page 39

361 22 4
                                    

*بسم الله الرحمن الرحيم*

🌸🌸🌸🌸🌸🌸
*MAKAUNIYA CE*
🌸🌸🌸🌸🌸🌸

Page 39...

  By
Jiddah S Mapi

*____________________________________*

*🌈KAINUWA WRITERS✍🏼 ASSOCIATION*🤝🏻
'''{United we stand and succeed;Our ambition is to entertain & motivate the mind of readers}'''
https://www.Facebook.com/kainuwawritersassociatio

~ ajiyar zuciya Baby ta sauke tace "kedai bari kawai sister"
Minal tab'e baki tayi batace komai ba.

_washe gari_

Su Baby sun sa kayansu a mota Hamma yarda ne yake tayasu yanajin ba dad'i Minal zatayi nesa dashi, kowa yashiga mota Minal ce kusa da window sun gama sallama da kowa, knocking na glass d'in akayi, Minal ce ta sauke glass tanason ganin ko waye, Hamma Yarda tagani tsaye ya zuba mata manyan idanunshi, ganin kallon yana nema yayi yawa yasa tace "lafiya Hamma yarda?" Kawar da kanshi yayi gefe, hannunshi yasa a Aljihu ya Ciro wata farar paper ya mika mata, bai jira ta bud'e ba ya juya yashhiga gida, Duk abinda suke yi akan idon Daddy, Murmushi yayi ya kawar da kanshi.
Baby tace.

   "Irinsu ba'ason rabuwan nan"
Mommy ce ta harareta, kama bakinta tayi tana dariya kasa kasa, Driver ne yaja mota suka d'au hanyar Abuja.

  "Bilal ya kwana da mugun zazzab'i, manyan idanunshi har sun kankance, lips nashi sunyi jaa alamar yanajin jiki, daidai da sallah a zaune yakeyi shima da kyar, yana cikin wannan halin Latif ya shigo shima fuskarshi da alamar Damuwa Sam baiji dad'in fasa mishi waya da akayi ba, yana shiga yayi sallama Amma ba'a amsa ba, karasawa yayi cikin bedroom Bilal ya hango kwance akan gado ya kudundune jikinshi da bargo jikinshi yanata rawar sanyi, Da gudu ya karasa yana tambayarshi "Bilal meya sameka?"

  "Bilal baya iya bud'e bakinshi, sai lumshe idonshi kawai yake, Latif ne ya Ciro waya da sauri yakira doctor, cikin minti goma sha biyar saiga doctor yashigo, duba Bilal yafara yana mishi gwaje gwaje, ruwa ya d'aura mishi tareda yi mishi Allura, a lokacin Bilal ya samu bacci, Doctor ne yacewa Latif "tin yaushe yafara rashin lafiya? Kun barshi saida ciwo yaci jikinshi kafin Ku kira doctor? Yanzu Abinda nakeso dakai ka rika kula da lafiyarshi kada kabarshi yana yawan tunani domin zai kawo mishi babban illa"
Latif ne ya gid'a kanshi cikin jin tausayin Abokin nashi, magunguna Doctor yabashi yace "ga wannan ya rikasha akan lokaci" godiya Latif yayi ya biyashi kud'inshi, 6:30Pm daidai Bilal ya bud'e manyan idanunshi yana kallon silin, a hankali ya maida kanshi zuwa ruwan da yake hannunshi, tashi yayi da Sauri ya zame ruwan yana kallon Latif, Latif ne ya mike yace
"Bilal lafiyarka kuwa? Kana gani fa ruwa aka sa maka kuma ka cire, bakason lafiyarka ne?"

   "Dama kun damu da lafiyata ne?"
Latif cikin mamaki yace "wani irin maganane wannan Bilal? Lafiyarka ai abun Damuwa ne"
Bilal ne ya tab'e baki ya mike zuwa toilet Dan ya watsa ruwa, Latif ma bece komai ba Dan yasan Halin Bilal tsab idan yace bazaiba to babu Wanda ya isa ya hanashi, Gashi Bilal tausayi yake bashi sosai ganin yanda ya rame ya kara haske kamar ba jini a jikinshi, Bilal ne yafito daga toilet d'in ya zauna a gefen gado yana shafa lotion nashi me kamshi ko kallon inda Latif yake baiyi ba, latif ne ya matso inda yake ya dafa kafad'arshi yace.

   "Bilal gaskiya kana bani tausayi, ada nayi niyan sai kasan darajar Minal kafin nafad'a maka inda take, Amma gaskiya lamarinka sai karuwa yake, kana ramewa sosai"
Bilal ne ya zame hannun Latif cikin fushi yace "basai kafad'a min ba na  hakura kawai"
Latif yace "nasan bazaka iya hakura ba kana fad'a ne kawai, Amma dolene nafad'a maka, ranar Dana sameka a airport to aranar naga passport na Minal kuma na duba information akai sai naga an rubuta Abuja Maitama"
Bilal ne yariko hannunshi idonshi ya cika da hawaye yace "Dan Allah Latif kar kayimin karya don samun lafiyana pls"
Latif yace "ba karya nake ba gaskiya nake fad'a maka"
Bilal ne ya mike yanufi wardrobe passport nashi yafara nema, zauje yayi visa.

    "Baby tayiwa Daddy maganar makarantar Minal, Daddy yaji dad'i sosai washe gari akayi mata register a makarantar su Baby, Minal tafara zuwa school rana ta farko harta fara gane Abu, 'yan mata sai zuwa wurinta suke wai sunaso suzama kawaye, Minal sai dariya kawai takeyi musu.

   "Bilal yayi visa gobe da sassafe zai tafi Abuja, Latif ne yace "Bilal yakamata fa kabi komai a hankali kada kayi gaggawa"
Harara Bilal ya banka mishi baice komai ba yaci gaba da shirya kayanshi.

  _Guy's am seriously busy am trying my best to write in return just expects ur moment.
.well if you won't comments I will not give update...silent readers pls comment....next Update when can't promise am vary busy, Thanks you All_

✔ote and Comments

  *Wattpad*

@jiddah S Mapi

MAKAUNIYA CE Where stories live. Discover now