page 10

402 21 3
                                    

*بسم الله الرحمن الرحيم*

🌸🌸🌸🌸🌸🌸
*MAKAUNIYA CE*
🌸🌸🌸🌸🌸🌸

By
Jiddah S Mapi

*___________________________________*

*🌈KAINUWA WRITERS✍🏼 ASSOCIATION*🤝🏻
'''{United we stand and succeed;Our ambition is to entertain & motivate the mind of readers}'''
https://www.Facebook.com/kainuwawritersassociation

Page 10

Tana gama fad'in haka tajuya tayi tafiyarta, Bilal kuwa jiyake kamar yabita ya lakad'a mata dukan tsiya, Amma idan yayi haka Asirinshi ze tauno, gyara zama yayi azuciyarshi yace "Afrah ce take fad'a min magana son ranta? Yaushe aka haifeta lalle saina nuna mata ni d'an halak ne bad'an haram ba da wannan tunanin yatashi yabar wajen"
Da dare kowa ya hallara ana cin abinci Bilal yace Daddy ina Neman wata Alfarma awajanka, Fad'i duk abinda kakeso nayi maka alkawarin zanyi maka, Daddy dama inason gobe ad'auramin Aure! Baki Hajiya babba tabud'e cikeda shinkafa tace Bilal yaushe kazama d'an iska? Aure kake roka ayi maka Gobe? Shikenan Bilal ka gama damu Kazama d'an iska,
Wani irin bakin ciki Bilal yaji Hakika badan Hajiya babba tana matsayin kakarshi ba babu abinda ze hana yau ya sauke mata mari,
Daddy ne yakatse mishi tunani tareda cewa "Bilal meyasa kakeson kayi Aure gobe kanada wata matsala ne?
Shiru Bilal yayi daga bisani yace Aa Daddy kawai makauniya nakeson na Aura kuma gobe nakeson anemota,
Makauniya? Bakada hankaline Kana makaho ka Auri makauniya? Da sauri Hajiya babba ta Karb'i zancen dacewa yanason yamayar mana gida gidan makafai shiyasa kaga shi makaho matarshi makauniya 'ya'yansu makafai shikenan gidan yazama na makafai....Ya isa, Hajiya babba kidaina min shishigi a lamurana  ni nace inason in Auri makauniya toke ina ruwanki? Meye had'inki dani wai? To Wallahi idan ba'a nemamin makauniya gobe na Aura ba to zan bar gidannan."
Da sauri Daddy yakatsar dashi no...no...no ba maganar Barin gida insha Allahu gobe za'a nema maka,
Hajiya babbace tafara bala'i ta inda take shiga batanan take fitaba, ace za'ayi Aure a waje bayan ga yarinya agida meye laifin Afrah yarinya kyakkyawa ga tsayi ga jiki kamar matan samudawa ga hanci kamar indiawa ga zakin murya kamar larabawa ga ilimin boko kamar turawa.
Haka takarashe surutunta babu Wanda ya tanka ta saima Daddy dayake kashe mata ido taki koda kallonshi,
Afrah Kuwa tarike cokali cikeda shinkafa takasa ajiyewa takasa sawa abaki sai bin Bilal take da kallo kamar wata zararriya,
Bilal ne yad'an saci kallonta yanason ganin abinda Hajiya babba ta lissafo cewa tanada shi amma baiga komai ba. Sai Jikin datake dashi kamar biredi,dariya yayi azuciyarshi yace Allah yakyauta.

