cikin nutsuwa Har Allah yasa taga bedsheet d'in d'aukowa tayi ta  shimfid'a dakyar,
Haka tagama gyaran d'akin cikin zuciyarta tace Alhamdulillah nahuta dawannan matsifaffen, koba komai zai barni da idanuna koda bana ganin komai"
Kwanciya tayi akasa tana d'an hutawa, muryan Hajiya babba taji afalo tana cewa "ina Makauniyar takene?  Yarinya bazaki fito ki zauna a cikin 'yan uwanki ba? Wannan wani irin bakin haline? Zaki fito ko saina zo?"
Dasauri Minal tamike tana Cewa "gani Hajiya babba kiyi hakuri gyara nake"
Gyaran Ubankine? Akwai gyaran dayafi sada zumunci ne?
Fita Minal tayi tana lalub'en kofan falo, ahaka harta iso cikin falon tazauna akasa tana baiwa Hajiya babba hakuri,
Ke dallah kimin shiru, tashi zakiyi kishare cikin falon nan sannan ki goge ko ina, kina jina?
Minal ce tace "to" Hajiya zanyi....kada kiyima kiga ikon Allah mayya kawai Mara gata kwad'ayayya, tashi kifara maza"

"Mikewa Minal tayi tana Neman tsintsiya bata ganiba, Hajiya a taimakamin da tsintsiya, Wani irin tsintsiya? Kiyi da d'an kwalinki, sa'arki ce ni dazakice in nema miki tsintsiya? Mara tarbiyyar banza,

Minal cire d'an kwalinta tayi tafara goge cikin d'akin, gashin kanta ne ya bazu yazo mata har fuska, idan ta d'aure gashin saiya kara kuncewa,ga falon yayi mata girma harta gaji tabarshi haka, laluben inda take jin karan TV tafara don ta goge, dakyar tasamu ta goge TV da receiver,  Bilal ne yayi sallama a falon tsayawa yayi yana kallon yanda take kokarin gyara gashinta daya zubo mata afuska, azuciyarshi yace " me kuma takeyi afalo? Wannan yarin yan mahaukaciya ce, nida nace tagyara d'akina kuma tazo tana gyaran Babban falo?"
Karasawa inda take yayi, yana zuwa yarike gashinta yana ja, "wato ke bakyajin magana ko? Ince ki gyara d'akina kizo kina gyaran falo? Kuma ba d'an kwali akanki? Ko bakisan maza suna shiga falon bane?.....kayi hakuri yaya Bilal Hajiya babba ce tasani gyaran Falon,
Shine me? Bata kai tasaki gyaran bane?
To barima kiji kina gama gyaran nan kije kibawa flower ruwa kina jina?
Tace eh, cikin azaba Dan ita kad'ai tasan irin rik'on da yayiwa gashinta, saketa yayi tayi tangal-tangal tafad'i akasa,
Tashi tayi dakyar tafara Neman hanyar Fita,  tana fita taci karo da Hafeez Wanda yake tsaye abakin kofa yanajin duk abinda sukayi da Bilal, hannunta yarike tareda janta, tsorata Minal tayi tafara tambaya wayene? Ina zaka kaini?
Shiiiii kidaina magana wajen flower zan kaiki, da Minal taji haka sai tayi shiru"

"Bayan lambu yakaita yace " zauna" zama tayi shima yazauna agefenta har jikinsu yana gugan juna, d'an matsawa gefe tayi atsorace tace "lafiya kuwa"
Haba baby meyasa kika cika tsoro ne?.

dafarko dai sunana Hafeez, matsayin kanin Bilal nake agidannan, naji duk yanda kukayi dashi, nasan Bilal baya sonki kuma bazai tab'a sonki ba musamman yanda kike miskiniya, Bilal da mata manya yake harka, masu kud'i da aji ba irinki kamar tsinken tsire ba, bugu da kari gaki Makauniya"
Nasani baya sona nima kuma na tsaneshi cewar Minal.
idan harkin yadda da abinda zan fad'a miki kuma kika Amince, na rantse da Allah a cikin kwana Uku zan kaiki India agyara idonki tsaf kifara ganin duniya, idan kuma baki yadda ba to wallahi yanzu kika fara ganin wulak'anci a gidannan kai ba gidannan bama ako ina,
Da sauri Minal tace menene kakeso kafad'amin Wallahi zanyi Inde zakasa akaini India infara gani"

Numfashi Hafeez yaja tareda cewa "kiyimin Alkawarin bazaki fad'awa kowaba" dasauri tace "nayi maka Alkawari"

"Okay to idan kin yadda zan rika biya miki bukatanki wanda nasan Bilal bai tab'a yimiki ba, nima kibiyamin nawa bukatan, Minal tace " menene bukatan naka?"
Bawani Abu bane domin nasan mafi yawan 'yan mata yanzu Bazawaraye ne, kema inasa ran haka kike ko?
Dasauri Minal tamike tareda cewa "kasan me kake fad'a kuwa Hafeez? Baka da hankali ne? Zinafa kake niyan muyi, hawayene yafara bin kumatunta, ina matsayin untynka kake min irin wannan maganar? Minal kin shiga uku, ina rayuwarnan zata kaimu, mutane ba tsoran Allah kowa yazo wajenka daniyan taimako saiya nemi yayi lalata fakai, Hafeez idan haka ka d'aukeni Allah ya isa tsakanina dakai, bazan yafe maka ba mugu azzalimi, don 'yan mata bazawaraye ne shine nima kakeson ka lalatamin rayuwa? Gara na zauna babu idanu da inyi zina".......ke ya isa dalla karki rainamin wayo, an fad'a miki bansan sirrinki bane?

Inace ke kike ciyar da gidanku da sunan talle kije kina rabawa gayu jikinki a titi, shine yanzu Dan kina gidanmu kike nema kiyi pretending, to bari naja kunnenki, idan kika fad'awa mutane abunda yafaru tsakaninmu saina saceki insa acire idon naki gaba d'aya, yana fad'in haka yabar wajen,
Minal zama tayi akasa tana kuka. Wannan wani irin k'azamin gida kika shigo ne Minal? Ya Allah katsareni ka kareni daga sharrin mutanen gidannan"

Bilal saurin juyawa yayi don bayason Hafeez yaganshi azuciyarshi yace "wato soyayya sukeyi shine yajuya mata baya, shiyasa take kuka, nasan Hafeez nasan halinshi akan mata babu macen da zaiyi soyayya da ita wani Abu be shiga tsakaninsu ba, wannan ma Ashe mazinaciya ce, Karuwar gida wacce tafi na waje hatsari, dolene insan abunyi"

✔ote & comment

Jidah S Mapi

MAKAUNIYA CE Where stories live. Discover now