Page 5

385 24 0
                                    

🌸🌸🌸🌸🌸🌸
*MAKAUNIYA CE*
🌸🌸🌸🌸🌸🌸

(An heart touching story)

*Written by*
Jiddah S Mapi

*بسم الله الرحمن الرحيم*

*🌈🇰AINUWA 🇼RITER'S✍🏼*
*🇦SSOCIATION🤝🏻*

_wannan littafin sadaukarwa ne ga yayata Maryam S Mapi_

*WATTPAD*
_Jiddah S Mapi_


*Page* 5

"Minal bacci take amma zuciyarta kamar wuta har mafarkin abinda taji saida tayi, tinda take bata taɓajin abinda ya tsinka mata zuciya irin wannan ba, acikin mafarkin taga wasu mutane biyu sunje sun watsawa Bilal Acid, afirgice tatashi tana tana cewa idonka! Ka gudu idonka! Zasu watsa maka Acid, dasaufi Umma tashigo ɗakin tana rike Minal, lafiyarki kuwa? Meya sameki? Kodai Jinnu ne? Dan Allah Minal kifaɗamin abinda yafaru ke kaɗai kika ragemin aduniya bayanke banida kowa banason in rasaki Minal kitaimaka kifaɗamin suwaye suke bibiyarki?
Shiru Minal tayi batason tafaɗawa Umma abinda yake faruwa dan tasan Umma bazata barta taɗau mataki ba,
Sharewa Umma hawaye tayi tace ba komai Umma mafarkin abin tsoro nayi shiyasa natashi afirgice, kin tabbata? Cewar Umma
Minal tace eh Umma
To tashi kije kiyi wanka Minal tace to"

_Washe Gari_

6-4-2019 ranar Juma'a shida ga watan Aprilu shekara ta dubu biyu da goma shatara Bilal ne kwance akan makeken gadonshi idonshi alumshe azahiri bacci yakeyi amma a baɗini ba bacci yake ba, tunani yake akan abunda yafaru da iyayenshi da kanwarshi wanda haryau zuciyarshi tanayi mishi wasi-wasi akan wannan hatsari dasukayi, juyawa yayi ahankali yana kallon wani Agogo dake cikin ɗakinshi wanda Daddynshi yabashi tin lokacin yana primary yana daraja agogon sosai, gani yayi har karfe takwas yayi dasauri yasauka akan gadon yayi hanyar toilet, wanka yayi da sabulanshi me kamshi sannan yafito yashafa mayukanshi me kamshi da sanyaya zuciya, wata jar riga yaɗauko wanda aka rubuta Mad over you ajikin da bakin rubutu, sai wani jins nawando dayasa da picap jaa yasa da baƙin flatshoe namaza yaɗauki makullin motarshi yafice agidan.

"Minal kuwa yau wayarta take dubawa kowani bayan mintuna gani take kamar zaman datakeyi na ɓata lokaci ne gashi Umma zataje unguwa yau tahanata fita ko ina
Kuma tasan zuwa unguwar Umma idan taje bata dawowa dawuri
Gashi yaune su Alhj Umar da Alhj Nura zasu cika kudirinsu akan abokin gabanta wato Bilal, duba agogo kawai take idan karfe biyar yayi zatayi tafiyarta acewarta ko Umma bata dawoba
Karfe 5:50 cif Minal tafita agida babu wanda yasani sabida Umma bata gida Mashin me kafa uku takama tayi hanyar company tana zuwa tawuce wajen me gadi tagaidashi ina wuni baba? Yace lafiya lau ɗiyata meya fito dake yau da goshin mangariba haka?
Minal shiru tayi dan tarasa me zatace sai can wani tunani Yafaɗo mata tace Baba dan Allah yau Bilal yazo aikine?
Be zoba cewar baba megadi amma lafiya kike tambayarshi?
Eh dama baba wallahi sonake nbashi hakuri akan abinda yafaru cewar Minal amma dan Allah kokasan adreshin gidansu?
Eh nasani inji Baba megadi G.R.A house Number 3
Tom nagode baba cewar Minal
Fita tayi dasauri takama mashin tace me mashin Hause Number GRA house number 3 zaka kaini amma inason kajirani sabida sauri nake
To badamuwa Hajiya cewar me mashin ɗin"