Minal tad'anji sauki Amma har yanzu bata mike yanda take ada ba saima kara yauki da take, Ummace tace "Minal ki rinka yin Abu da karfi mana meyasa kika cika raki da yauki ne haba, dama gaki kamar sandar sunuka kuma kina kara lalata kanki da kasala"
Minal Ce tad'an ciji leb'enta nakasa kad'an tace to Umma ai Allah ne yahalicceni tsiririya haka kawai sai ayita cemin sandar sunuku? Takarashe maganar cikin tura baki da rirrintse idanu, ita adole an zageta.
Shikenan to Minal d'ita kinsan fa banason kiyi fishi, kid'anyi dariya kad'an to ko hankalina zai kwanta, kara mak'e fuska tayi tana fuffura hanci ita aduniya ba abinda ta tsana Kamar ace ita tsiririya abun yana b'ata ranta matuka,
Kumafa idan kaganta kamar abarwa iska tsabar rashin Auki, da kyar Umma tasamu tafara dariya haka sukayita hiransu, cikin hiran nasune Umma take cewa "nikam Minal bakida saurayine?" Shiru Minal tayi nad'an wasu lokuta Kafin tace Umma nibanida saurayi Madina tacemin inada kyau kar in kula kananan samarai, kumani wad'anda suke cewa suna sona daga Isa me rake sai wani me siyarda Dankali abakin kasuwa, kumafa Umma dankalin ba d'anye ba dafaffe mamanshi take mishi yake kaiwa Bakin kasuwa kato dashi.
Haba Minal ina laifin me sayar da Dankali? Ko Dankalin ba sana'a bane ba? To banason buri banason araina mutum duk Wanda yazo miki kirikeshi hannu bibbiyu kina Jina?
Tura Baki Minal tayi kafin tace "To"  mikewa tayi tana surutu azuciyarta duk iya kwalliyanta ace me Dankaline yake sonta dame rake? Dankalinma ba d'anye ba dafaffe. Idan suka karamin magana saina had'asu da Almajirai suyi musu dukan tsiya, idan yaso naraba musu Alale ladan duka.

Daddy duk ya rud'e ina za'a samu makauniya Kafin gobe? 'Dauko wayarshi yayi yakira Alhaji Nura, kana inane? 'Dayan b'angaren aka amsa da ina office, OK muhad'u A Farm house nawa, ok.
Bayan wasu lokuta Alhaji Nura da Daddy suka had'u a Farm house,
Bayan sun gaisa Alhaji Nura yake cewa lafiya kuwa naganka acikin damuwa?
Gyaran murya Daddy yayi Kafin yace "wato Alhaji Nura lamarin Bilal yana d'auremin kai, yau kawai yazomin da zancen yanason gobe gobe ad'aura mishi Aure da makauniya idan bahakaba zai bar gidan"
Wani irin dariya me sauri Alhaji Nura yayi Kafin yace "shine Dama maganar? Ai fad'uwa tazo daidai dazama, idan ya Auri makauniya ai bakuda matsala, ita bagani takeba balle idan taga anyi Abu babu kyau tafad'a mishi, kaga zaka kama tsuntsu biyu da tarko d'aya, nafarko dolene yakara Aure idan matarshi tahaihu sabida kula da yara kaga saika Aura mishi Afrah, nabiyu zega kamar kanasonshi tinda har kayi mishi abinda yakeso kaga ze mallaka maka komai nashi"
Dariya Daddy yayi tsabar farin ciki shiyasa nakeson shawara dakai Alhaji Nura, kana saurin gane abu to Amma samun makauniyar shine matsala ni ina zan samu makauniya?
Wannan ba damuwa bane Akwai wata yarinya datake sayar da Alale a company da tanada ido amma yanzu ta makance zanyi magana da mamanta,
Nagode Alhaji Nura Allah yabar zumunci,  Allah yakara had'a kanmu,
Ameen cewa Alhaji Nura nan sukayi sallama kowa yatafi gida.

