page 30

400 23 4
                                    

*بسم الله الرحمن الرحيم*

🌸🌸🌸🌸🌸🌸
*MAKAUNIYA CE*
🌸🌸🌸🌸🌸🌸

By
Jiddah S Mapi

Page 30...

*🌈KAINUWA WRITERS✍🏼 ASSOCIATION*🤝🏻
'''{United we stand and succeed;Our ambition is to entertain & motivate the mind of readers}'''
https://www.Facebook.com/kainuwawritersassociation

"Runtse idonshi yayi  bai kara bud'ewa ba, Minal ganin yarufe idonshi yasa tayi tsalle ta d'ane gadon, ta lullub'e jikinta da bargo,
Bilal dayaji ta kwanta sai ya bud'e idonshi a hankali, Ya sauka akan gadon"
Wata babbar jaka ya d'auko ya bud'e yaciro kayansu jerawa yayi a wardrobe.

Yana gamawa, Toilet yanufa yayi wanka yayi Alwala.

Yana fitowa yayi sallah raka'a biyu, hawa gadon yayi shima ya kwanta, Amma bacci yakasa d'aukanshi, sai juye juye yake, sab'anin Minal datake baccinta cikin kwanciyar hankali,
Yaye bargon nata yayi yajata jikinshi yarungumeta sosai, mutsu mutsu tafara Alamun ya saketa,
"Ke Kidaina abinnan idan ba hakaba ranki zai b'aci"
Cak Minal ta tsaya bata kara koda motsi ba.
A rungume da ita yayi bacci.
Lab'ewa tayi saida taga yayi bacci kafin itama tayi.

_washe gari_

Bayan sunci abinci Bilal yace "jiya baki tambayeni maganar danace zamuyi ba meyasa?"

Minal tace "yaya na manta ne"

"Okay dama maganar da zamuyi itace, meya sameki a ido har kika makance?"

Shiru Minal tayi batayi maganaba.

Bilal yace "karki min karya ni mijinkine bai kamata kib'oyemin sirrinki ba"

Hawayene yafara fita a idanun Minal, cikin kuka tace "yaya Bilal koda nafad'a maka bazaka yadda ba, abune Wanda jinshi yafi rashin jinshi Alkhairi"

Bilal yace "idan kika fad'amin gaskiya baki b'oyemin ba ai kin fita a hakki, damuwana ne idan nayadda damuwana ne idan ban yadda ba"

Minal tace "yaya na Makance ne sabida kai!!!"

Sabida ni kuma beauty? Tayaya?.

Cikin kuka Minal tace "yaya Daddynka ne da Alhaji Nura suka tura awatsa maka Acid a ido, nikuma lokacin naje nabaka hakurin Manja Dana watsa maka a Riga, shine najiyosu, washe gari naje domin in fad'a maka Amma bansan inane garden naku ba, shine garin nemanka suka watsamin Acid d'in kuma naga fuskarsu, Hafeez kaninka kuma yana nemana da fasikanci nikuma naki yadda dashi shine yakemin barazana akan zai kasheni, ita kuma Madina ina jinku kuna hira da ita a bedroom amma muryanta kad'ai nakeji, Hajiya babba kullum saita zagi iyayena shiyasa na tsani gidanku, kuma koda mun koma Nigeria bazan iya zama a gidanku ba gara na zauna da Mahaifiyata, dama ta sanadiyyarka na makance gashi kuma ta sanadiyyanka na warke, kaga 1-1 kenan ko?"

Bilal manyan idanunshi ya zuba mata kamar maye, yanaji idan ya bud'e bakin shi to dole saiya sume sabida yanda zuciyarshi take bugawa, janyota jikinshi yayi ya matseta  sosai, idanunshi suna fitar da hawaye.

"Beauty da gaske Daddy ne yakeson ya nakasani?"

Minal tace "nifa ban fad'a maka Dan kaje kafad'a mishi ba,tom"

Bilal kuka kawai yakeyi kamar karamin yaro, Minal yabata tausayi sosai A hankali tafara rarrashinshi, tana bubbuga bayanshi, kwantar da kanshi yayi akan cinyarta zuciyarshi a cakud'e hankalinshi a tashe, A hankali yace "Minal narasa iyayena da kanwata wacce nafi sonta fiyeda komai, ta hanyar Accident, Na tabbata ba Accident bane kawai akwai abinda aka shirya kuma da yaddar Allah saina gano ko menene"

Minal dukda Haushin Bilal datakeji Dan yana zarginta da fasikanci, hakan bai hanata tausaya mishi ba, itama kuka tafara tana lallab'ashi, saida yaga tafara kuka sosai kafin ya danne zuciyarshi yayi shiru.

