page 32

384 17 1
                                    

*بسم الله الرحمن الرحيم*

🌸🌸🌸🌸🌸🌸
*MAKAUNIYA CE*
🌸🌸🌸🌸🌸🌸

By
Jiddah S Mapi

Page 32...

"Sauri take kamar zata tashi sama, batasan ma ina zataje ba burinta kawai taga tabar Cikin Hotel d'in yanda ko yadawo yanzu bazai ganta ba, tana Cikin tafiya ne ta hango wani majalisa da sauri ta karasa tana gaishesu babu Wanda ya kulata Sai  harkokinsu suke, ta gaji iya gajiya gashi bata samu mafita ba, tin safe take yawo a gari babu me taimaka mata ga yunwa ga kishi duk ta Tara, zama tayi a karkashin wata bishiya, har yanzu bata daina jin ciwon jiki ba, kishingid'a tayi tad'an lumshe kyawawan idanunta da Alamun gajiya, jakarta ta ajiye a gefenta ta d'aura hannunta akai sabida tsaro, wani nauyayyen bacci ne ya kwasheta ba shiri, mikewa tayi a kasa tafara bacci".

Bilal kuma wani farin cikine ya zagaye jikinshi ganin Minal ta sakko da wuri, idan ya tuna abinda yafaru tsakaninsu Sai yayi murmushi, jin kanshi yake kamar sabon halitta, wani babban super market ya nufa, kayan bacci na mata masu kyau ya zab'o, da turaruka masu kamshi, b'angaren kayan sweet ya nufa ya d'ebo su Chocolate da oatmilk dasu candy sweet Sai Ice cream saya siya mata sabida yasan tanaso sosai, wani zobe da d'an kunne na gold ya d'auka mata, murmushi yayi azuciyarshi yace "nasan idan tasa wannan she will become like princess".
A takaice zuwa wannan super market dayayi, yayishi ne sabida Minal Dan yanason ya faranta mata kamar yanda itama ta faranta mishi,
Yana gama siyayyan yanufi wajen me kaza, yasiyo gasasshe guda biyu, mota ya kama ya nufi Hanyar Hotel Cikin zumud'in zaije yaga beautyn shi.

"Yana zuwa ya wuce Room 120 Wanda shi suka kama, Murmushi yayi yace "nasan yanzu tana jirana"
Sai de me? Yana zuwa yaga kofar d'akin Rubb da kwad'o, Cikin mamaki yace "kai waya rufe d'akin? Kodai namanta d'akin ne? No Room 120 muke kuma gashi shine wannan"
Ajiye ledojin hannunshi yayi yatafi wajen reception, tambaya yayi, ina makullun Room 120? Mika mishi makullin akayi Cikin mamaki yace to ina Minal taje? Kai baridai na dubata Cikin d'akin, da sauri yaje wajen d'akin ya d'ebo ledojin yashiga,
"Beauty? Beauty?"
Shine abinda yake fad'a nemanta yake acikin d'akin har karkashin gado saida yaduba dasu toilet gaba d'aya Amma ko Alamunta babu, Cikin firgici yafita a d'akin ya nufi wajen reception Yana tambayarsu waya kawo makullin, wata mata ce tayi mishi bayani cewar ai wata yarinya ce takawo Hannunta d'auke da jakan kaya"
Bilal Cikin tashin hankali yace "no no beauty baza kiyi hakaba nasani zaki dawo"
Barin wajen yayi da sauri yanufi harabar hotel d'in da wuraren shakatawarsu amma bai ganta ba,
Zama yayi a bakin get Yana jiran dawowarta.

