page 20

406 24 6
                                    

*بسم الله الرحمن الرحيم*

🌸🌸🌸🌸🌸🌸
*MAKAUNIYA CE*
🌸🌸🌸🌸🌸🌸

By
Jiddah S Mapi

Page 20...

*___________________________________*

*🌈KAINUWA WRITERS✍🏼 ASSOCIATION*🤝🏻
'''{United we stand and succeed;Our ambition is to entertain & motivate the mind of readers}'''
https://www.Facebook.com/kainuwawritersassociation

"Yana fad'in haka yajuya yabar gidan gaba d'aya, zuciyarshi a cunkushe yarasa me zaiyi yanzu, Asibiti ya nufa wajen Minal"

Daddy da duk haushi yake ji yasa ya tashi a tsawace yace "haba Hajiya meyasa zaku baiwa wannan dak'ik'iyar matar guba tasawa Minal a abinci, yanzu baga irinta ba, nasan halin Bilal idan yace zaiyi Abu to babu Wanda ya isa ya sashi, gashi kun jawo yafasa Auren Afrah, wannan ai bala'i ne"

Hajiya babbace tace "dakata Umar, karka sake kace zaka d'aura mana dukkan laifi, kai me ze hana ka zuba mata, sai mune zaka baiwa, kuma yanzu kana mana tsawa, ai idan yasan wata to besan wata ba, Dan yaga nayi shiru? To wallahi be isa ba saiya Auri Afrah koda boka koda Malam"
Tana gama fad'an haka taja hannun Afrah fuuuuu wacce take ta kuka sai d'aki.

Sun bar Daddy tsaye baki bud'e yarasa me yake ciki, sallamar 'yan sanda ne ya katseshi daga tunani, DPO ne yace "Alh munzo muyi bincike akan kisan kan da akayi"

Azuciye Daddy yajuya yace "get out from my Room!!!"

DPO ne yace "kamar yaya? Akan me zamu Fita? Ai sai munyi binciken da aka turamu"

Daddy ne yace "to bata mutu ba, kuyi abinda zakuyi, idan kunga dama Ku bincika har cikin kwalban drinks"
Yana fad'in haka yabar musu wajen, cikin jin haushin su Hajiya Babba sun b'ata mishi plan"

"Bilal yana zuwa Asibiti, yawuce d'akin da aka kwantar da Minal, yana shiga yaga ansa mata uniform na patients, blue, kanta babu d'ankwali, hakan yasa gashinta ya bazu, akan gadon, fuskarta tayi fayau, idanunta a rufe, karasawa yayi kan gadon da take, d'ankwalinta ya d'auko ya d'ago kanta a hankali, yad'aura mata, a hankali yakara maidata, kura mata ido yayi, yanajin tausayinta a kasan zuciyarshi, doctor ne ya turo kofar yashigo"

Doctor yace "Bilal ka samo ruwan sanyi da towel ka goge mata jikinta"

Bilal yayi shiru daga baya yace "doctor babu mata ne wad'an da zasuyi mata hakan?"

Doctor yace "malam Bilal ita fa matarka ce, me zai hanaka yimata hakan?"

Bilal ne yace "okay doctor zanyi mata"

"Fita doctor yayi"

"Bilal ne yamik'e tareda d'ibo ruwan sanyi acikin wata 'yar roba da farin towel, zuwa inda take yayi, ya zauna, ya rasa ta ina ma zai fara, saida yad'an ja lokaci kafin ya d'agata ya fara cire mata uniform d'in, bayan yacire mata ne yasa towel d'in a ruwa ya fara goge mata jikinta a hankali, yana gamawa ya shafa mata wani lotion me dad'in kamshi, ya mayar mata da kayanta ya kara kwantar da ita, tareda rufeta da bargo"

"Mayar da robar yayi da towel d'in, yazo ya zauna kusa da ita yariko hannunta yana murzawa a hankali, tausayinta yakeji har cikin zuciyarshi, cire bargon yayi tareda hawa gadon shima ya kwanta a gefenta, yaja bargon ya rufa musu, a haka har bacci ya d'auke shi"

"Doctor ne yashigo d'akin da niyan yimata wasu Allurori, ganin Bilal yayi kwance a kan gadon, dariya yayi, a fili yafurta " Allah ya shiryeka Bilal"

"Daddy yau yana cikin bak'in ciki, wayarshi ma ya kashe, Dan bayason damuwa, Yarasa wani shawara zai bawa kanshi, tunawa yayi da Alhaji Nura, da sauri ya d'auko wayarshi ya kunna tareda neman numbar Alhaji Nura"

MAKAUNIYA CE Where stories live. Discover now