Shikuma Bilal yau agidansu Latif ya wuni suna hira sai karfe 5:30 yadawo gida, kwanciya yai yaɗan huta kaɗan kamin yatashi yanason yayi alwalar mangariba,
Masallaci yatafi lokacin daya fito Minal dame mashin sunata hira kamar dama sunsan juna kasancewar Minal akwai saurin sabo da mutum masallaci me mashin ɗin yaje shima yabarta awajen, Minal tana zaune agefen mashin ɗin taga wasu mutane guda biyu sunzo zasu shiga gidan Alhj Umar zuciyarta ne yayi bala'in tsinkewa amma kuma saita tuna mutanen dazasu zo ze kasance 'yan dabane su kuma waɗannan da shadda ajikinsu me zafin gaske sannan da wata 'yar karamar jaka ɗayan yarataya awuyarshi da alama abokan Bilal ne
Kallonsu take har suka shige gidan.
Bayan an idar da mangaribane Bilal yadawo yaga mace zaune akofar gidansu amma tajuya kanta ba'a ganin fuskarta kawar dakanshi yayi yawuce gida ko kara kallonta beyi ba,
Ita kuma Minal ganin yashiga gida yasa ta tashi da sauri zata shiga gidan taɓoye lokacin megadi yana masallaci dasauri tashig ciki tarasa ta ina zata farabi acikin gidan Babban gidane batasan ta inane garden da ake faɗaba tsayawa tayi tana tunani taji ance ke!! Me kijeyi anan? Fitsari ne kawai btayi ba awando tsabar ruɗewa juyowa tayi taga wani tsoho da alama megadi ne yadawo, jikinta yana rawa tace dama Latif ne ya aikeni wajen yaya Bilal dajin haka se megadi yace ok ok jeki dataga tatsira sauke ajiyar zuciya tayi tace Alhmdllh dama Baba yacemin a garden kuma bansan gadmrden ɗin ba
Kibi senta har karshe zakiga garden ɗin nima dan ina sauri ne yasa bazan kaiki ba sabida Alhaji ya aikeni, to baba nagode cewar Minal"

Minal senter tabi kamar yanda Baba megadi yace daidai wajen kwana taga wasu 'ya'yan itatuwa kala kala wajen dasanyi sosai sannan yana kamshin fruits lumshe idonta tayi tana mejin daɗin yanayin wajen,
Tana buɗe idonta ahankali ahankali tayi tozali da Bilal zaune kan plastic chair dawata farar center table agabanshi wanda aka cikata da kayan itatuwa dakuma drinks kasancewar inda yake akwai ɗan haske kaɗan yasa take iya ganinshi
Ɓuya tayi abayan wata bishiyar inab yanda zata iya hango duk abinda ze faru.

"Shikuma Bilal kawai yana zaune ne amma sam yau yanajin wajen baya mishi daɗi, karan takun mutane yafaraji abayanshi daya juya sai yaga ba kowa
Waya yaɗauko yakira Latif yace mishi dan Allah Latif kazo akwai wata magana dazamuyi
Ok cewar Latif"

Yana kashe wayar yaji an ja plastic chair dayake zaune akai yana kokarin tashi yaji ɗayan ya rirrike hannayenshi duka biyu,
Gani yayi ɗayan yaciro wani abu a kwalba yana kokarin watsa mishi kafarshi yaɗaga ya buge abun dasauri meshi ya ɗauko ragowan suna kokarin watsa mishine yajuya fuskarshi a dasauri abun yataɓa kanshi ihu yasa sabida zafin dayaji, sukuma mutanen sunaji yayi ihu ɗayan yace yataɓa idonshi?
Dakai ɗayan ya amsa mishi alamar Eh.

Ita kuma Minal hankalinta akan wayarta da aka kira da sabuwar numba jin ihu da Bilal yayi yasa ta tashi afirgice tana kallon meya faru,
Ganin mutanen data gansu ɗazu tayi suna fitowa, dagudu ta iso wajen tana ganin ɗayan ze bugeta tayi saurin rike riganshi tana bugunshi gashi fuskarsu duk sun ɓoye da bakaken abu,
Ganin yarinyan zata tara musu jama'a yasa yaciro ragowan Acid ɗin yawatsa wa Minal a idanu, saurin sakeshi tayi tasa wani irin ihun daya ɗaukin cikin unguwar GRA gaba ɗayanta tace Wayyo IDONA dasauri me mashin ɗin yashigo gidan yaga Minal Kwance tana ihun idonta,
Hanunta yarike yafita da ita dasauri tana ihu tana murza idonta, dasauri yasata amashin ɗin yaja yabar unguwar da ita.

"Bilal kuwa yanajin sunce yataɓata idonshi? Se yayi pretending kamar a idonshi abun yasameshi, yasan cewa wannan shiri ne kuma yaji ihu amma idan yabuɗe idonshi yasan zasu watsa mishi a ido domin alamu sun nuna makantar dashi sukeson suyi, daidai lokacin da mutabe suka shigo gidan jin anyi ihu,
Sukaga Bilal kwance yana murza ido dasauri suka karasa inda yake suna tambayarshi meya faru? Yace Acid a idona sun watsamin shikenan namutu kutaimaka min".

_✔ote Comment & share pls_

✍🏻 *JIDDAH S MAPI*

MAKAUNIYA CE Where stories live. Discover now