page 21

333 21 1
                                    

*بسم الله الرحمن الرحيم*

🌸🌸🌸🌸🌸🌸
*MAKAUNIYA CE*
🌸🌸🌸🌸🌸🌸

  By
Jiddah S Mapi

Page 21...
*___________________________________*

*🌈KAINUWA WRITERS✍🏼 ASSOCIATION*🤝🏻
'''{United we stand and succeed;Our ambition is to entertain & motivate the mind of readers}'''
https://www.Facebook.com/kainuwawritersassociation

Umma ce ta karaso tace "dama kana sonta ne? Kuma kake wulak'anta ta? Yarinyar nan da kasan wahalar data sha a rayuwarta da bakayi mata haka ba, kun yaudareta, wai zaku kaita India a gyara mata ido, amma kuje kuna wulak'anta ta, to bari nafad'a maka, banason nakara ganinka a Asibitinnan, kuma kaida Minal har Abada, zan d'auketa awajenku, bazaku kara ganinta ba, balle kusamu damar wulak'anta ta, kaje mun gode da hidima"

Bilal k'afafunshi sun kasa d'aukarshi, jin kalamun mahaifiyar Minal yake kamar Almara, cikin yanayi na nadama yace "Umma wallahi na tuba, Umma bazan iya kwana a d'aki d'aya banda Minal ba, nasaba da ita"

"Ka saba da ita ko?
Ai gara kacemin ka saba da dukanta zanfi ganewa"

"Umma Dan Allah ki yi hakuri ki yafemin
Wallahi na tuba"

"Idan kaga na yafe maka to Minal ma tayafe maka".

Suna cikin haka, Minal tad'an d'aga  hanunta, a hankali tace "Yaya Bilal inajin fitsari"

Da sauri Bilal yaje inda take ya d'agota yace "Kina lafiya Minal?"

Minal kawar da kanta tayi tace "yaya Bilal nace maka inajin fitsari"

'Daukanta yayi ya kaita toilet, shiya cire mata wandon uniform d'in, datayi fitsarin yayi mata tsarki, kafin yariketa suka fito.

Umma Ce ta k'araso wajen ta rungume Minal tana kuka, Minal tace "Umma yaushe kikazo?"

Umma tace "Minal jiya nazo, ya jikin naki?"

Minal tace "da sauk'i Umma"

Doctor ne yashigo d'akin yana tsokanar Bilal "Malam Bilal d'azu na shigo ai naga kana wata yanayi shiyasa nafita"

Bilal kawar da kanshi yayi Dan yanajin kunyar Umma sosai.

Doctor ne yace "yawwa dama ba wata Matsala, jira kawai muke ta farfad'o gashi kuma Allah ya taimaka, zaku iya tafiya gida Amma saimunyi mata Allurori"

Minal tace "Allura kuma? Meyasa za'amin Allura?"

Doctor yace "kina tsoro ne Madam?"

Minal tace "niba tsoro nake ba"

Doctor yace "okay Bilal kabiyoni Office kaida ita akwai wasu magani da ya kamata a bata"
Daganan yafice a d'akin.

Bilal ne ta rik'o hannun Minal, yanufi office na doctor da ita.
Suna zuwa doctor ya d'auko Allura yace "to madam tashi ki karb'i Alluranki"

Idanun Minal ne yafara cika da hawaye, a hankali tace "Dan Allah kar kayimin da zafi"

Doctor yace "kince ai bakya tsoro, to meye na kuka?"

Bilal ne yafara dariya kasa kasa.

Minal tasan Bilal yana nan sai kawai ta dak'e ta mike .

Doctor ne yace "juya to Madam"

Minal taki juyawa, Bilal ganin hakane yasa yatashi, ya iso wajenta, ya rungumeta yad'an ja wandon uniform d'in kad'an, kafin yayiwa doctor Alama da ayi mata.

A hankali tafara cewa "kasakeni yaya Bilal, wallahi zan cijeka, banason Allura"

Bilal ko kulata baiyi ba,
Doctor ne ya d'auko Alluran yazo yayi mata.

Lokacin da Alluran ya shigeta ihu tayi tareda kankame Bilal sosai, kamar zata mayar dashi ciki.

Saida Aka gama Alluran kafin tafara jin kunya, taki sakin Bilal.

Doctor ne yace "to sakeshi mana ai an gama ko bakiga na zauna ba?"

Bilal ne yace "ai bata gani, idonta yasamu Matsala".

Doctor yace " matsala kuma?" Meya kawo mata matsalar?"

Bilal ne ya tambayi Minal wacce take rungume dashi har yanzu yace "Minal meya samu idonki kiyiwa doctor bayani"

Ita kuma Minal gani take kamar ta kwafsa datayi kukan Allura, (abinka da fulani) hakan yasa taki sakin Bilal, cikin jin kunya, tace "munyi fad'ane da wasu mutane shine suka watsamin Acid"

Doctor yace "subhanallah, dolene sai an fita da ita kasar waje kafin a gyara mata idon"

Bilal yace "eh ana kan hanyar zuwa"

Magani likita yabata, yace a kula sosai, Allah yakara mana sauki gaba d'aya"

_✔ote & Comment_

Jiddah S Mapi

MAKAUNIYA CE Where stories live. Discover now