"Latif yana cell babu abinda ake gana mishi sai Azaba, kuka yake yana rokansu sufad'a mishi abinda yayi Amma sunki fad'a, tin yana rokansu harya fara gajiya yayi shiru yana kallonsu,
Wani babban police ne yashigo yana tambayansu ya Amsa laifin shine?
No yallab'ai wannan yanada taurin kai yaki fad'an komai cewar wani police me katon tumbi da gashin Baki,
OK kubarni dashi kuje kuyi aikinku zanyi mishi wasu tambayoyi, Fita sukayi akabar Latif da DPO sannu Malam Latif cewar DPO dakyar Latif ya Amsa da yawwa,
Malam Latif inason kafad'amin gaskiya domin gaskiyarka shi zai fitar dakai anan, sabida ni bana d'aurewa karya gindi kaji?
Kai Latif ya gyad'a mishi cikin Azaba da fitan hayyaci,
Yawwa shin Malam Latif Kaine ka aikata abinda ake zarginka dashi?
Bansan me nayiba,
Ok bazaka fad'i gaskiyanba kenan?Alright may be haka shirya barin nan dawuri ba,
Wallahi bansan menayi ba, enough! kana nufin kace bakai katura akashe Bilal abokinka ba? What!!! Bilal natura akashe? Bakai kad'aiba harda Ubanka shima yau anan ze kwana saikun gane kuskurenku,  Latif mamaki yahanashi magana sai kawai yazubawa DPO na mujiya yakasa koda kwakkwaran motsi tsabar girgizan dayayi, DPO yakira sauran ma'aikatan yace kuci gaba da dukanshi har sai yafad'i bakinshi, haka suka fara dukan Latif Baji bagani,
DPO yana fita aka kirashi awaya yana d'auka yace Allah yataimaki Alhaji, yanzu fitowana daga wajenshi bakaga yanda yayi laushi ba, d'ayan b'angaren akace ka kara bashi wahala sosai yanda zebar duniya cikin sauki, Dariya DPO yayi yace kaga Musa afili Fir'auna azuci wato kai Alhaji har yanzu baka daina mugunta ba? Cikin dariya Daddy yace zan daina ranar daka daina aikin d'an sanda, kace sai karshen rayuwarka? Dariya suka kwashe dashi Kafin DPO yace bari muje muci gaba da biwa jama'a hakkinsu,
Daddy ne yace ko kuma kubawa Aljihunku hakkinsu ba,
Kashe wayar sukayi suna dariyar mugunta"

_Washe gari_
Alhaji Nura ne yaje gidansu Minal bayan sun gaisa da Ummane yace am dama wata alfarma nazo nema awajenki, Ummace tace wani irin Alfarma Alhaji? Alhaji Nura ne yayi dariya tareda cewa "nasan kinason 'yarki Minal ko?"
Alhaji wazai haifi 'ya yaki?
Hakane to inason kibani Minal gobe ad'aura mata Aure dawani d'an gidan uban gidana, nayi miki Alkawarin zan fitar da ita kasar India agyara mata idanunta, sannan shima yaron makahone ammashi bamuda tabbacin warkewarshi sabida shi Acid aka watsa mishi idanun sun tarwatse,
Shiru Umma tayi tanajin abinda yake cewa, ita harga Allah tanason taga Minal tafara ganin Abu kamar kowa to Amma..idan tayarda daga baya suka karya Alkawari fa?
Alhaji Nura ne yace hajiya nayi miki Alkawarin bazan bari ta cutuba believed me, dasauri Minal tafito wacce take rakub'e ajikin kofa tana shafe shafen inda zatabi, Ummace ta tashi tariketa, rike hannun Umma tayi tareda cewa "Umma kitaimaka ki yadda ad'aura Auren yau wallahi ni nayadda indai za'a kaini Aduba idona, Dan Allah Umma nasan kina sona kuma zakiso kiga ina rayuwa kamar kowa takarashe maganar tana kuka sosai.
Jikin Umma duk yamutu tana tausayawa 'yar tata sosai, kallon Alhaji Nura tayi tareda cewa na Amince Amma sai Baban yaron yazo dakanshi Kafin ad'aura Auren yau,
Cikin farin ciki Alhaji Nura yace to...to..to insha Allahu yanzuma kuwa, nan yaciro bandir na 'yan dubu dubu ya ajiyewa Umma dafarko taki karb'a Amma yace kememe saita karb'a, godiya tayi shima yace ya gode nan yajuya yayi tafiyarsa yana me farin ciki,
Umma Ce tacewa Minal 'yata bakya ganin kamar munason mu tafka kuskure? Da mahaifinki yana raye kina ganin zai yadda da wannan Auren? Minal tace Umma zai yadda tunda yanason farin cikina, to Allah yasa hakan yafi Alkhairi, Ameen Umma"

Kuyi hakuri jiya nasa page 8 amaikon page 9

✔ote & comment

Jiddah S Mapi✍🏻

MAKAUNIYA CE Where stories live. Discover now