Minal bacci take Cikin kwanciyar hankali, wasu samari ne sukazo wucewa, Sai sukaga mutum kwance akasa rungume da jaka, zaro ido d'ayan yayi da turanci yace "kai kaga wata fine girl a can?"
Da sauri d'ayan ya juya yaga yarinya kwance tana sharar bacci, juyawa sukayi gabas da yamma sukaga babu me kallonsu, wurin Minal suka nufa d'ayan ya wupce jakar ya bud'e, ganin kud'ad'e yasa yace "guy's yaufa mun fito da sa'a ga kud'i ga kaya"
Tafawa sukayi suna jin dad'i, Minal ce taji hayaniya akanta da sauri ta mike tana laluben Jakarta, ganin samarai guda uku a kanta suna kallonta kuma da Alama 'yan kwayane yasa ta tsala ihu tace "kafa me naci ban Baka ba?"
Gudu take tsakaninta da Allah Samaran suna bin bayanta, mutane suna kallonsu Amma babu Wanda ya kula, Minal ihu take tana cewa "a taimaka min" babu Wanda yakejin yaren Hausa a cikinsu, Sai samaran suce "Ku kama mana ita b'arauniya ce"
Idan mutane sunji haka Sai su kyalesu,
A halin yanzu ta gaji da gudun kafafuwanta sun mutu, daidai wani kwana ne wata mota tazo da gudu, itama Minal da gudu tazo Sai kawai motar ya d'auketa cakk, Minal fad'iwa tayi a
kan motar a sume jini nabin fuskarta,
Da sauri me motar ya taka birki, samaran kuma ganin haka suka juya aguje da Jakar kud'in.

Wani sugar Daddy ne yafito daga motar shida wata kyakkyawar mata wacce bazata wuce shekara 40 ba, inda Minal take kwance suka nufa, d'aukanta sukayi suka sata a mota se babban Asibiti.

Bilal yana zaune a harabar hotel har dare Minal bata dawo ba, Da karfi yace "why? Why Beauty meyasa zakiyi haka, ina kikaje? Dana sani daban fita ba, Jin ana kiran Sallah ne yasashi tashi yaje yayi Alwala taredayin Sallah yayi Addu'a Allah yasa Tadawo, zama yayi akan sallayar yakasa yin komai, wasa wasa har Isha yayi bata dawo ba, ba karamin tashin hankali Bilal yake Ciki ba, ledan daya siyo su kazane yayi ball dashi, zuciyarshi kamar zai fasa kirjinshi yafito. "ina kika shigane Minal?".

Minal an kaita Asibiti likitoci ne suka taru akanta ganin yanda Take zubar da jini a kanta, da kyar aka samu aka tsayar da jinin wani farin kyalle aka d'aura mata akanta, Matar da suka bugeta ne taketa zirga zirga a asibitin,
Sai bayan isha kafin tafara motsa hannunta alokacin mutumin yafita Sallah matar ce kad'ai a d'akin ganin Hannun Minal yana motsi yasa tafice da gudu takira doctor, lokacin da suka karaso Minal ta farfad'o sai kiran " kud'ina, kud'ina kawai take".
Matar ce tarike hannunta tace "kiyi hakuri 'yata zan baki kud'inki kinga yanzu da ciwo akanki idan kikaci gaba da kuka kanki ne zaiyi ciwo"
Minal tace "to Amma zaki taimaka ki mayar dani kasar mu?"
Matar tace "wani kasa ne?"
Minal tace "Nigeria"
Matar tace "dama me kikazo yi anan?".

Cikin kuka Minal tace " Wanine ya satoni daga Nigeria sabida ni makauniya ce, shine yasa aka warkar dani, bayan na warke shine yamin Fyad'e yace kuma zai kaini wurin yankan kai yayi kud'i dani shiyasa kikaga na gudu".

Cikin tausayawa Matar tace "oh Wannan duniyar ta lalace babu Wanda zai taimaka maka Dan Allah sai Dan wani Buri nashi, Allah dai ya kyauta".

Lallab'a Minal tayi tace " kiyi hakuri in Allah ya yadda zan taimaka miki, Muma dama Next week xamu koma Nigeria kinga kafin lokacin zaki d'an samu sauki, saimu tafi gaba d'aya".

_✔ote & comments_

_Jiddah S Mapi_

MAKAUNIYA CE Where stories live. Discover now