Ahaka sukayi sati d'aya a India, acikin satin idan suna kwance yagwada nemanta, saita fara mishi kuka, a haka zai hakura ya kwanta wani lokacin yayi ta mata nasiha akan duk matar data hana mijinta hakkinshi tana cikin tsinuwar Allah da mala'ikunshi har wayewan gari, ita kuma Minal saidai tace mishi Allah ya yafe mana baki d'aya.
A haka harya gaji ya kyaleta.

Kamar kullum yauma Minal ta takurashi saiya fita da ita yawon shakatawa, da kyar ya yadda Dan yanzu har haushi take bashi nakin Amincewa dashi.

"Wanka tayi da sabulunta me kamshi, kwalliya tayi had'i da tattare gashin kanta ta kitsashi waje d'aya, d'an kunne red tasa da warwaro red, Jan bakinta ma red colour, wani dogon Riga baki jikin anyi adon da red beat tasa, hannun a yanke kad'an kad'an, jan gyalle me beat baki tasa, zuwa wajen Dressing mirror tayi ta tsaya tana kallon kanta, wani murmushin daya bayyana dimple nata tayi, Glass na Bilal tagani half face baki ta d'auko tasa a idonta, " Wow shine abinda tafad'a lokacin dataga kanta jikin mirror"
Turare me kamshi ta d'auko ta fesa duk jikinta dashi, zama tayi akan stool tana jiran fitowar Bilal.

Bilal ne yafito daga wanka d'aure da towel babba sai karami kuma yana goge kanshi, tsayawa yayi turus yana kallonta.
Minal kuma ganin yana b'ata musu lokaci yasa ta sakko daga kan stool d'in cikin takunta na kasaita ta nufi wurinshi, karb'an karamin towel d'in tayi tafara goge mishi jikinshi,
Tana gamawa taja hannunshi zuwa wurin dressing mirror, Lotion nashi ta d'auko ta Murza a hannunta, a hankali tafara shafa mishi duk jikinshi.

Tana gamawa taje wurin wardrobe ta d'auko mishi wani Riga red colour da wando black sai picab ma red, zuwa wurinshi tayi cikin shagwab'a tace "yaya gashi kasa kar muyi dare"

Bilal shima cikin shagwab'a yace "kisamin mana Beauty".

Sunkuyar da kanta tayi cikin jin kunyar maganarshi,
Ganin ta sunkuyar da kanta kawai yayi murmushi, yaje yasa kayan data zab'a mishi, picap yasa idan ka ganshi kamar shima ka sace ka gudu (Ammafa Minal tafishi kyau, bari na gudu kafin team Bilal su rufeni da duka).

hannunta yariko yace " kinyi kyau  Beauty"

'Dago kanta tayi a hankali tace "ai ban kaika ba yaya"
Murmushi yayi yace "har kin fini ma, muje ko?"

Minal tace "ka manta Abu biyu"
Yace "mena manta beauty?"

Wurin dressing mirror taje ta d'auko agogo da turare tazo wurinshi, hannunshi takamo ta d'aura mishi agogon ta fesa mishi turare me k'amshi,
Bilal sai kallonta yake har taje ta ajiye ta dawo.

Hannunta yariko suka fita zuwa cikin garin India domin bud'e ido,
Wani wurin shakatawa me kyau Bilal ya kaisu,
Daga ganin wurin zakasan na masoyane sabida wani grass Capet dake shimfid'e akasa, sannan kowani round kujeru bibbiyu ne akai, sai gefe kuma akwai wani Ruwa me kyau da d'aukan hankali,
Minal ce taga wasu suna siyan Ice cream, da Sauri tace "yaya zansha Ice cream"

Bilal yace "dawani bakin?"
Karamin bakinta ta turo tace "da wannan mana"

Yace "bud'e mugani"

Cikin shagwab'a ta bud'e mishi bakinta,
Dariya yayi yace "bakinnan yayi karami dashan ice cream"

Kuka tafara mishi tace "ni wallahi saika siyamin"
Yace "sorry banda kuka muje in siya miki".

Share hawayenta tayi tace " to"

Bayan sun siyo ice cream ne suka dawo wurin ruwan kafafuwansu sukasa a cikin, Minal tanashan ice cream nata, shikuma Bilal sai kallonta yake tayi.

Kallonshi tayi tace "kai bazaka sha ice cream bane?"
Bilal yace "zansha mana idan kin bani"
Murmushi tayi ta d'ibo a spoon tace "haa"

Bud'e bakinshi yayi tasa mishi,
Tace "yaya yaushe zamu koma gida?"

"Sai ranar da kika yadda dani".
Minal tace "wani irin yadda kuma Yaya Bilal?"

Lumshe idanunshi yayi a hankali yasaukesu akanta, sunkuyar da kanta tayi sabida bata iya jure ganin cikin idonshi, kwarjini yakeyi mata bana wasa ba,
A hankali yace "nafison mu koma Nigeria kinada katon ciki".

_✔ote & comment_

Jiddah S Mapi

MAKAUNIYA CE Where stories live. Discover now