page 29

382 24 2
                                    

*بسم الله الرحمن الرحيم*

🌸🌸🌸🌸🌸🌸
*MAKAUNIYA CE*
🌸🌸🌸🌸🌸🌸

By
Jiddah S Mapi

Page 29...

"Suna fita aka kaita wani babban d'aki me d'auke da na'urori da dama, uniform nurse d'in tabata karb'a tayi tasa, daganan suka kara fitowa zuwa wani d'aki d'an karamin da wata karamar gado, nurse d'ince tacewa Minal " sleep"

Minal tace "zan baki wasiyya idan kun kasheni kufad'awa Umma cewar yaya Bilal ne yakashe ni, sannan kifad'awa yaya Bilal yabawa Umma dubu ishirin acikin kud'in dayayi dani, Allah yasa in cika da imani"

Nurse tsaya tayi tana kallon Minal yanda take surutu babu Tsayawa gashi bata jin yaren datakeyi, batayi mata magana ba ta kwantar da 'ita tareda yi mata Alluran da zatayi kwana d'aya bata tashiba harsai angama Aiki.

Bacci me Nauyi ne ya d'auke Minal, wasu manyan doctors ne suka shigo suka fara mata aiki, bayan Bilal yayi sign yabiya kud'in.

_Nigeria_

"Umma da Madina sun nemi Minal sama da kasa basu ganta ba, iya tashin hankali Umma tashiga, kuka take ba kama hannun yaro, " ina kika shigane Minal? Kinsan banida kowa sai ke ya zakimin haka?"
Madina ce tace "Umma ko zamuje gidansu Bilal ne mu tambaya?"

Da Sauri Umma tace "Dan Allah muje"

Tafiya sukayi gidan Alhaji Umar,
Suna zuwa lokacin Daddy yana waya da 'yan sanda akan aduba mishi duk inda Bilal yake, su Ummane suka tsaya agefe suna jiran yagama wayar, yana kashe wayar yace "Ku kuma me kuke buk'ata?"

Umma ce tace "Alhaji nice maman Minal matar Bilal, tin shekaran jiya muke nemanta Amma bamu ganta ba shine mukace bari muzo mu tambaya ko Bilal yasan inda take"

Daddy yace "amma bakuda hankali, an fad'a muku nan gidan b'arayi ne masu satar mutane? To bari nafad'a muku nima banga Bilal ba tin shekaran jiya, na kira layinshi akashe, sabida haka kubar gidannan before I  loo
Loose my temper"

Da kuka suka bar gidan Umma tana cewa "Dana sani da ban yadda da wannan Auren ba" Madina tanata bata hakuri.

_India_

"Anyi Aiki lafiya ansa mata bandage a idon sabida sai gobe around 2:30Am cif zata tashi"
Bilal ne ya kwana a gefenta yana me tausaya mata.

_washe gari_

2:30Am cif hannun Minal yafara Motsi, Bilal ne zaune agefenta yanata Addu'ar Allah yasa anyi a sa'a, ganin hannunta yana motsi yasashi kara kaimi wajen yin Addu'ar, wani doctor ne yazo daidai wajen yana son ya gyara mata kwanciyar sabida yaga tana motsi, da sauri Bilal yariko hannunshi yace "nahi" wato Aa.

Tashi yayi yagyarata me kyau tareda riko hannunta yana wasa dashi, baifi da minti biyar ba Minal ta tashi afirgice tace "Dan Allah karku kasheni".
Bilal ne yariketa yace " ke tsaya babu Wanda zai kasheki yanzu sai anjima tukun"

"Doctor ne yazo da gudu yafara kwance mata bandage d'in, yana gama kwancewa Minal taga wani haske acikin idon ta, da sauri ta runtse idon, Bilal yace " bud'e idonki ki kalleni"
A hankali tafara bud'e idon harta saukeshi akan Cute face nashi me d'auke da murmushin jin dad'i,
Takasa koda motsi sai kallonshi take kamar statu, hura mata iska yayi a ido yace "kallonfa Hajiya? Ko na miki ne?"

Batayi magana ba har yanzu mamaki ne a ranta, Tashi Bilal yayi zaije yakarb'o maganin,
Yaji an rungume shi ta baya sosai, murmushi kawai yayi Dan yasan itace, a hankali tace "yaya Bilal idona yana gani?"

Cikin wasa yace "Aa idona ne yake gani"

Sakinshi tayi tadawo ta gabanshi ta rungumeshi sosai kamar zata mayar dashi ciki, "Ash karki karyani Malama, jeki kwanta zan karb'o magani"

Tace "zan bika mu karb'o tare ina son ganin ko dagaske na warke"

Dariya yayi yariko hannunta yace "to muje hajiya me idanu"

Suna fita tafara ganin indiyawa sai kallonsu take baki bud'e har suka iso cikin office d'in, Wata doctor ce mace zaune kan kujera, tana ganin Bilal tafara dariya tareda wani yauk'i tana kwarkwasa, tashi tayi tabasu Maganin, kafad'ar Bilal tariko tana mishi bayani da harshen turanci,
Minal ce abin yabata haushi tace " Madam bakya ganin  tareda matarshi yake ne?

Bilal yaji abunda tafad'a Amma be kulata ba, ganin sun shareta yasa taja hannun matar tace "ba magana nake miki ba?"

Matar tace "what are you saying?"

Minal tace "oho dai kifad'a da Hausa kiga ikon Allah"

Bilal yace "batajin Hausa kiyi mata magana da turanci"

Minal tace "oho, you mata, ni dashi we are mata da miji, Aure d'aurawa ni dashi, sabida haka I will tell you"

Da Bilal yafara dariya saida tafara mishi kuka kafin ya daina, hannunta yariko yace "karkiyi kuka Mrs Bilal muje amiki Allura saimu tafi ko?"

Minal taki yin magana har suka je akayi mata allura da kyar ta yadda, ana gama yi mata Bilal yakarb'i takaddan sallama, suka nufi Hotel, Minal ido tazuba tana kallon kasar India a zuciyarta tace "idan nakoma gida zan fad'awa Madina duk abinda nagani"

"Chungathara" wani Babban Hotel ne dake kasar India acan suka sauka, Bilal yace "oya jekiyi wanka kifito zamuyi magana"

Minal tace "to"
Wanka tayi ta d'aura towel Amma towel d'in yayi mata karami, tsayawa tayi a toilet d'in takasa Fita, Bilal ne dayaga ta dad'e yace "Me kikeyi ne?"

"Yaya Bilal towel d'in yamin karami ka taimakamin da babba"

"Ni sa'anki ne dazaki aikeni, idan bazaki fito ba kizauna haka"

Dataga ba sarki sai Allah kawai ta mazge tafito tana kakkare jikinta da hannu, Bilal dayake zaune akan gado hankalinshi yana kan chatting, sai jin kamshin turaren wanka yayi, data lura baya kallonta tafara tafiya cikin sand'a tanason d'auko kaya tasa, d'ago kai Bilal yayi caraf idonsu yahad'u dana juna, da sauri ta d'auke kanta tafara Neman kayan dazata sa, saidai tana bud'e wardrobe d'in taga wayam ba komai, durkushewa tayi awajen, shikuma Bilal yakasa d'auke idonshi akanta, Minal ganin yana kallonta sosai yasa tace "yaya Ka daina kallona haka"

Har yanzu idonshi bai bar kanta ba, zuwa lokacin har idonshi yafara sauya kala, sabida ganinta haka ba karamin rikitashi Tayi ba.

_✔ote & Comment_

Jiddah S Mapi

MAKAUNIYA CE Where stories live. Discover now