page 15

387 22 4
                                    

*بسم الله الرحمن الرحيم*

🌸🌸🌸🌸🌸🌸
*MAKAUNIYA CE*
🌸🌸🌸🌸🌸🌸

By
Jiddah S Mapi

Page 15....

*___________________________________*

*🌈KAINUWA WRITERS✍🏼 ASSOCIATION*🤝🏻
'''{United we stand and succeed;Our ambition is to entertain & motivate the mind of readers}'''
https://www.Facebook.com/kainuwawritersassociation

"Fine! tinda kinsan kur'ani, to Aure zanyi kuma mata biyu rana d'aya, don nalura bakida kunya, wata kila idan nakawo wacce zata baki wahala zaki shiga hankalinki"

"Haba Bilal? Bakasan cewa Allah ya halatta maka ka Auri mata hud'u bane? Ko ka manta da inda yake cewa (fankihu ma d'aba lakum minannisa'i masna wa sulasa warba) Ku Auri abinda yayi muku dad'i daga cikin mata biyu ko uku ko kuma hud'u, ni Asuwa dazan ja da maganar Allah, bugu da k'ari niba sonka nake ba, danasan kai za'a Auramin dabanyi kuskuren yadda ba, Amma duk da haka kai mijina ne kanada hakki akaina, Wanda har sai ranar da Muka rabu kafin ya sauka"

"Ummm dama kinsan Al-kur'ani haka, shine kuma kike aikata zina? Ko kin manta inda Allah yake cewa (wala tukribuzzina) kada Ku kusanci zina, wannan kam kin manta ko?"
Cikin zuciyar Minal kuna yake, tarasa meyasa Bilal ya tsaneta, "me nayi maka kake min sharrin mafi munin Abu aduniya?"
Bilal fita yayi tareda bankad'o mata kofar,
"Yanzu aka fara wasan Malam Bilal, cewar Daddy daya tsaya abakin kofa yaji duk abinda sukayi"
Wucewa Bilal yayi, kamar bega kowa ba, Amma zuciyarshi yasan akwai mutum abakin kofa, b'uya yayi a inda yasan baza'a ganshi ba, tsayawa yayi yana jiran Wanda yashiga d'akin yafito, cikin ikon Allah saiga Daddy yafito daga d'akin, rud'ani Bilal yashiga, to meya kawo Daddy wajen Minal? Kuma saida nafita kafin yashigo, anya bawata akasa?
Astaghfurullah, nasan akwai wata dalilin dayasa yazo, don daddy ko a mafarki bazai cuceni ba, saidai wannan yarinya me kama da Aljanun, nasan zata iya yin komai Dan ba sona takeba"

Wayarshi ce tafara ruri, yana dubawa yaga sunan Abba yana yawo, zuciyarshi ne tayi dumm, da sauri yafurta "Abban Latif?" Mezan fad'a mishi yanzu? Nashiga Uku.
Daurewa yayi yad'auka "Hello Abba ina wuni? Bilal ba gaisuwa ne yasa nakiraka ba, kasani cewa ni Abokin mahaifinka ne tun muna yara, nasan komai nashi, nasan halinshi mutumin kirkine, tun lokacin dayake Raye ina kula da companyn shi da dama, ban cutar dashi ba sai yanzu daya mutu zan cutar dashi? Bilal kaida wannan Daddyn naka kun bani mamaki, shine abinda zaku saka mana dashi? Shikenan Ai akwai Allah, ina rokan Yashiga tsakanina daku, anjima kazo ka karb'i komai na dukiyarka dayake hannuna, kitt yakashe wayar"
Jikin Bilal yayi la'asar a fili yafurta "da wanne zanji? Da Minal datake cin Amana na, koda tunanin meya shigar da Daddy d'akina, ko kuma Abban Latif dayake so na karb'i komai nawa na wajenshi?"

"Da Afrah zakaji yaya Bilal, ka zubar da duk wata damuwa ka Aureni, nayi maka Alkawarin Ranan daka Aureni zan bankad'o maka sirrin dakake son kasani, cewar Afrah wacce hajiya babba ta aikota takira Daddy, da zuwanta  taga Bilal yana lab'e itama saita lab'e"

"Juyowa Bilal yayi yana kallon Afrah, wacce tasha Riga da wando, hannun rigan an yanka dogo dogo kamar jelar shanu, Tsaki yaja yaci gaba da tafiyarshi"
Dasauri ta tari gabanshi ta tsunkuya har kasa tarike kafarshi "yaya Bilal nasan nayi maka kaifi a rayuwarka, wallahi na tuba bazan kara ba, idan kace kar in kara sa wando da gyalle wallahi bazan kara ba, nidai kawai ka Amince zaka Aureni koda baka sona, ka dubi girman Allah ka yadda da buk'ata ta, wallahi idan naganka da wannan matsiyaciyar matar taka, sai naji zuciyata kamar zata fashe tsabar kishi, bana son ka rab'e ta ko kad'an, hasalima kwana dakukeyi a d'aki d'aya shiyafi komai d'agamin hankali, yaya Bilal ka taimakawa k'anwarka, please"

