page 41

449 23 5
                                    

*بسم الله الرحمن الرحيم*

🌸🌸🌸🌸🌸🌸
*MAKAUNIYA CE*
🌸🌸🌸🌸🌸🌸

Page 41...

  By
Jiddah S Mapi

*____________________________________*

*🌈KAINUWA WRITERS✍🏼 ASSOCIATION*🤝🏻
'''{United we stand and succeed;Our ambition is to entertain & motivate the mind of readers}'''
https://www.Facebook.com/kainuwawritersassociatio

   ~me gadi yagaji da zirga zirga gashi ba Dama ya d'agasu sabida matane, cikin hanzari ya d'aga Bilal yasashi a gaban mota, Daddy ma yatashi yasa su Baby da Mommy da Minal a mota, suka nufi hanyar asibiti, suna zuwa aka karb'esu hannu bibbiyu, likitoci suka rarrabu akansu suna basu kulawa, Daddy da me gadi ne suka d'an fita domin subasu wuri, Zagaye cikin Asibiti Daddy yafara yana tunanin menene yasa dukkansu suka suma a lokaci d'aya? Share zufan daya fito mishi a goshi yayi, Megadi ne yace "Alhaji zamanin yanzu mutanefa ba abun yadda bane, zakaga mutum simi simi kamar mutumin kirki saika zauna dashi kafin kasan Halinshi, ni Dama tun zuwan yaron bai shiga raina ba, bakaga gashin kanshi ba kamar rumfa"
Daddy cikin dakewa yace "malam Yusuf Addu'a shine babban abinda yakamata muyi yanzu ba wai surutu ba"
Malam Yusuf shiru yayi bai kara cewa komai ba,
Sai bayan Isha kafin su Baby suka farfard'o Abin Mamaki Baby da sunan Yaya Bilal ta tashi, Mommy ma Bilal taketa Ambata, Sai Minal data tashi Tana Hawaye wani nabin wani, ta b'angaren Bilal yana farfad'owa yaganshi a d'aki kwance, a hankali yagmfara bin d'akin da Kallo, murya a toshe yace "Ashema Mafarki nakeyi, to amma inane nan?" Wani doctor ne yashigo yayiwa Bilal murmushi tareda mika mishi hannu suka gaisa, yace "Sannu Kaine Bilal ko?"
Bilal gid'a kanshi yayi alamar eh "ok wad'anda aka kawoku tare suna nemanka, Akwai wacce takeson ganinka acikinsu"
Bilal sai a lokacin ya tuna abinda yafaru sauka yayi akan gadon yace "ka kaini wurinsu"
Doctor yace "kabi a hankali fa"
'Dakin dasu Minal suke Doctor yakaishi, suna zuwa Doctor yayi sallama Bilal ma cikin sanyin murya yayi sallama, Minal ce kwance ta rufe idonta kamar me bacci, Zuciyarta tana mata sake sake da Dama, Jin sallamar Bilal yasata kara runtse idonta, Bilal yana shiga d'akin yaga Mommy tanata kuka, karasawa wurinta yayi da gudu ya rungumeta, itama rungumeshi tayi sosai tana kuka, Baby ma tashi tayi akan gadon da aka kwantar da ita ta rungume Bilal ta baya tana kuka, cikin sheshekar kuka Bilal yace.

     "Mommy kuna Raye Dama? Shine kuka gujeni, harda ke Nabeelah? Yafad'a yana kallon Baby,
Mommy ce tarufe bakinshi tace " munyi hakane domin mu kub'utar da kanmu da kuma kai daga zalincin Yayan Mahaifinka, Alhaji Umar, Bamuyi don bama sonka ba"
Baby cikin kuka tace "Yaya bansan kana Raye ba, wallahi ban sani ba" taci gaba da kuka me tsuma zuciya,
"Ina Daddy?" Cewar Bilal.
Lokacin Daddy yashigo yana tsaye abakin kofa yace "gani nan, waye kai?"
Bilal cikin mamaki yake kallon Daddy juyawa yayi wurin mommy yana kallonta sai yaga ta kawar da kanta tana kuka sosai, "Daddy baka sanni ba?"
Daddy ne yace "ina zan sanka bawan Allah naganka dai a gidana"
Bilal cikin firgici yace "mommy kina jin abinda yake cewa"
Mommy batayi maganaba sai kuka, cikin kuka tace "Bilal yanzu ba lokacin magana bane kabari idan munje gida sai nayi maka bayani"
Minal tana jinsu Amma tayi likimo tana jin labarin kamar Almara, kara runtse idonta tayi tana numfashi kamar meyin bacci, Bilal ne yajuya yana kallon inda take idanunshi ne suka cika da hawayen farin ciki ga Minal ga Iyayenshi ga kanwarshi wacce yakesonta sosai, tashi yayi yanufi wurinta, A hankali yariko hannunta yana shafawa, Kwantar da kanshi yayi akan hannunta hawaye sunabin kumatunshi, cikin kuka yace.

   "Lalle kin cancanci yabo Beauty, Had'uwata dake ya haifarmin da farin ciki mara d'orewa, Kin Makance ta dalilina, Wanda sanadiyyar haka ni na tsira da lafiyata, Kin had'ani da iyayena, Nagode miki Minal, insha Allah saina zama gatanki a duniyarnan,  zan saki farin ciki Wanda bakiyi zato ba, zan maidaki tamkar sarauniya, Zaki fito daban acikin mata"
Minal tana jinshi, Amma tayi mishi shiru, janye hannunta tayi daga nashi, ta juya mishi baya kamar acikin bacci, Murmushi yayi yace "nasan dole kiyi fishin dani, Amma komai zakiyimin zan jure har lokacin da zaki sakko ki kulani"

MAKAUNIYA CE Where stories live. Discover now