"Baiyi mata magana ba kawai ya kwace kafarshi yabar wajen, baisan wani yanayi yake ciki ba, shin tsanarta yakeji ko tausayinta? Baisan meyasa yarinyar take sonshi dayawa ba, son datake yimishi yayi Over, shi yanzu ji yake kamar ya tattara kayanshi yagudu yabar garin Gombe ma gaba d'aya, yaje inda babu Wanda ya sanshi, yayi rayuwa cikin farin ciki ba irin rayuwar dayake ciki ba, wata zuciyar kuma tace " idan ka tafi wa zaiyi maka binceken Abinda yake faruwa? Kamata ace nad'au fansar Ran iyaye na Dana k'anwata kafin nabar duniyar ma baki d'ayanta"

"Hajiya babba ce ta karaso inda Afrah take kwance tana kuka, d'agota tayi tana mata matsifa, " Haba Afrah, ya zaki zubar da Ajin ki na 'ya mace ki sunkuya har kasa kina rokan namiji ya Aureki? Duk abinda kukayi ina jinku, Kinaso ki taunawa mahaifinki Asiri akan Namiji? To ki sani idan kika taunawa mahaifinki Asiri, kika Auri wannan d'an iskan yaron, kinga wannan jikin naki kamar an sawa fulawa yist? To wallahi saikin koma kamar matarshi tsabar ramewa, kai gara itama ai halittar tace haka, kuma ita idan ta rame zatayi kyau, sabida Asalinta Farace, Amma ke idan badan man bilicin ba ai da sai gyaran Allah, ko kallo bazaki ishi mutane ba, kinga ga rama ga bak'antaka saiki dawo kamar An soya kwad'o"

"Haba Hajiya babba wannan ai cin fuskata kike"
Waya fad'a miki?
Ni gaskiya nake fad'a gara ki hakura mushawo kan matsalar a hankali, tinda Allah yarufa mana Asiri kina shafa man dazakiyi haske, gaki da jikinki tab'as b'as, sai mubi komai a hankali ko?"
"Gyad'a kai Afrah tayi nan suka nufi d'akin Hajiya babba suna kullace kullace".

"gidansu Latif Bilal ya nufa, d'akin Abban Latif ya nufa danufin bashi hakuri, yana sallama Abba yamike yace "yawwa ga takaddun gidajenka, da companonin ka, Bilal banason komai yakara shiga tsakaninmu, Wata shari'ar kuma sai a lahira"
Bilal hakuri yarink'a bawa Abba, tareda ce mishi bincike yakeson ayi shiyasa Yace a ajiye Latif, kuma babu abinda 'yan sanda zasuyi mishi, da kyar Abba ya hakura, kafin Bilal yatafi"

"Latif ana kulawa dashi sosai a station, Idan kaganshi baza kayi zaton kamashi akayi ba, har wani haske yakeyi"

_washe gari_
"Minal ce zaune kan d'aya daga cikin kujerun d'akin, muryan Afrah taji tana cewa " Haba yaya Bilal meyasa zakayi shiru, ko kana tsoron kada matarka tajimu ne? Ni gaskiya idan zamuyi soyayyarmu kawai mu fito fili mu nunawa duniya, adaina wani b'oye b'oye, kowa tasan Akwai Aure tsakaninmu dakai, Dan Allah kayi magana yaya Bilal nawa kajiii?"

Zuciyar Minal ce tayi wani kara dummm "soyayya suke yi dama? Haba no wonder Ruwa bata tsami banza, yanda take nuna kishi afili nasan Akwai wani Abu a kasa, Ashe sune manyan karuwan gida, yake kora kunya da hauka?
Allah yashirya al'ummar musulmai"

Murmushin nasara Afrah tayi ganin yanayin fuskar Minal ya sauya, azuciyarta tace "zakiga munafinci yarinya, sai kin bar gidannan da kafarki, bankad'o kofar tayi Alamar ta tafi".

"Bilal ne yafito daga toilet, sabida yana d'an jin surutu kad'an kad'an " wannan yarinyar kodai Aljanu gareta, idan ba Aljanu ba wazaiyi magana shi kad'ai"
Bud'e kofar falo yayi, nan yaganta zaune ita kada'ai "ke? Dawa kike surutu?"

Minal kuma gani tayi ya mugun raina mata wayo, yanzu sugama magana da Budurwarshi kuma yazo yana tambayarta dawa take magana?
Murmushin karfin hali tayi kafin tace "da budurwarka wacce tafito daga d'akin nan yanzu muke magana"

Budurwata? Cewar Bilal "lalle kin tabbata me Aljanu,
To Allah yakawo sauk'i"

✔ote & comment

_Jiddah S Mapi_

MAKAUNIYA CE Hikayelerin yaşadığı yer. Şimdi keşfedin